Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 6 of 86

Ya na mgana ina jin zuciyata na kara narkewa cikin soyayyarsa, ina jin na gama yarda da shi, ko da baya so na to ina da matsayi mai girma acikin Rayuwarsa.
Abu daya na ke so na kara sani, shine me yasa ya kaini aka sakamin Implanta?  Tunda yace ya na sona meyasa ba ya son had'a zuru'a dani?
Kai Tsaye ya Dago ni muna kallon juna, sumbata ya ke shirin yi na yi saurin kauda kaina ina nuna masa bakina da ya fara cika da miyau.
Sai ya yi dariya ya mikamin ledan da har miyau ya fara taruwa ya taramin na Zuba, ina kallonsa ya ijiye ledan a gefensa ko kyamkyami ba shi da shi.
Cikin mamaki nace"Baka kyamkyamin Miyau Assadiq?
Cikin sauri yace"Ina da kyamkyami mana, Sai dai ke ce ban isa na yi kyamkyamin ki ba, abunda ke sakaki miyan ai ni ne na Digasa ko?
Zai sake rikoni na yi saurin kwace kaina ina fad'in"Ka bari na wanke bakina."
Ya na dagamin gir yace'To miye?
Ban kulasa ba na shige ciki da gudu sai da na sake yin brush sannan na dawo, kuma bai yarda ba sai da ya kama Fuskata muka sumbaci bakin juna na wani lokaci sannan ya kalleni ido cikin yace"Siya soyayyarki ce taja min duk abunda na zama yanzu, Wallahi kin ji Rantsuwan musulmi ban taba kyamatar komai da zai Fito daga Tsatson ki ba Hasiya, a lokacin bani da mafita ne, sai ta hakan dalilina shine ba na so ki samu ciki har ki haihu iyayena ba su san da ke ba, ba na so abunda zamu haifa ya zo ya Fuskanci laifin da ba shi ya aikata ba, Daman ina da niyar in komai ya Daidaita na gaya miki da kaina sannan na kai ki a cire miki, ammh har ga Allah har acikin zuciyata Siya bani da wata manufa ta sharri ko kin had'a zuru'a da ke daga bangarena."
Ya karishe fad'a ya na kallona nima shi na ke kallo ammh na kasa mgana.
Zuciyata daga chan gefen ta na gasgasta shi, wata kuma na Kokarin nuna min ba haka ba ne.
Ganin haka yasa ya kara rike Hannayena ya na fad'in"Ki yarda dani Hasiya wlh ba karya na ke fad'a miki ba, ki Fahimceni."
Sai na lumshe ido kafin na bude ina kallon yadda ya marairaicemin kamar wani maraya, lokaci daya kuma ya na shafa Tafin hannuna cikin wani irin Salon da ya sa, sai da tsikar jikina ya tashi.

Bani da zabi illah Aminta da Assadiq domin nan duniya bani da wanda ya fisa cikin gyad'a kai nace"Na Aminta da kai Assadiq, na kuma Fahimceka na kuma yarda cewa baka na gudun had'a zuru'a dani saboda Canfi da ke kaina ba ne"
Da Sauri yace"Astagafurullah.! Kada ma ki kara wannan Tunanin, ni ban yarda da Canfi ba , sannan ina da ilimin addini nasan Allah ke yi ba Mutum ba."
Sai na yi masa mirmishi ina jin zuciyata na samun natsuwa kafin na koma saman kirjinsa na kwanta ina Fadin"Assadiq ya kamata ka yi saurin sanar da iyayenka mganata kafin na haihu ko?
Ya na shafa kaina zuwa bayana yace"In sha Allahu, zan sanar da su kada ki damu."
Sai na jinjina masa kai shuru muka yi kafin ya muskuta ya na fadin"Daman Alhaji Jibril baffan ku ne Siya?
Sai na Dago ina kallonsa kafin nace"Na kaduna?
Sai ya gyadamin kai, cikin mele baki nace"Eh kanin babanmu ne, ammh da ya ke sanadina yasa tunda babanmu ya rasu ba su duba bayansa ba, a cewarsu duk wanda ya rabemu shima zai iya rasa komai na shi."
Shuru ya yi kafin yace"Mutane yanzu sun saki Allah sun kama boka da mallam, da kuma Canfe canfan banza da wofi, mutane ba ikilasi ba Tauhidi, sun manta da Allah shi ne Allah, komai baya faruwa sai da cewarsa da kuma Umarninsa."
Ina jikinsa har a Lokacin idanuwana suka kawo kwallah kafin nace"Farkon Rayuwata na taso cikin Farinciki, Daga baya ta juye zuwa kunci da bakinciki na shiga Tsaka mai wuyar da kai ne ka fitar da ni acikinsa Assadiq don Allah ko da iyayenka ba su karbeni daga Farko ba, kada ka Juyamana Baya ni da cikin da ke jikina."
Sai kawai na fashe masa da kuka ina Rokon kada ya zabi sultana ya rabu dani kai tsaye yace"Kamar yadda Saboda ke ban barta ba, ke ma kuma saboda ita bazan barki ba Siya".
Sai na kara kamkamesa ina ta kuka, shi kuma ya na aikin lallashina.
Daganan kuma daga lallashi sai kuma ya fara kokarin nuna min yadda ya yi kewata.

