Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 39 of 86
Dagachan Gusai ba su yarda sun gayama su Abba suna tafe ba, Mijin Surayya ya dauketa ita da su Umma da Mama da Innani sauran kuma mijin Sa'ima ya Tuka su, sai kuma Direban mijin Sadiya shima ya ba su mota dai uku duka kuma gidan suka tafi, megadi kawai aka bari mallam Taju ya na binsu da Fatan isa lafiya da kuma Allah ya tashi kafad'un magajin gida.
Da azahar suka isa can suka iske Tahir ya iso shima Tun safe sai dai sun samu hankula sun kwanta Tunda sakamakon Hoton kai ya fito kuma komai Normal buguwar ba ta shafi kwakwalwar kansa ba.
Kuma an fito da shi daga Emergency zuwa daki na musamman Cuwukan ne kad'ai suka samu Dressing ammh karayan ba'a Daura shi ba Abba suna ta shawaran in da za'a bar shi ko anan din ko kuma a kaisa asibitin dala kano a yi masa Daurin asibiti.
Har alokacin Sadiq barci ya ke yi a wahale sai dai ance da safe ya farka yana ta kukan kansa.
Dukkansu matan nan da kuka suke Fitowa daga dakin nan Sultana kam ta kasa shiga ma saboda tashin Hankali a ranar ma sai ga su mallam Shitu da su Goggo Hassu sun zo suma cikin Tashin hankali.
Saboda yanayin Tsamin jikin Sadiq yasa mallam Zakari yace a barsa anan a yi masa Daurin asibiti ammh in fa akace za'a rika Kai can da mara lafiya nan za'a iya samun matsala.
Domin shi Baba Sammani yace gwara a yi Daurin gida zai fi yin kyau..mallam zakari yace halin da yake ciki za'a duba.
Karshenta dai aka tsaya a matsayar anan kaduna zai zauna a yi masa Dorin asibiti a gani, kuma Abba na saka hannu ya bama likoticin dama sukace a daran za su daura shi.
Abba bai bar su Umma ba saboda Innani Tunda suka zo ta ke faman koke koke, daga asibitin gidan Alhaji jibril suka tafi sallah dagachan kuma yace su kama hanyar Gusau inda ma yaji dad'in ganin mazajen su Surayya sai ya samu salaman cewa zasu kula da iyalansa.
Maallam Zakari ma Abba ya yi ya koma gida yace yana nan sai yaga yadda Jikin Sadiq ya yi.
Tahir ma da ya yi zuru zuru yace yana nan sai zuwa gobe ko Jibi zai koma ganin haka yasa su Baba Sammani suka juya zuwa shinkafi su da su Goggo Husai a ranar.
Ita Surayya ba ta bi su Umma gidan Salima ba, ta tsaya a asibitin tace anan zata yi sallah abinci kuma bazata ci ba, suna ta waya da subai ne da ta taso daga kano
Saddiqa kuma gobe zata taso daga Kebbi gabadaya hankulansu yaki kwanciya, Shahida ma ta iso daga katsina dazu kowa ka gani Fuska ta jeme sai jan ido kawai.
Shiyasa bata san abunda ya faru ba, ashe suna fita daga asibitin nan Umma ta bama Sadiya da Sajida kudin mota tace suje Zariya su fattaki Hasiya daga Rayuwar Sadiq su tabbatar da bata kara marmarin kusanto Rayuwarsa ba.
Mama ce kara zuga Umma tana fadin ai wannan yarinya ba matar zama ba ce Annoba ce
Tunda Sajida tasan gidan ita tayi musu jagora Umma tace su yi sauri zata san yadda tayi suka b'ata Lokaci kuma Surayya bata fahimci komai ba.
Ko tasha ba su je ba, a bakin hanya suka samu mota duk da Tsadar da aka yi musu suka shiga hakanan sai Zariya.
**********
Zariya.
Tun ranar da Assadiq ya bar ni zuwa Abuja na ke ta kiran wayarsa a kashe, har washegari to ban damu ba sai na yi Tunanin kila babu chaji ne.
Ko aiki ya yi masa yawa zai kirani Daga baya, ban kara shiga damuwa ba sai da naga har dare bai neme ni ba, kuma na kara kiransa har Lokacin wayarsa a kashe.
Ranar barci na rabi da rabi ne, sai kuma da safe na tashi da sanyin jiki da faduwar gaba.
Haka kurun nake jin wani iri acikin jikina.
Ranar na kira wayar Assadiq ban san adadi ba, in nace bari na kira Anty Surayya sai na kasa sai nake ganin kamar zata ce na cika zakewa ne shiyasa na kasa kiranta. sai dai na kasa natsuwa ina ji araina da wani abu ni bai saba min haka ba, abunda bai taba Faruwa ba.
In dai Assadiq ya tafi Abuja yana isa zai kirani ko ya yi min sakon cewa ya isa lafiya ammh yau har an kwana Biyu ban ji daga garesa ba.
Daman na bari ne zuwa dare in ban same sa ba daga baya zan kira Anty surayya naji ko ita sun yi waya da shi.
Allah sarki bansan abunda ke faruwa ba, ita kanta Surayya tashin Hankalin da ta ke ciki ne yasa ta manta da Hasiyar kwata kwata ballatana ta kirani ta fad'amin.
