Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 48 of 86

Kuma nan ta ke Umma ke tambayansa bayan suna Sulatana zata koma dakinta kafin dai ya koma wajen aiki.
Shi yace duk yadda ta yanke daidai ne a wajensa.
Sai dai bai yi kasa a gwiwa ba ya kalli Umma yana fadin"Ita Sultanan na son komawa da gaske?
Umma tace"Eh mana, ni ce daman na hana kuma yanzu na saki Allah ya baku zaman lafiya gabadayan ku."
Sai amswa ya ke da Ameen yana mamakin Umma.
Ita kuma Surayya sai take ganin kamar Umma ta yi sanyi ne na d'an Lokaci.
Saboda jiram su Sajida sai sha Biyu na rana suka tafi tashar Sharon suka yi gabadayan su, Mama bata samu zuwa ba diyar kanwarta ta rasu, Siyama ma bata je ba suna da Jarabawa.
Sakeena ce kad'ai a dakin mama sai Sajida Sadiya, Sa'adatu bata samu zuwa ba wai mijinta ya hanata.
Surayya sai su Goggo Hassu sai Hajiya Innani.

Ba su isa ba sai karfe uku saura na Rana koda suka isa gidan suna ya Tumbatsa da Mutane.
Gida cike fa, nan suka iske Saleema sun zo tun safe daman ta yi ta kiran su sukace suna hanya
Saukar ban girma aka yi musu daman Tunda an sam suna hanya an tanadar musu nasu abincin na musammam.
Shinkafa jallop da alala har da nama sai kunin aya da Zobo.
Ni da kaina nazo har falo muka gaisa na kuma saka Ramatu da Safiya suka kai mu su yaran.
Sun zo sun samu har anyaka Raguna Uku,har an gyara su ma tunda za'a soya da wuri a ba su nasu su tafi da shi.
Sun sameni na yi kunshi sannan na yi kitso, kuma sun iske ni da wata Atamfa da muka yi anko da su Adda Fati har da Ramatu da Safiya.
Na saka less ma da Safe Cikin kudin da Assadiq ya Turomin na siya.
Sannan Maman suhailat ta bani materila na dinka shi shima.
Sai Anty Surayya ta bani leda shake da kaya, akwai dinkakku da wad'anda ba'a dinka ba sai na jarirai da su pamparrs da sabulan wanka tace daga gare su ne.
Turmin Atamfa yafi goma leshi guda Biyu har da mayafai da Hijabai, kayan yaran ma masu kyau da su fin kala goma, kuma damam an kara siya musu wasu, Ramatu da Safiya duk sun gwangwaje ya'yan na su da kayan yara har da takalma da safuna masu kyau.

Su Adda na nuna mawa suna ta Godiya, taro ya yi armashi Sosai duka matan Baba saminu da na Baba Tanko duk sun zo min, su salima da la'asar suka dauki hanyar kaduna.
Ita man jiki ta kawomin na yara Hajiya Murjanatu kuma ta aikomin da Atamfa da kayan yara Fathihatu kuma ta bani kudi.
Kai hatta yan gidanmu ma samaru sun kawo sabulai, Ummi ma tazo ta kawomin kayan yara har Fadila sai gata tazo min suna tare da Ummin suka zo, na kuma san harda gulma ya kawota.
Saboda gidan ya yi kad'an ga baki yasa Adda Fati ta Shiga makotan ta inda suke mutunci gidan maman hanna ta roka aka kai su Anty Surayya can suka kwana da Sassafe kuma aka tashi da aikin suya nama Saboda sun ce da wuri za su kama Hanya.
Sai da Safen ne Sajida da Sadiya suka shiga har dakin da na ke Lokacin mun dawo wanka ni da Inna Talatu.
Ita fita ta yi ta bamu waje, suka nemi gafarata nace musu ya wuce.
Sannan suka bani wayata da Key din dakina tare da Atm din bankina.
Sadiya ce ke sakin Fuska Sajida kuma tunda tace na yi hakuri ta kauda Fuska ni kuma na nuna musu komai ai ya wuce ni dai Tunda suka barni da dan'uwansu ai sun gama min komai.
Misalin sha Biyu na rana suka tafi, Suka bar mim Innani kamar yadda Assadiq yace ta na ko kamkame da ya'yan magajin gida ta bakinta.
Ta dankgwali Hancin wancan tace sulaimanu, sai ta dangwali hancin wancan tace muhammadu, ba ruwanta ita fa Imnani in za'a zauna ta yi ta Hira ba'a gwasaleta shikenan su Adda na shan Labaran su Assadiq da Abba.
kuma ba sakaya komai da komai ta ke fad'a ni dai ina Ta tsoron kada ta je ta fad'i abunda ya faru tsakanina da su Sajida sai kuma aka ci sa'a Hirarta bai kaita can ba.
An diba musu nama da yawa sun tafi da shi, Amma na Abba dabam na Assadiq ma dabam, sai kuma na Umma shima Dabam na su ne aka had'a waje d'aya.
Naji dadin zuwan su kuma hakan ya kara tabbatar min da cewa da gaske ne Assadiq na sona kuma ya Tsayamin.
Su Adda kuma suna ta Hiran sun fara Saukowa, suna ta kuma bani shawarwarin yadda zan kara jawo su gareni a sannu ko Saboda yan yaran nan.
Ni dai jin su kawai na ke yi, zan yi dai iya bakin kokarina ammh ba lalle ne na Burge wasu daga cikin su ba.
Ni dai na sakama raina zan zauna da Assadiq cikin Amana na yi masa Biyayya har karshen Rayuwata.
Saboda ya yi min komai a Rayuwata ko nace ya na kan yi mini mana.

