Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 34 of 86
An riga an yi sallar azahar Abba kuma ya tsaya a chan ya yi tashi, shi kuma sai ya yi nashi a bangaren Abba.
Sai da ya idar da sallah ya Kira Big sis yace sun iso shi da Hasiya Tun dazu.
Surayya tace shine bai kawo ta gidan ta ba? Shi kuma yace ya na Tsoron ya kara yin laifi.
Dagachan Bangaren Surayya tace"Ba wani laifi, bazata sake acan ba ne, zan zo anjuma sai mu taho tare wajena daganan ma sai taga kayan da na siya mata ko?
Kai tsaye yace"Shikenan sai ki zo kawai ki Daukemu tunda nima Umma ta daina ya yina."
Surayya tace"A'a chan kai da Mamanka ni kanwata kawai zan dauka kaji ma na gayamaka."
Daga haka ta katse wayarta yana mata Dariya.
Sai da ya koma Bangarensa sannan ya kirani a waya yana jin kunya shiga Dakin Mama.
Ni ko sai da na yi mgana aka bani daki na shiga na kama ruwa na yi sallah ina zauna na yi tagumi kiran Assadiq ya shigo wayata.
Shi ya debemin kewa da Hiransa yana bani Labarin yadda suka yi da Tahir ya kirasa yana tambayansa wai daman ciki ya yi min?
Sadiq yace"Eh mana na yi kankanta da yin cikin ne?
Tahir ya yi tsaki kafin yace"Dan iska, kawai."
Na yi ta dariya ina fadin bai kyauta ba, shi kuma yana cemin Tahir ne yaja domin ya yi masa tambayan Renin wayau.
Sai da muka fi awa muna waya sannan yace naci abinci sai na yi masa karyan naci, jin haka yasa yace na kwanta na huta.
Daganan muka yi sallama kamar kuma yadda yace sai na kwanta sai barci Saboda gajiyan mota. sai bayan la'asar na tashi Lokacin ne naji ana ta Hidima na gobe sallah.
Ina bangaren Mama har bayan shan Ruwa sai lokacin Siyama ta kawomin abinci ta na min wani kallo.
Tuwon shinkafa miyar egusi, sai kuma Ferfesun kayan ciki da lemun kankana.
Naci kad'an saboda bana jin yunwa sai na sha lemun, bayan na idar da sallah na kira Assadiq na yi masa barka da shan Ruwa sai yace na fito zamu gaisa da Abba.
Da Tulin Cikina gaba na sanyo Hijabi na samu Mama da Siyama afalo nace mata Assadiq na kirana zan je na gaida Abba ta bi ni toh shikenan.
Ina fita haraban gidan na Hangosa shi yazo ya rikeni har bangaren Abba.
Muka had'e da Umma achan ta na had'a ma Abba kayan Bude baki..
Zan duka yace na zauna a saman kujera na zauna muka gaisa cikin Sakewa yana tambayana ya karatu nace masa mun gama jarabawa.
Kai Tsaye yace"Ki saki jikin ki fa, nan ma duk gida ce kuma zaki ki ji dadin salla tare damu."
Mirmishi na yi kafin nayi masa godiya umma kuma tana gama abunda zatayi ta fice ko amsa min barka da shan ruwan da na ke yi mata bata yi ba ta Fice.
Abba da Assadiq tare suka yi Bud'e baki, ni kuma sai nace bari na taka zuwa bangaren Innani.
Na gane gidan yanzu kuma na kai kaina bangaren Innani ina shiga sultana na fitowa ta dawo kai Innani Ruwan zafi.
Muka kusa cin karo sai muka tsaya muna ma juna kallon kallo
Ni ce ma na kauda shurun ina Mirmishi nace"Sultana."
Duk da ina jin wani abu a raina ammh sai na Danne.
Ita ko wani irin banzan kallo ta yi min kafin kawai ta bangajeni ta wuce a bakinta naji tace"Banza mai kwacen miji kawai."
Ni ba wannan na damu ba sai bangazar da ta yi min kamar bata ga bani kad'ai bace.
Bango na Dafe yasa ban fadi ba, na bita da kallo ina jinjina kai.
Da sallama na shiga Falon innani suna zaune da Farida.
Da farko bata ganeni ba sai da na yi mata bayani tunda itama Faridan bata sanni ba.
Aiko sai ta washe baki ta na ta min Dariya ta fara min fira labarai harda na Umma da ta hana sultana komawa gidanta.
Tace min"To ni in na saka baki sai ayi cewa na zabe ki naki jikata, kinsan mutane ba'a iya musu. Kuma ni na saduda ne na bi Allah Tunda sulaimanu da magajin gida suka min nasiha na yi shuru da bakina kada na Tofa ace na yi munafurci."
