Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 8 of 86

Kuma da ya koma sai ya kasa kiranta tunda ya rasa ta ina zai fara, sai gaahi ta kira da kanta , ta na mai tuni kan maganar da ya ce za su yi kai tsaye yace in zai gayamata zai kirata da kansa, Daga baya ma data matsa masa sai yace mata bakomai.
Ita kuma duk sai ta Damu, saboda tafi  kowa Sanin kanin na su ta tabbata akwai abunda ke damunsa.
Har ta fara Tunanin ko sun samu matsala da Sultana ne? Ta shirya taje har gida ta turketa ta tambayeta Sultana ta rantse mata suna zaune lafiya cikin soyayya, daganan sai ta sare sai Tunaninta ya bata ko daga wajen aiki ne?

Har megidamta ta yi ma mganar suka Tattauna shi yace koma menene kada ta matsa masa ta yi masa addu'a yadda ta ke da Sadiq ya tabbata da kansa zai zo ya fad'a mata da Damuwarsa.
Da shawaransa ta yi amfani ta kyalesa sai dai ta dukufa yi ma kanin nata addu'an koma meke damunsa Allah ya kawo masa mafita ta alheri.
Bata sani ba Allah ya amsa addu'arta sai dai kila mafitan ta yi jinkirin samuwa ko bayyana.

A satin da zai je zariya wajen Hasiya ya samu wayar Umma cewa Innani ba ta da lafiya, ta zame ta fad'i acikin Falonta yanzu haka ta na asibiti.
Hankali tashe ya kira Hasiya ya gayamata yace ta yi masa Hakuri ya je Gusai yaga innani, itama duk ta damu fadi take"Ka gaisheta Assadiq. Allah ya tashi Kafad'un Innani."
Ya rika amsawa da Ameen Hankalinsa ya tashi da wayonsa bai san Lokacin da innani ta kwanta asibiti ba, ko ciwo ta ke yi ta gwammace ta yi ta shan jike jike.
Yaje ya iske innani an dawo ma da ita gida, bayanta ne wato kugunta ya Bugu, zai zazzabi a jikinta likitoci sun ce a daina barinta ita kad'ai Tunda jikinta na Tsufa ne ta na Bukatar wani mataimaki.
Sai ga Innani kwance shuru baki ba mgana, sai ido kawai ta Saduda ta ga mutuwa.
Sadiq shi ya yi ma Abba mganar ko cikin ya'yan Su goggo Husai ya Dauko daya daga cikin su ta dawo nan da zama a sakata makaranta.
Wacce zata rika kwana da Innani ta na kula da ita.
Shawaran Magajin gida ita tayi aiki, Mutanen Shinkafin daman sun zo Dubata, Da Abba ya yi mganar da Dan'uwansa  sai yace akwai Autar Hussai, Farida ta na jss2 ne yasan zata iya kula da Innani.
Haka ko akayi ana mgana Hussai tace ta ba su Farida har abada, Kwana daya Tsakani ta had'o kayanta ta dawo Gusai da zama.
Cikin Sati daya aka sama mata Gurbin karatu a makarantar da su Sultana ke zuwa,kuma tare a ke kaisu Direba kuma ya Daukosu.
Sultana ita gidanta ta ke tafiya ita da Siyama mai tayata zama, ita kuma Farida ta na shashen Innani.
Gata ba ta da kiyuwa, ga son aiki da kazar kazar Umma da Abba sun yaba da ita sosai.
Innani duk masifarta sai da ta ragama Farida ganin yadda ta ke hidima da ita, sai dai suna tafka tsiya in Tace zata yi ma Innani Jagora ko zuwa daki ko makewayi.
Sai Innani ta fara fad'an ita ba makaunniya bace kada Farida ta raina mata wayau mana.
Ita ko sai tace to in ke ba mahaukaniya bace ki cire gilashin mana kuma ki yi tafiya ba sanda mu gani.
Da Innani taji haka sai bakinta ya Mutu, tasan Faridan na taimakonta kuma duk inda Mutum ya ke Rahama ne, ta na jin dadin jin motsinta kusa da ita ballatana da tare suke kwana su tashi, bakin Innani ya Bude hira chau cau, labaran tsoffin garin shinkafi ba wanda Innani ba ta bata ba, har da Labarin kakarta da irin kishin da ta yi da Innani, yo ina ruwan Innani watarana ma cikin zencen har Hussai din ta ke zagewa in yan tsiyanta suna wajen
An dai samu ta Rage tsine tsine ammh fa watarana in aka tabota yini zatayi Allah ya tsine ma uwar barawo tun ballatana in ta ajiye abu bata gani ba, wani Lokacin kuma manta inda ta ijiye take yi sai ta fara jan Hanci ta na Tsine ma barawon da bata gani ba da Danginsa gabadaya.

