Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 21 of 86
Cikin Yanayin maganarsa daga gani yana da barkwanci yace"Gaskiya kin yi sa'a Asiya, kin yi sa'ar samun Nagarttacen miji irin Sadiq."
Sannan ya kalli Surayya kafin yace"Kudos to Sadiq, zan so mu had'u na sara ma Namiji Uban maza.".
Hararansa ta yi kafin tace"Sai wani kod'asa ka ke yi ban gane ba ne?
Yana yar dariya yace"Kina jinta ko Asiya? Kwantar da hankalin ki in zan kara aure ke zaki fara sani."
Cikin gatsene tace"in ban sani ba ina ruwana Dr? Ba kaina zata zauna ba, ai ta mallam ba ta wuce Ameen"
Dariya ya sska mata ya na fad'in"Eh kaji ta. Allah yasa to da gaske ki ke."
Ya fad'a Lokaci daya ya na jan hancinta ba ita kadai ba har ni sai da na yi dariyan barkwancinsa.
Ta make hannunsa ta na masa Hararan wasa mikewa ya yi ya na Fadin"Asiya na tafi, kada ki damu You are Welcome in to Shinkafi Family da yardan Allah."
Kaina na kasa ban yi mgana ba sai dai na yi mirmishi nace"A dawo lafiya."
Nan suka barni a falo Surayya ta tafi raka mijinta.
Sai da sukaje haraban gidan bakin motarsa Sannan ya kalleta ya na fadin"Gaskiya Surry kada ki bari a wulakanta yarinyar nan, abar Tausayi ne da labarinta da kika bani, kuma ina da Tabbacin shima Sadiq Tausayinta yaji Shiyasa ya yi auran nan ba wanda ya sani."
Surayya tace"Hakane ai da kanta ta fad'a tace taimakonta ya yi saboda mahaifiyarta."
Dr yace"Nasan ta bangaren Abba game din mai sauki ne, Umma ce da Kakarku nasan sai kun yi ta ban baki da Nuniya."
Surayya tace"Kamar ka sani domin tun ajiyan Umma tace bata yarda da wannan auren ba, ko ya saki Asiya ya zauna da Sultana ko kuma ya saki Sultana ya zauna da abunda ya zab'a, innani kuma kasanta Allah da su Allah ya isa jiya ta yi ta makama Magajin gidan nata."
Dr ya jinjina kai yace"Daman ai za'a sha fama, ku dai ku tsaya mata don Allah, Umma ta Duba maraicinta tare da Rabon da ke tsakaninsu Thank god ma, sun yi aure da ta hanyar zina aka samu wannan cikin fa?
Surayya tace"Nima tunanin da na fara yi kenan a farko naji Tsoron Allah ya kamani nace to yanzu inda ba su yi aure ba fa? karfin Rabon da ke Tsskaninsu yasa ya lalace."
Cikin yar damuwa yace"To kin gani, ya kamata dai a duba lamarin cikin Fahimta sosai."
Surayya ta tabbatar masa da cewa in sha Allahu zata iya bakin kokarinta.
Sun yi sallama ya shiga mota ta mika masa jakarsa ya karb'a ya na fadin"Yanzu Zaku tafi chan gidan ne?
Sai ta girgiza kai kafin tace"Anya! Inaga sai anjuma kada mu je ta ga mutane ta kasa sakewa, kila sai Sadiq din ya iso."
Daga haka Suka yi sallama ya tada Mota ta na daga masa hannu sai da megadi ya Bude masa get ya fita Ssnnan itama ta koma cikin gida, Direba ya tafi kai yara makaranta daganan zai kai motar gareji, tana Tunanin ita zata Tukasu ita da Asiya zuwa gida anjuma.
Tana komawa falo ta ga Asiya har ta yi barci nan saman kujera.
Sai ta kara jin Tausayinta a Fili ta Furta baiwar Allah yanzu haka jiya bata samu barci ba.
Sai ta kyaleta ta koma dakinta ta Dauki wayarta sai ta ga Saddiqa ta kirata wajen sau uku bata kusa sai ta bi bayan kiran.
Taji tsoro da taji saddiqa na gayamata labarin ya bazu a kunnen har wad'anda ke nesa, yanzu haka ma Shahida daga katsina ta na hanya, Salima ma an ce ta taho, Subai'atu ke fad'amata ta kirata da Safe tace zata zo gusai itama zata zo ne? Sai ta nuna mata a'a bazata samu zuwa ba tunda sai adaran jiya ne Surayya ta kira Subai'atun ta na gayamata komai da kanta.
Surayya ta rike baki kafin tace"To duk waye ya fad'a musu?
