Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 3 of 86
Ta daukomin Hijabi da takalmi na saka ta tambayi jakata na nuna mata ta Dauko harda wayata a ciki, akwai Kudi a hannuna sannan ina da shi a banki, daman Akwai Atm aciki Tana Rirrikeni dani muka fito ita ta kulle Dakin nan muka had'u da maman Sulahait ta na ganina ta fara salati ta na fadin"Na shige su Hasiya daman kin dawo? Baki da lafiya ne naga kin dashe kin yi uban fari kamar wata mai yaron ciki?
Ni dai halin da na ke ciki bai barni nayi mgana ba Safiya ce ke fad'amata na dawo kila Ciwon ya kwantar da ni, Sai ta Fara fad'an ana zaman makota kuma sai na yi shuru ban iya kiran kowa ba.
To ni Allah na Tuba ina cikin wani yanayin da ba na iya gane komai ma da komai, Safiya na rikeni da ni muka fita bakin titi muka samu adaidaita, muka hau ta tambayeni wani asibiti muke zuwa nace mata ta kaini kowanne, sai tace muje asibitin musulmi akwai Cousin dinta na aiki a wajen, tun ma muna adaidaitan ta kira ta ta fad'amata sai tace mata tana asibitin sai mun zo.
Saboda ita yasa muna zuwa ba Dadewa naga likita, ita ta yi mana shige da fitan siyan kati da Sauran su, likita na min Tambayoyi ina amsawa daganan ya turani dakin da za'a dibi jinina da Fitsari sannan yace na galabaita zasu Rikeni su gani zuwa yammah.
Ni dai gani nan kwace kamar ruwa a wani office mai Dauke da karamin gado na marasa lafiya.
An dibi jinina sannan Wata Nurse ta rakani Tiolet na yi fitsari a wani Roba sannan na dawo na kwanta Safiya da wannan yar'uwanta na ta ke ta Shiga ta fita a kaina har sai da aka sakamin Drip, abu d'aya ke damuna miyan bakina da baya yankewa, sai da Safiya ta sama min leda ina tofawa aciki, ko fa Barci na ke yi in miyan nan ya Taru sai na tashi na zubar da shi na ke samun sukuni.
To yau din ma haka ya faru barci ya kwasheni ammh bi ni bi ni Miyan bakina ke tadani, kwata kwata na kasa gane kaina, zuwa yammah sai na samu karfin jikina sosai har Safiya ta fita bakin asibiti ta siyomin kayan marmarci naci, kuma tace ta Duba wayata ba Chaji balle ta gayama yan'uwana.
Ni kuma sai nace ta kyalesu kawai tunda naji sauki, sai da ruwan ya kare na koma gaban likita, daman kananan Roba biyu aka sakamin sai babba guda daya.
Abunda Likita ya fad'amin ya sandar dani, ya na mikamin Result din da suka gani acikin jinina da fitsarina, ammh na kasa karb'a saboda Tashin Hankali da mamaki.
"Ciki gareni ni Hasiya, haka likita ke fad'amin har na Tsawon wattani biyu da kwanaki."
Sannan ya Cigaba da bani shawarwarin cin abinci ko da zan yi amai sannan da samun cikakken Hutu da natsuwa, sai kuma yace ina da maleria a jikina sai na kiyaye, ya Rubutamin maganin karin jini na samu ciki sai paracetomol sai mganin Maleria.
Na fito rike da Takarda a hannuna ina tafe miyau ya cika bakina, har mganar Miyan na yi masa yace na yi hakuri zan bari zuwa wani Lokaci, ammh yanzu na rika cin cingam ko shan minti.
Safiya na ganin na fito ta zo ta rikeni muka samu waje muka zauna.
Ta karbi takardun hannuna ta na fadin"Me likitan yace?
Kai Tsaye nace"Ciki gareni Safiya."
Sai ta washe baki ta na fad'in"Daman Sister Zainab ta fad'a tace ta na Tunanin ciki ne, kai Congratulation kawata na yi miki murna soon to be come a mother."
Ta fad'a ta na dafa kafad'ata cikin murna sai kawai na bi ta da kallo ammh na kasa mgana sai dai na yi mata ya ke, takardan mganin ta Duba ni kuma sai na kalleta ina fad'in"Magunguna ne ya Rubutamin akwai sauran kudi a jakar ko?
Sai tace"Akwai kudi ammh ba su da yawa 5k na gani kuma kinga an siya kati an biya kudin ganin likita sannan an Rubuta ruwa da alluran da aka yi miki."
Ina Rausayar da kai nace"Akwai kudi a cikin bankina, ki yi amfani da Atm dina."
Sai ta amsamin da Toh, kafin tace bari taje ta dawo.
Nan ta barni ina zaune ina Tunanin, makomata, shin makomar Tafiya ko kuma makomar zama ne?
Ina shafa cikina ina hawaye to in na tafi ina zan kai wannan gudan jinin da ke cikina?
Ashe akwai rabo mai karfi a tsakanina da Assadiq, Shiyasa har aka gano wannan Implant din ajikina aka Ciremin shi Saboda wannan Rabon da zai Shiga Tsakanina da Assadiq.
Lalle na kara Shiga cikin Tsaka mai wuya, ni dai bazan zubar da cikin jikina ba sanman bani da tabbacin Uban cikin zai karbesa Tunda tun asali baya so ya had'a zuru'a dani.
Hango su Safiyq na yi da yar'uwanta yasa na yi goge hawayena har suka kariso.