Tun safe ina kwance kamar ruwa ban iya yin komai ba abinci ma Maman suhailat ta aiko min da Doya da miya naci na sha ruwa dakina kaca kaca cikina ya yi nauyin da yanzu ban iya moruwa. sai dai na kwana in an kira sallah na tashi nayi gabadaya hankalina baya jikina.
Wajen biyu da wani abu na rana naji ana bugamin kofar d'aki kamar hauka abunda ya bani tsoro shine jin ana ta mganganu kuma naji muryan Maman Suhailat na kiran sunana.
Sai na Rarumi dankwalina na taka da Cikina a gaba naje na Bude kofar sai dai me? Ko gama Bude kofar ban yi ba aka Bugo min kofar saman cikina sai gani na yi baya na fad'i a kasa Dabas.
Ni dai ina ji Maman suhalat na salati kuma naga sanda yan'uwan Assadiq suka tsallake suka shigo dakin suna fadin"Bakar Annoba zo ki fice daga Rayuwarmu mun gode, ammh bazamu bari ki karisa mana Dan'uwa ba."
Maman suhailat ita ta kamani ma mike ina raba ido, Sajida ce tsaye a gabana ta nuna ni da yatsa tana fadin"Ki kwashe kayanki kaf ki bani key din dakin nan zan Rufe dakin zaman ki da Dan'uwan mu ya kare, tunda burin ki ya cika kin kusa kashe shi."
Sai Hankalina ya tashi cikim Rawan murya nace"Me ya faru da Assadiq din?
Kusan ni da maman suhailat muka yi tambayan a lokaci d'aya.
Ban tsamnani ba sai da naji Sajida ta kwasheni da mari sai da na fad'a jikin Maman su Suhalait saboda azaba.
Ta kuma nuna ni da yatsa tana fadin"Har ki ke da bakin tambayata? To yana chan a gadon asibiti ya karareaye duk kuma saboda ke bakar Annoba da Jaraba, Saboda haka Umma tace mu zo mu sallame ki, ki kara gaba ki yi nesa da Rayuwar Dan'uwanmu in ba haka ba ke zaki rasa taki rayuwar."
Hankalina ya tashi cikin Firgici na fashe da kuka na kasa mgana.
Maman suhailat ce ke fadin"subhanallah ku tausaya mata baku ga halin da ta ke ciki ba ne?
Sadiya tace"Mu kuma baki ga Halin data sakamu ba ne? Daga wajenta ya ke ya samu hatsari ya na chan baisan inda kansa ya ke ba, kuma kice mu kyaleta wlh sai ta kara gaba malama ki zo ki kwashi kayanki ko mu yi miki watsi da shi.'"
Ni ban damu da kaina ba irin Assadiq da akace yana chan baisan inda kansa ya ke ciki ba.
Duk da halin da nike ciki haka na Duka ina rokon su gayamin inda Assadiq ya ke su kuma barni naje na gansa daga baya sai na tafi ammh sukace ban isa ba.
Ganin zasu faramin watsi da kaya yasa Maman suhailat tace na bar kuka na shiga na had'a kayana su Sajida ba su da Mutumci.
Ina kuka harda majina na had'a kayana akwati biyu Maman suhailat na tayani, su kuma suna Tsaye zagi da cin Mutimci sai wanda suka manta. ni kuma ina ta Rokon su, su barni naje na Duba Halin da Assadiq yake ciki sukace ban isa ba.
Kaya kawai suka bari na Dauka na Dauko wayata suka kwace da jakata suka caje komai suka kwashe kudin ciki har da Atm dina, Hijabi kad'ai suka barni na saka suka Turoni waje suka rufe dakin su kuma saka key din a jaka.
Allah yasa gidan dagani sai maman suhailat, itace ke ta ba su hakuri ba su ma tsaya sauraranta ba suka min kashedin ko da wasa kada na kuskura na kara nuna ma san kaninsu, na jira a duk inda na ke zan samu takardan sakina, mari da dunguri ba wanda ban sha shi ba suka tafi da komai suka barni Durkushe ina ta kuka.
Maman suhailat tajani dakinta ta na ta lallashina da bani baki.
Taso ma na kwana a wajenta kafin da safe asan mafita nace mata ta bani kudi zan tafi, sai dai ban nuna mata in da zuciyata ke rayamin naje ba.
Sai nace mata gidan Adda Fati zan tafi kamar ta sani sai ta bani 5k ta kuma rakani har bakin Titi na samu adaidaita.
Sai da muka d'au hanya sannan nace ya kaini tasha, motar gada zan hau gwara naje wajen Amma. Da naje na sauke ma Adda Fati halin da nike ciki gwara na tafi wajen uwata a wannan Halin da nike ciki lallashinta na ke Bukata.
Ina mota ina kuka kukan tunanin wani Hali Assadiq ke ciki, shi kawai nake Tunani a raina kuwa ina ta masa addu'an Allh ya bashi lafiya Allah Sarki ashe Shiyasa najisa shuru ashe ashe shi ga halin da ya ke ciki ban sani ba.
A cikin raina na yanke shawaran zan rabu da Assadiq ko saboda son da na ke yi masa na barsa ya yi rayuwarsa cikin salama sannan na kara aminta da maaganar mutane a kaina ni din Bakar Annoba ce.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.