A nan saman kujera mun kasa ko shiga ciki komai ya wakana, ni kaina nasan na yi kewar mijina, shima haka ballatana ga cikin jiki, Sai dai muna Samun natsuwa na mike da gudu sai Tiolet naje zubar da miyau shi na bari da tattara mana kayanmu, ni daga nan tubewa na yi na tsabtace jikina.
Ko da na fito ya shigomin da akwatuna ciki tare kayanmu da muka yi falati da su, shima wanka ya shiga ya Tsabtace jikinsa.
Dagani har shi ba ma jin yunwa, nad'ewa muka yi a gado muna sake Sabon Hira ya kashe wayarsa gabadaya Saboda yace yanzu lokacina ne.
Muna kwance a kan filo daya fuskokin mu na kallon Rufin Dakin, hannayemmu sarke a waje d'aya, Juyawa na yi na rab'i da rabin jikinsa na kira sunansa"Assadiq?
Da sauri yace"Uhm SiyaAssadiq."
Ina shafa gemunsa nace"Ya ku ka kare kai da abokin ka din nan? Domin nasan yasan har yanzu muna tare.?

Assadiq ya yi shuru saboda baya so Hasiya tasan a kanta sukayi fad'an da ba su taba yi da Tahir.
Sun rabu zukata ba bu dadi kuma Daga Lokacin ba su kara neman juna a waya ba.
Ba kuma wani abu ya had'a su ba, sai Tahir da ya ke jifan Hasiya da kalmar Annoba sannan ya na rainata Saboda ita bazawara ce, kuma ya na kokarin nuna masa ya saka Rayuwar Ahalinsa a bala'i tunda ya kasa rabuwa da Hasiya.
Yasan ya yi kuskure da ya yi masa karya ammh Hasiya matarsa ce kuma Sirrinsa bazai taba bari wani ya ci zarafinta ba Shiyasa ya yi ma Tahir Tsawa akan kada ya kara aibata matarsa in kuma ya kara sai ransa ya baci, shikenan Tahir yace yaje tunda ya zabi hasiya sama da shi, ya bar shi duk sanda ya gane kuskurensa ko ta kwabemasa yasan zai nemesa.
Shima a lokacin ransa ya baci shiyasa har yanzu bai ko nemesa ko ta waya ba.
Sai da yaji muryata ina kara fad'in"Uhm ka yi shuru?
Da Sauri yace'Na fad'a masa gaskiyan cewa muna tare yanzu."
Kai Tsaye nace"To me ya ce maka?
Ajiyar rai ya sauke kafin yace"Me kuwa? Abokina ne fa ba Ubana ba Hasiya, ba shi da ikon zab'a min Ra'ayina"
Sai na yi shuru na kasa mgana,Ammh na Fahimci shi da abokin nasa ba su yi Rabuwar dad'i ba.
Gudun kara Tabarb'arewan al'amarin yasa na yi shuru da bakina.
Sai dai na kara lafewa a jikinsa ina fad'in"To ka na Tunanin a yanzu bazai gayama kowa ba?
Sadiq yace"Da zai fad'a da Tuntuni ysa fad'a, nasan Tahir bazai taba fad'an komai a kan ki ba, sai dai in dan ni ne na Bukaci hakan."
Ajiyar rai na sauke kafin nace"Allah yasa komai ya zo da Sauki Assadiq."
Cikin jinjina kai yace"In sha Allahu Khairan Siya ta."
Daga haka ya Rumgumeni yace mu yi barci ya gaji, kamar wasa sai ga shi barci ya kwashemu dagani har shi, sai dai ni miyau ne ya rika tadani da na mike daman ya san miyau ne ya cika bakina.
Muryansa cikin barci yace"Miyan nan ba shi da magani ne Siya?
Ina kara kwanciya ajikinsa nace"Likita yace for now dai babu, ammh yace zuwa gaba zai rage."
Kara rikeni ya yi cikin barci barci yace"Ya na takura min mata ne Shiyasa."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.