Congrarulation Sister dinta ta fara yi min, na amsa ina ya k'e, Safiya ta nuna min magungunar da ta siyo min ita kuma yar'uwata ta zauna gefena ta na bani shawarwarin yadda zan kula da kaina ina gyad'a mata kai.
Sai shidda Saura muka bar asibitin muka koma gida, Safiya tamin kokari Daman ta jini shuru ne ban je makaranta kuma bata samu na a waya Shiyasa ta zo, ba ta tafi ba sai da tambayeni abunda zan ci nace ta dafamin shinkafa da mai da yaji ita na ke sha'awa.
Sannan ta sakamin Ruwa na yi wanka naji karfin jikina, ta na nan maman Sulaihat ta shigo, ta na ganin ina tofar da Miyau a leda ta fara fad'in Allah ya inganta tun ballatana da taga Safiya na dariya sai ta san abunda ta ke zargi ne, gashi kuma rame na yi wani irin Fari fayau da ni.
Safiya sai da tayi mangariba ta tafi, tace zata rika sakamin Attendence in kuma za'a yi test zatamin kafin naji sauki na dawo makaranta.
A haka muka rabu bayan na yi mata godiya sosai.
In da Allah ya taimakeni Maman Suhailat ke kula dani, zata shigo da Safe da rana sannan da yammah , tace me zan ci? Komai kuma nace ina so zataje dakinta ta dafamin, in ba ita ba yarta ta dafamin, ita kan zo ma tamin Share share ko ta sakamin ruwan wanka, Ummi dai ta shigo ta gaisheni ita da matar da ke dakin Fadila yanzu.
Ina cin abinci ammh ba sosai ba, Sai dai abinci na daga Tuwo sai Fate , sai kuma Shasshaka na ke iya ci sai kuma Kunin tsamiya.
Sai kuma kunzo saboda Miyan da na ke yi, ba domin maman suhailat ba da na zama kazama.
Wayata kuma tundaga ranar ban kara kunnawa ba, ta mutu ma ba chaji Adda Fati ma ta ji ni shuru kuma wayata a kashe yasa ta aiko Habiba ta Dubani sai ta iskeni kwance ina Fama da Farin baki da miyau.
Ta koma ta gayama Adda Fati sai gata tazo, ni da bakina ban fad'a mata ina da ciki ba ita ce ta gane, kuma itace ta gayama Ramatu da Adda Rukayya.
Amma kanta Adda Fati ta kira ta ta na Fad'a mata ina ta fama da Laulayi.
Ta kirani ta gaisheni har da hawayenta na Farinciki nima yau zan zama uwa, Ramatu da Adda Rukayya duk sun zo dubani.
Abakin su naji na koma kamar Zabiya saboda hasken da na kara sannan dagani cikin nan zai sakani rama Sosai.
Suna ta dai zencen su, Saboda ganin ba na iya komai yasa Adda Fati ta ce Habiba ta zauna da ni har sai na ji sauki na kama jikina, nace mata da ta bar shi Maman sulaihat ma na kula dani, sai tace sai a barta da Wahala? Har daki Adda Fati ta shiga ta yi mata godiya tace bakomai kamar y'a ta Daukeni.
Wasa wasa sai da na kwashe kwana goma sha ina kwance sannan naji sauki na mike, sai dai ban daina kwana da zazzabi ba, sannan ga Miyau ni shi yafi damuna ba, haka zaka shiga cikin Jama'a ka na fama da Miyau?
Sannan Tun naga nafi Sati Biyu Assadiq bai biyo bayana ba na kara Tabbatar da ma da kaina zama bai ganni ba.
Duk a tunaninsu Adda Fati Assadiq ya zo ya dubani ya koma ne, ganin bani da matsalan komai yasa ba su kawo ma wani Tunani ba.
Sati daya Habiba tamin nace ta koma gida naji sauki, ranar da na cika Sati biyu Ranar lahadi, daman a ranar na gama kudurin Tafiya wajen Amma Tunda naji sauki.
Zama na ba shi da amfani , bazan taba Damuwa don Assadiq bai karbi Cikin jikina ba, ni dai ina son kaya na kuma zan renesa na haifesa ko da shi d'in baya bukatar haka.
To ta ina zai bukaci haka Tunda ba Sultana bace? Ni fa daman taimako na ya yi, baya so na ban dace da Rayuwarsa ba shiyasa ba zai zo ya had'a wani abu da ni ba.
Safiya ta dawo wajen sau biyu ta Dubani, ta yi ta min fad'an na kunna wayata sai na yi mata karyan inaga ta lalace tunda na yi ta kunnawa taki kawowa.
Misalin karfe sha daya da wani na Safe ne, na yi wanka na shirya cikin Doguwar rigar abaya baka sai na saka Hijabi saboda na rame.
Na adana komai Saboda bansan yadda Tafiyar tawa zata kasance ba, ammh ina ji a jikina ba ta dawowa bace.
Na janyo akwatina babba da karamar sai karamar jakata da na saka Muhimman abubuwana, na yanke shawaran zan ce ma Maman suhailat cewa zan je wajen mafiyata Saboda Mijina sun tafi wani aiki kuma zai Dade bai dawo ba saboda gudun zargi.
Da wannan shawaran na saka Takalmi na janyo akwatina kii sai kofar Daki na saka hannu na bude da makulli sannan na Cire makullin a Hannuna.
Ina Bude kofar, ya na karisowa wajen kamar ko daman ya na wajen ne ni dai ban sani ba.
Na dai gansa kaawai a gabana, ya na kallona nima ina kallonsa cikin mamakin ganinsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.