*Janafty*
*TMWB3K013*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65

Kamar yadda Umma ta fad'a ashe da gaske take yi, bayan suna da kwana uku ta shirya Sultana ta maidata gidan mijinta duk da sultanan na ta koke koken ita bazata koma ba sai ta gama Jarabawarta gabadaya Umma tace bata isa ba.
Daga Sadiq har Abba suna mai Farincikin ganin Sauyawar Umma, Ko naman suna da yaji da su Anty Surayya suka kawo mata da girmamawa ta Karb'a ta na saka albarka su Sajida ma suna kokarin kawo mata wata mgana a gaban Surayya ta ja musu kunnen bata so, sannan ta na basu Umarnin su shirya da Dan'uwan su bata son ta kara jin wata mgana.
A lokacin Sadiya sai ta kada baki tace"Umma mu kenan zamu bisa muna yi masa mgana! Yaron da ya fara gaba damu?
Umma tace"Eh ku bi shi ku yi masa mgana ku basa hakuri, ai durkusa ma wada ba gajiyawa ba ne."
Da haka ta kashe bakinsu kuma Sai suka yi girman kai ba su ba shi Hakurin ba, shi kuma bai kara bi ta kansu ba tunda dai Siya ta gayamasa sun je sun bata Hakuri kuma sun dawo mata da abunda suka karb'a.
Umma bata nemi Rakiyar kowa ba sanda zata maida Sultana domin ko mutanem shinkafi tun jiya da Safe suka koma gidajensu Mama kuma tana gidan Gaisuwa.
Sai da suka isa gidan ne ta saka Sultana ta zage itama ta tayata suka gyara gidan gabadaya ta kuma sakata ta Dauki waya ta kira Sadiq tace masa ta dawo tana Bukatar Cefane zata yi girki.
A lokacin baki ta tura kafin tace"Umma ni fa baya kirana, ko mgana ma ba ya yi min indan ya ganni."
Sai idanuwanta suka ciko da kwallah Tausayinta ya kama Umma sai dai bata nuna ba cikin ba ta Umarni tace"Maza ki kirasa, Umarni na ke baki ba shawara na zauna ina yi da ke ba."
Dole kanwar naki ta kira Yaya Sadiq da ta manta rabon da su yi mgana ta waya.
Kiran har ya katse bai dauka ba ta kalli Umma a marairaice tana fadin"Kin gani ko Umma bai Dauki Kirana ba, ni fa daman baya sona Hankalinsa na kan bazawarar matarsa da ta haifa masa ya'ya."
Umma ta yi mata banza kamar bata ji ta ba, in da Sultana tasan yadda ta ke ji acikin ranta da bata kara harzuka ta ba.
Duk lakwas din data ga tayi gani tayi Sadiq da Ubansa suna neman su saka Mahaifinta ya yi mata Mugun baki Saboda wata bakar Annoba, shiyasa ta yanke Shawaran gwara ta sauya taku.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.