Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 80 of 86
Mun gama waya da Amma kenan sai ga kiran Umma itama muka gaisa ta gaisheni tunda ko jiya ta kirani ta gaisheni da jiki.
Ni da kaina na ke gayamata diyar yayata zata zo ta taimakamin
Umma tace"Eh gwara haka ko ya ya mutum ya ke ai Rahama ne. tunda ga su Asim a wajena."
Cikin karfin hali nace"Umma su sha zamansu wlh, in suka dawo bazan iya da su ba."
Umma na dariya tace"Jiya ai sun yini Hiran Mami, Jiya Asif da rigima ya tshi ashe zazzabi ke jikinsa sai da na bashi mgani"
Sai na ke gayama Umma su Asim ba su cika yawan ciwo ba sai dai ko zawon Hakora da suka yi ta fama da shi Shima din bai ba su wahala sosai ba.
Kaf yayayen Assadiq ba wacce bata kirani ta yi min sannu ba, Hatta Sadiya itama ta kirani ta min sannu Sajida kuma daman tunda muka daidaita lokaci bayan Lokaci muna mgana.
Allah sarki har ce min ta yi in ina so sai ta yi ma Umma mgana ta zo ta taikamin, ni kuma kunya da nauyi suka saka nace ta yi zamanta bakomai.
Bazan iya kwanciya yayar mijina na Hidima dani ba abun akwai wani iri aciki.
Da na gayama Assadiq ma a lokacin Dariya kawai ya yi kafin yace"Ikon Allah Su Sajida an zama gama garin zawarawa."
A lokacin da ya fad'i haka sai da nace"To wai bazaku iya gyara Lamarin ba Assadiq?
Assadiq yace"Abba ya zauna da shi, laifin fa duk na Sajida ne ko za'a gyara sai in shi mijin ne ya dawo yace zai maidata kuma abu ne da ya had'a da Uwa dole kuma ya yi ma mahaifiyarsa Biyayya, ni tausayinta na ke ji ya'yanta Uban duk ya rabata da su Yar kibar nan ta Sajida duk ta ta fi, bakin nan nata da baya shuru da Had'e had'e rayuwa ta gama nuna mata gaskiyan da ake gayamata bata Dauka ba, duk ta zama wata a firgice."
Ya na wannan mganar ina Hasaso abunda ya faru dani Lokacin da Abubakar ya sakeni.
Kusan zauncewa na kusa yi, na fita Hayyacina kai Allah ka raba kowata mace da kaddaran sakin aure da zawarci.
Kamar yadda muka Tsara Tahir ya Biya ta Zariya ranar Wata alhamis ya Taho min da Amna.
Da ya ke wani Taron siyasa ya karfafa ma Tahir shigowa Abuja kuma daman Hauwa'u ta matsa zata Biyosa ta zo wurina yasa ya zo da ita.
Sanda suka iso Assadiq na wajen aiki shima yana sauke su ya wuce inda zaa shi.
Dakin da Sultana ta sauka na sauke Amna da Hauwa'u.
Hakuri na ba ma Hauwa'u na Roketa ta shiga kitchen ta da fa musu wani abu su ci ni dai ba na iya moran kaina Ballatana na Morama wani.
Hauwa'u tace"Haba bakomai bari na shiga na girka"
Da ta tambayeni me zata girka nace abunda zai fi sauki tunda tafiya suka sha. Ni kuma na shige daki na kulle kaina saboda kamshin girki in na shaka ba zaman lafiya.
Ina da sauran miya tun wanda Safiya ta yi ne kafin ta tafi, Sai ta dafa musu Taliya fara suka ci da miya.
Ni kuma na Tura gaya hakanan na sha Ruwa.
Amna kuma ta shiga kitchen ta na wanke wanke, Adda Rukayya ba ta wasa sosai ta ke koyama ya'yanta ayuukan gida saboda Rayuwa.
