Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 4 of 86
ASSADIQ ne sanye da kananun kaya Riga da wando fari da baki sai jaket da jakar baya, duka Hannayensa na cikin Aljihun wandonsa.
Yadda na ke kare masa kallo shima haka ya ke karemin kallo.
Cikin mamakin ramar da na yi masa har a ido, ni kuma naga ya yi kiba sannan ya kara haske.
Sai naji Duhu ya mamaye ganina na kishin Tuna amarci fa ya ke yi ai Dole naga ya sauya.
Kawai sai na juya masa baya ina kokuwa da Numfashina.
Mirmishin saman baki ya yi sannan ya taka ya shiga dakin ya na fadin"Tsanar da kika min siya har ta kai ki juya baya daga kallon Fuskata?
Sai kuma ya bi akwatin gefena da kallo.
Kafin ya yi mgana na koma falo Fuu, sai ya bi ni da kallo kafin ya Rufe kofar ya Tura akwatin ya taddani a falo a zaune a kasa na saka kaina a gwiwa.
Da Sauri ya ijiye akwatina tsakar falo ya karisa gareni jikinsa na rawa ya ke fadin"Siya na san ni me laifi ne ammh don girman Allah ki tsaya ki Saurareni."
A fusace na Dago ina kallonsa kafin nace"Na saurareka? Ashe akwai sauran abunda zaka gayamin wanda ban ji ba, ko kuma nace ban gani da idanuwana ba?
Umh! Abubakar kenan"
Na fad'a hawaye na kawo idanuwana, da Sauri ya saka Hannu zai rikeni na Zabura naja baya ina fadin"Kada ka kuskura ka tab'ani Tunda BAKA SO NA ASSADIQ."
Ido ya zaro kafin yace"waye ya fad'a miki ba na son ki SIYA?
Cikin Idanuwansa nace"Kai ne."
Cikin karin mamaki yace"Ni kuma? Look Siya boye miki Asalina ya na da Nasaba da Sonki da na ke yi, ina sonki ba na son na Rabu da ke shiyasa ban taba fad'a miki komai game dani ba."
Kallonsa na ke yi ina tsiyayan hawaye kafin na kira sunansa"Assadiq."
Sai kawai yace da Sauri"Ki tsaya ki Fahimceni Siya, mu zauna mu yi mgana don Allah, ammh kafin nan wannan akaatin nan na miye ne? Ina kike shirin tafiya?
Kai Tsaye nace"Wajen mahaifiyata."
Sai ya koma ya zauna Dabas kafin yace"Why Siya? Sai ki iya tafiya yanzu ki bar ni?
Mirmishin takaici na yi kafin na jawo karamar jakata, na bude na Dauko masa takardan shaidar cikina na mika masa.
Sai ya ki karba'a ya na kallona Sai ya kira sunana "HASIYA.."
Da Sauri nace"Sakon ka ne aciki ka Duba."
Ba musu ya karb'a ya Bude ya Fara Dubawa, ina kure masa ido naga ya Dago a razane ya na kallona.
Cikin mirmishi nace"Ka yi mamakin ko? Ka yi mamakin ya aka yi na samu ciki Ahalin ka kaini an datsemin Hanyar samin cikin ko Assadiq?
Ina ganin Razana da Firgici a idanuwan Assadiq.
Ya na kallona ina Hango kunya nadama da Tsananin tsoro da wani abu a akwayar idanuwansa.
Cikin Sauri na mike ina fad'in"Zaka iya sakina Assadiq ammh sai dai ka sani ko Sama da kasa zata had'e bazan amince na zubar da wannan cikin ba."
Na fad'a ina kokarin Danne kukana ammh sai da ya kwacemin.
Cikim kuka na cigaba da fadin"Na yarda baka sona, ammh ni ina sonka Assadiq don Allah ka barni da cikin nan na yi maka alkwarin zan yi nesa da Duniyarka har abada ba wanda zai san ka na da wani gudun jini bayan Ya'yan da Sultana zata haifa maka."
Ban karishe mganata ba naji ni gabadaya acikin jikinsa.
Ya yi min wani karkarfan Riko cikin wani irin Sauti yace"Tare zamu rene gudan jinin mu siya, zai kuma zo Duniya ya iske gatan Iyayensa Biyu tare da gatan duka Ahalim mu Siya."
Cikin mamaki na Dago fuskata da tayi jage jage da majina ina kallonsa
Cikin mamaki na kira sunanshi.
"Assadiq"
Kai ya gyad'amin kafin yace" Ina sonki HASIYA, ki yarda ko karki Yarda, ina sonki sannan kuma na yarda da kuskurena na kuma karbi laifina zan kuma gyara, ta hanyar gayama Ahalina da Duniya cewa ke MATATA CE.! Kuma cikin da ke jikin na wa ne"
Ya fad'a ya na shafa kasan marata, sai naji kamar zan suma saboda dad'i
Cikin kuka nace"Ko da kuwa hakan zai jefa rayuwarka cikin Tsaka mai wuya?