Ni dai sai dariya na ke yi mata, Innani akwai dadin zama.
Dan zaman da na yi a bangarenta na sha Labarai kala kala harda na chan mutanen shinkafi.
Sai zuwan Surayya ne ya tada Hirarmu tace daga wajen Su Abba take Sadiq yace ina sashen Innani.
Ta zauna itama ammh bata dade ba, tace na taso mu tafi na yi ma Innani sallama sai da muka fito ne muka had'u da Sadiq.
Sai da na shiga mota sannan suka koma gefe suna mgana da Anty Surayya na wani Lokaci sannan suka yi sallama ya lekoni yana fadin"Siya Good Night"
Sannan ya sumbaci goshina Surayya na fadin"Sadiq ba kunya a gabana."
Ya matsa baya yana dariya.
Tun a mota muka fara hira da Anty Surayya da muka je gidanta ma na jima afalo muna Hira har da mijinta sai da na fara jin barci ta kaini inda na ke sauka tace na yi wanka na Huta.
Ta kuma kawomin man zafi na shafa aiko ina yin haka sai barci.
Da safiyar idi kuma an tashi da hidima duk yadda naso na taimakamata hanani ta yi, tace na shirya in zan iya mu tafi masallacin Idi nace mata zan iya.
Ta bani kayan da Assadiq ya yi min kala uku leshi daya Atamfa biyu.
Atamfar na saka an dinkamin Buba kamar an aunani Cif dani.
Sai bakin Hijabi sabo saboda Fatata sai ya yi min bakyau kamar wata baturiya. itama ita da mijinta da ya'yanta sun yi kyau sosai shi ya tukamu zuwa masallacin idi.
Chan muka had'u da Assadiq da Abba bayan an sauko masallaci sun sha Fararan kaya har da manyan Riguna.
Sama sama muka gaisa yace sai ya zo gidan.
Da muka koma gida abinci muka ci Sinasir Anty Surayya ta bada aka yi mata, ni kuma bayan na ci na koshi na koma daki na kira yan'uwana da abokan arziki na yi musu barka da Sallah da Ramatu ne muka jima muna waya.
Bayan mun gama na ijiye wayar na kwanta sai bayan azahar na tashi Anty Surayya tace na sha barci har Sadiq yazo ya tafi.
Sai da na yi salla ta kwasomin kayan da ta siya na jarirai shago guda ina ta kallo ina saka albarka
Mun dade muna Hira da ita ta na kara bani baki akan Umma ta na tabbatar da zata sauko watarana.
Sai Dare Assadiq ya dawo bamu wani jima muna Hira ba ya tafi saboda na fara jin barci washegari ma Dangin mijin Anty Surayya ne suka zo.
Shiyasa bamu je gidan su Assadiq ba sai Washegarin sallah da kwana Biyu.
Na sanya leshin nan Shima dinkin Buba ne, ya zauna a jikina sai na sanya Hijabi kalan adon leshin.
Muna mota Anty Surayya ke fadamin Saboda ni yam'uwanta wannan sallar ba wanda yazo gidanta. Kuma sun saba a jiya kannen nata suna zuwa wajenta su yini.
Muna zuwa gidan ko suna nan a shashen Umma, Sadiya da Sajida sai Sa'adatu Saddiqa kuma Tunda ta koma bata zo ba, ya yi kusa da yawa.
Shashen Mama duk ya'yanta ne su Sa'ima da su Shahida har Salima ma tazo sallah.
Dukkansu kuma a shashen Innani muka gansu dukkansu kuma na bi su na gaishesu suka amsa min a wulakance, wasu ma ba su amsani ba.
Innani kuma ta karbeni cikin Fara'a kamar yadda ta saba min na riko mata Turare daman tundaga Zariya na bata ta karba ta na ta saka albarka su Sajida nata tabe baki.
Umma kuma har bangarenta mukaje na gaisheta sai a ranar ta amsamin da lafiya.
Daman kuma bangaren Mama muka fara zuwa muka gaisa, Abba kuma baya nan sun fita da Assadiq.
Anty Surraya tace mu zauna a bangaren Umma, ita kuma ta bi Umma ciki ban san me suke Tattaunawa ba.
Na jima zaune ni kadai sai ga Sultana ta shigo da irin less din dake jikina.
Kallon kallon muka yi ma juna ina shirin na gaisheta naga ta yi tsaki ta wuce kawai.
Kiran sallar mangariba yasa su Sajida suka baro bangaren Innani zuwa Falon Umma.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.