Muna falo ni da Hauwa'u muna ta Hira, ta na gayamin taji dadin kayan gyaran da ta siya hannun Surayya Dee.
Ni na had'a su tunda na gayamata ingancin kayan tace taji dad'in mganin sanyin nan tare da tsumin nan, ita yanzu kazar Amare ta ke so ta kara siya taci.
Ina daga zaune nace"Ki siya wlh kazarta na da kyau, kuma ta na jimawa a jikin mace ta na aiki, nima fa na so na kara siya sai kuma ga Laulayi da gudu na watsar da su na yi ta kaina."
Hauwa'u na min dariya tace"Result din gyara ne kika gani fa Madam"
Ina jin miyau ya Taru a bakina nace"Uhm ai naga gyara sosai."
Ni na gayamata Surayya ta fara Dahuwar Tatattabaru sosai kuma suke da inganci nan take Hauwa'u tace zata yi mata mgana ta na so.
+234 803 277 3332.
Ina raina Amna sai ga ta, ta zage ta share min gida tas ta goge ta saka Turare.
Ko da ya ke yanzu shekaranta sha uku, ta riga Adda Fati haihuwa ita Adda Fati ta jima ba ta Haihu ba ne sai Adda Rukayya ta dauke girman.
Hauwa'u kuma ta yi musu abincin Dare har da mazajen namu.
Ni nace ta yi girki saboda su kada su dawo ba abinci.
To ba su shigo da wuri ba ma, cikin su ban san wanda ya tsaya wajen d'aya ba.
A tare dai suka shigo gidan suna Hiransu suna Dariya, Hauwa'u ce ta shirya musu abincin ta kawo musu Amna ana sallar isha'i ta yi barci.
Ni kuma saboda kamshin abinci ina daki amma ina jiyo maganganun su tunda ba sa mgana a hankali kamar mu.
Ina ji Tahir na yi ma Assadiq tsiya da cewa yace kawai kuku ya kawo musu daga zuwan matarsa ta zama mai yi masa girki shi da matarsa.
Shi kuma yace masa ai shima an taimakesa yadda ya ke jin yunwar nan in bai samu abincin nan ba ai akwai matsala sannan ga Musulunci akwai taimakon dan'uwa musulmi wannan shima ya yi jihadi ne.
Ina jinsu suna ta cacar juna kamar yadda suka saba
Tahir na ce ma Assadiq ya shiga uku da Jaraba, yana da kananun shekaru kafin ya yi Hamsin ya kai ga ya'ya ashirin
Kilama yanzu haka Sultana ciki gareta.
Amsar da Assadiq ya ba ma Tahir ce ta bani dariya.
Wai ai ni ka shaida lafiyata kai ne dai na ke tunanin ko dai ko dai da matsala ne!?
Sai ga Hauwa'u da gudu ta shigo daki tana fad'in"Abokan nan ba sa jin kunyar fad'in mgana mai nauyi."
Ina kwance nace"In dai Assadiq ne ba'a kada shi a mgana, shi kuma mijin ki tsokana da neman zence."
Dole ai ta bar musu falon ta dawo wajena muna ta Hira.
Tana fad'in tsoro ta ke ji ta samu ciki Tunda ta na karatu.
Ni kuma nace mata abun na Allah ne ta yi fatan Allah ya zaba mata mafi alheri.
Sai wajen sha d'aya na dare Assadiq ya leko yace Hauwa'u ta shirya Tahir yace ba zai iya kwana shi kad'ai ba.
Ina daga kwance sai da na mike cikin mamaki kafin nace"To ba ga dakuna ba, sai ku kwana tare."
Assadiq yace"Haka nace masa, ammh sai naga yana nokewa."
Ni ko kamar da sauri nace"To don Allah Assadiq ka roke sa mana."
Asaadiq yace"Ke kam da son jan zence ki ke yi, kika sani ko yana Ihun dare ba ya so mu ji? Hauwa'u dauko mayafiki dare ya yi."