Da sauri yace"Eh na amince da hakan matukar zan cigaba da kasancewa tare da ke na shirya karban komai Siya."
Bansan lokacin da na kara Rumgumesa ba ina dariya ina kuka nace"Nagode Assadiq. nagode."
Kwata kwata naji jin haushinsa ya fita daga raina daman Fargaba na d'aya shine yace zai sakeni ko zai rabani da Cikin jikina.
Sannan maganar Boyemin Asalinsa da ya yi bai dameni ba, ta wanni Fanni ya yi hakane domin amfanin kaina da na shi gabadaya.
Ni ban damu da ya so ni ba, ni dai ina son shi kuma ina fatan na zauna da shi har karshen rayuwata.
*Janafty*
*TMWBK302*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/I7uxPXgtPKBHnVQjaEbRlE
Mun dad'e tsaye Rumgume da juna kafin ya sake ni, sannan ya bi fuskata tare da bakina da sumbata mai yawa.
Sannan ya ja hannuna muka zauna saman daya daga cikin kujerun falon.
Ya Rumgumoni ta rabin jikinsa na Dama, lokaci daya hannunsa na shafa kasan marata cikin sannu a Hankali kamar ya na shafa kwai.
Ni kuma na lafe a jikinsa ina sauke Numfashi ji na ke yi kamar dukkan wasu matsalolina na nan duniya sun kauce, kamar ni kad'ai ce Sarauniya da ta yi saura a duniya.
Idanuwana suna lumshe naji Assadiq ya fara mgana cikin Taushin murya da fari da kiran sunana ya fara
"HASIYA."
Na amsa cikin Dakushewar murya da alamun sanyi a cikinta, miyau kuma ya fara taruwa a bakina na kira sunansa nima bayan na amsa kiransa.
"Na'am Assadiq din Hasiya"
Mirmishi ya yi domin har sai da kunnuwana suka jiyomin Sautin mirmishin nasa da ya shiga har cikin zuciyata.
Cikin kwantar da kansa saman kaina ya fara fad'in"Zan fada miki ko ni waye, sannan zan amsa duka tambayoyinki game dani, nasan zaki ce me ya rage baki sani ba? To har yanzu akwai muhimman abubuwan da ya kamata ki sani game da Rayuwata Siya, ammh kafin nan sai kin fad'amin meyasa a wanchan Ranar a gusau kika taho zariya cikin Daran nan Siya? Sannan me yasa kika ki Daukan Wayata? Daga karshe sai naji ta a kashe, Siya kinsan iya adadin Tashin hankalin da na shiga bayan tafuyarki kuwa? Kinsan adadin irin Bugun zuciyar da na rika fama da shi in na Tuna a yanayin da kika taho zariya da daddare sannan ga hanyarmu sai a hankali?
Me yasa kika yi haka?
Ajiyar rai na sauke, kafin na Dago kaina miyau ya cika bakina shiyasa na tashi da sauri sai ya rikoni ya na fad'in"Ina kuma zaki muna mgana?
Bakina na nuna masa da ya cika da Miyau sai ya yi saurin sakina ya na fad'in"Sorry."
Kai na gyad'a masa, sannan na wuce zuwa cikin daki na shiga makewayi na zubar da miyan bakina sannan na wanke bakin, ban fito ba sai da na samu wata bakar leda na taho da ita, gudun kada maganar ta Gundiremu da yawan tashi na.
Sanda na dawo gefensa na sake zama kamar dazu sai ya kara rumgumoni,Ya dora kansa saman kaina da ke gefen wuyansa, ni kuma sai na nuna masa ledan hannuna ina Fad'in"Ka yi hakuri, na zama kazama yanzu ban iya hadiyan miyau."
Mirmishi ya yi kafin yace"Mun zama kazamai zaki ce, ni ma in naji miyan sai na Tofa abuna aciki ko?
Ya fad'a ya na leken fuskata sai na kyalkyace da dariya shima ya na tayani.
Sai da muka natsu sannan ya kalleni ya na fad'in"Umh baki bani amsar tambayoyina ba?
Shuru na yi kafin nace"Tsoro na ke ji, ba na so na zauna wata acikin yan'uwanka su Fahimci alakarmu da kai wani abu mara dadi yazo ya faru shiyasa na tafi."
Na kasa fad'a masa karona da abokinsa saboda bansan ya zai Dauki mganar ba.
Kai Tsaye yace"Me yasa kika tafi? Ba wajen Saliha kika zo ba? Ba wanda zai fahimci wani abu tunda ki na da alaqa da Mijin da Salima ta aura."
Cikin mamaki na kallesa shima ni ya ke kallo kafin ya yi mirmishi yace"Kin yi mamakin ya a ka yi duk na san wannan ko? Sai bayan tafiyarki a ranar nasan haka nima."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.