*Janafty*
*TMWBK3003*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/IhAz8h8nRy250ZnGGXwM65

Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641

*Bayan Wattani Uku.*

Wattani ukun da suka shud'e na yi su ne cikin farinciki tare da tsananin kulawa ta bangaren Assadiq da yan'uwana, Tunda a yanzu cikina na cikin wattani na shida da kwanaki ne har na fara Awo a asibitin musulmi. duk da Assadiq yaso na sauya asibiti, ni nace ya barni anan saboda Cousin din Safiya Sister Zainab, mun saba da ita sannan ta na kula dani, tare da bani shawarwarin da suka kamata.
A yanzu haka mun samu Hutun First Semister ina gida in da Allah ya taimakeni kenan, saboda Cikina ya yi wani irin girma na ban mamaki kamar ya na cikin wata na tara.
Ban yi kiba ba, sai dai na Kumbura kafafuwana da hannayena tare da Fuskata, komai ada da ya ke karami yanzu ya koma Babba.
Na zama wata katuwa sai Ciki mai Tsini ta gaba, ga uban nauyin da cikina ya ke yi, ina jinsa har a jikina Da Kafafuwana kuma har a asibitin na yi Korafi suka tabbatar min da komai lafiya namiji suka gani shiyasa na ke jin nauyin cikin a jikina.
Tuni na daina Amai, sai dai na kan yi in naci wani abun da cikina ya kasa karb'a Miyau kuma na daina ammh wani Lokacin sai na kasa had'iyam miyau sai na Tofar da shi.
Zazzabin dare shima ya tafi, sai kananun cuwuka da ba'a rasa ma su Ciki da shi.
A baya na dauka cewa iya son da na ke yi ma Assadiq ya isa ya rikeni ni da shi a zaman auren mu, Sai daga baya na Fahimci nima ina bukatar Soyayyarsa, Kuma sai a lokacin na kara tabbatar ma da kaina Assadiq ya na sona kuma zai iya komai Saboda ni. Kuma ya na son cikin jikina ya na kuma Burin samun Tsatsso daga bangarena.

Gatan duniya da Miji ke yi ma matarsa Assadiq na yi mini shi, Har fiye da zato na da Tsammanina, Ko da yaushe cikin kira na ya ke yi yaji Lafiyata, in kuma ya samu sarari ko ba ranar zuwansa Zariya ba ne zai samu lokaci ya zo ya ganni ko da bazai kwana ba.
Bai taba bari na yi kukan wani abu ba, Duk abunda na ke so kafin nayi mgana ya riga ya yi min shi.
Kayan abinci wani baya karewa ya ke tarar da wani, komai na Bukatar macen kwarai a gidan mijinta Allah ya bani shi ta bangaran Assadiq ta ko'ina Rayuwata ta inganta.
Kudi bani da matsalansu har ma ina taimaka ma yan'uwana, Amma ma dagachan bangaran ina taimakon su da iya abunda na ke da shi.
Sun zo kwanaki ita da Adda suka Dubani ba su dai kwana ba ne, Amma daman bazata iya kwana a wajena ba, da ma dai gidan Adda Fati ne, gidan Adda Rukayya daman Saboda Mijinta ba ta cika ganin baki ba.
Bangaren Maman Suhailat itama Tsakaninmu sai godiya sosai ta ke kula dani, in dai ta na gida sau ukun nan zata lekoni taga lafiyata shiyasa da Assadiq ya yi mganar kayan Haihuwa da nawa nace ita zan bamawa ta Siyomin ta na da kirki.
Nasan yadda zaman gidan haya ya ke, ana samun mutanen kirki da na banza ita dai maman Suhailat ko da ta na da wani halin to kirkinta duk ya shafe wannan.
Ramatu da tazo ta ga irin gatan da na ke ciki sai da ta kara dawomin da mganar da ta tab'amin shekarun baya.
Ta kalleni da tsinin Cikina a gaba kafin ta yi mirmishi tace"Kawata daman ai na fad'a miki watarana Zaki ji dadin Rayuwa kamar kowa koma fiye da kowa."
Na kalleta cikin mirmishi kafin nace"Hakane wlh gashi komai ya wuce sai dai Tunawa."
Ramatu tace"Kin tuna na sha gayamiki Daga salisu har Abubakar ba su ne gwanayen ba  gwanin in  yazo Shine yardaddaje har a wajen Ubangiji ki ka yi ta min musu kina ganin kamar haka bazata faru ba, yau gashi kin samu fiye da zaton da na yi miki Fata Hasiya."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.