Hauwa'u kunya ya hanata Dago kai sai ta mike tana fad'in" Kayana na can dakin."
Assadiq ya bata hanya ta fita sai ya kariso gareni ya zauna kusa da ni.
Lokaci d'aya yaga na hade rai sai ya yi dariya kafin yace"Da safe za su dawo kada ki damu kin ji ko my siya?
Ina zumbura baki nace"To me yasa bazasu kwana anan ba?
Hancina ya ja kafin yace"To na gayamiki kada ki matsa, kinsan akwai mazan da ba sa iya sarrafa jin dad'insu kila yana cikin su ne, kinga kuwa da kunya aji ihunsa a gidan abokinsa kuma yadda Tahir ya ke sabon shiga a lamarin kinsan ba'a daga kafa kullun ne Til Down."
Hannu na saka na dokesa a cinyarsa sai ya sosa wajen yana dariya kafin yace"Me kuma na yi?
Ina hararansa nace"Bansani ba, Assadiq ihu fa? Wani irin Ihu kuma?
Assadiq na dariya ya sunkuyo ya na min Rad'a da yasa na fara Turesa ina fad'in"Assadiq..Assadiq.."
Hannayena ya rike duka Biyu ya sama min karfi yana fad'in"Irin wannan irin wannan da ki ke sakani?
Ko na gwada miki irin shi ne?
Ai sai na yi lakwas ina kallonsa cikin ido kafin nace"Ka yi wa girman Allah ka yi shuru."
A kunne ya k'aramin Rad'a abunda ya aikata yasa sai da na koma na cukwikwayosa ina jin kunya Lokaci d'aya da Dariya.
Shi ma yana tayani har yana matsenin hanci yana fad'in"Ke siya kunyar taki ba ta fulani ba ne ko?
Ina Make kafarsa da kafata nace"Ta zamfarawa ne ko?
Baki ya Bude kafin yace"Bangane ba! Allah yasa ba mgana kika maida min ba."
Yadda ya Tsaya ya na kallona ne yasa na Fashe da dariya, shima kuma sai ya Tsaya ya na kallona lokaci d'aya yana girgiza kai kafin yace"Lalle Siya. to nagode."
Gabadaya mun Shagala mun manta da su Hauwa'u sai can ya tuna ya tashi da sauri ya fita Falo wayam.
Sai ga shi ya dawo ya na ce min"Tahir fa tuni ya tasa matarsa sun tafi, falo sai wayam ba kowa."
Kai Tsaye nace"bazai tafi ba, ka zaunar da shi ka na yi masa sharri."
Yana Tube rigarsa yace"Gaskiya na fad'a, bari na yi wanka."
Sai da ya fito ya tuna da bai ga Amna ba da sauri yace"Ina d'iyarki ne, ban ganta ba?
Ina kara shigewa cikin Bargo nace"Ta na dakin can, ta yi barci tun dazu."
Cikin jinjina kai yace"Amma dai taci abinci ko?
Sai na gyada masa kai lokacin Miyau ya cika bakina sai da na tashi dakyar na shiga Tiolet na zubar.
Na fito ina numfarfashi Assadiq ya kalleni yana fad'in"To ke ki samu wani Roba ki rika tara miyan aciki mana, zaki gaji da zirgan zirgan ta shi kuma"
Ina zama gefen gado nace"Ba ka jin kyamata ne?
Hararana ya yi kafin yace"Kyamar me? Ni da na yi sanadin miyan."
Ya fad'a ya na karisowa kusa dani, Dagashi sai karamin wando duk sanda zanga Assadiq a haka ba na iya had'a ido da shi.
Sai na juyar da kai zan kwanta ina Fad'in"Baka jin sanyi ne wai?
Saurin Taro kaina ya yi yana so sai na kallesa naki, runtse idanuwana na yi ina kiran sunansa cikin Shagwaba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.