Saddiqa dagachan bangaran tace"Kema kina da son jin magana wazai gayamusu wacce ta wuce mama"
Surayya sai ta kasa mgana, Saboda Daman Mama irin matan nan ne da komai ya faru sai ta kira ya'yanta ta fad'a musu macece dai mai son hira da ya'yanta akan komai..abunda ba Halin Umma ba kenan wani abun ma sai an jima da yinsa su ke sani a bakin yan Dakin Maman.
Saddiq ta katse mata Tunani da cewa"Saliha ce kawai kila bazata zo ba, ammh tun safe su Sakeena da Anty Sa'im suke gidan nan kuma nasan kan mganar ne."
Surayya tace"Allah ya kyauta."
Sai kuma ta kashe wayar saboda abun ne yazo mata a yadda batayi Tunani ba.
Bata dauka mama zatayi haka ba, taso ayi komai cikin sirri a gama sai daga baya kowa sai yaji, Tunda dai kowa ya sani bata da zabi illah ta daga waya ta Kira Sadiya da Sajida da sa'adatu tare da Sajida tace su zo gida yau akwai taro.
Dukkansu ba su yi mamakin kiran ba, a cire Sajida da tasan komai sauran sun ce su Sakeena ne suka kirasu suna fad'a musu abunda ke Faruwa suma kansu ya kulle daman suna Shirin zuwan gidan su ji in da kuma aka Haihu a Ragaya
Tana mgana da Sadiya a waya ta na gani Saddiqa na kiranta ba ta yanke ba.
Kuma suna gama mgana da Sadiya Subai na kiranta sai ta daga suna mgana ta na kara yi mata wasu bayanan ita kam sai fad'a ta ke yi ta na zagin Sadiq daman kuma ta na da fad'a Tun asali ita.
Da surayya ta fad'a mata abunda Mama tayi sai kawai ta yi tsaki kafin tace"Allah ya kara masa uban wa yaja? Da bai aikata ba, wazai yi yawo da mganarsa. Kuma hukuncin Umma da Saddiqa ta fad'amin ya yi daidai sai dai ya zaba don Ubansa."
Jin yadda ta Dauki zafi yasa Jikin Suryyya ya yi sanyi, ta so ayi wannan abu cikin Sirri ne bata Dauka abun zai kwabe haka ba.
Bata kara sarewa ba sai da Subai ta tabbatar mata da ta na hanya itama zata zo, sai ta ci uban Sadiq kuma sai ta kara Zuga Umma saboda yasan abunda ya yi bai kyauta ba.
Da farko Surayya bata damu ba ammh yanzu ta da fahimci gayya ne guda za su had'u masu bambamcin Ra'ayi sai taji tsoron abunda zai Biyo baya.
Ita Asiya take Tausayawama ba Sadiq ba tasan shi Namiji ne kuma duk tsiya dai shi nasu ne.
Falo ta lekoni sai ta iske har na gyara kwanciya sai barci na ke yi sai ta kyaleni ta shiga ciki ta na Tufka ta na faman warwara.
Sadiq ta yi ta kira da farko wayarsa bata shiga sai daga baya ammh kuma baya Dauka.
Sai kuma Hankalinta ya tashi ta Dauko ko wani abu ne ya same shi, sai da ya turo mata sakon ya na kan hanya ya kusa isowa gusau sannan ta samu natsuwa.
*******
11:13am
Karfe sha d'aya na safe Sadiq ya iso Gusau motar haya ya shigo daga Abuja bai zo da Motarsa ba, saboda Halin Fargaban da ya ke ciki bazai iya Samun natsuwar tuki ba.
Farko gidansa ya fara sauka Dake millions Quaters, ammh sai me Sultana bata nan, megadin gidan da Abba ya saka kuma ya ke biyansa albashi ya fad'a masa yace Tun safe suka fita da farko ya dauka Sun tafi makaranta ne.
Ya na da key din gidan a hannunsa dashi ya yi amfani ya Bude gidan ya shiga ya ijiye kayansa ya yi wanka sannan Ya taho nan gidan.
Yazo ya iske Abba baya nan ya fita Mallam Tajudeen ne ya ke fad'a masa Tun daga bakin get.
Shashen Umma ya fara isa, nan ya Iske Saddiqa da Sadiya, a yanayin kallon da suke masa yasa ya san suma susan komai sai kawai ya had'e rai, ya na cin mgani hannayensa suna sarke cikin Aljihun saukakken Farin yadin da ke jikinsa dinki riga da wando na zamani.
Umma na cikin daki, taki fitowa sai daya bita da kansa ammh kuma ya na durkusawa da niyar gaisheta yaga ta mike tsam ta bude kofar Tiolet ta shige da farko ya zata, ta shiga ta kama Ruwa ne zata fito sai da yaga yafi minti ashirin Umma bata fito ba ya zargi wani abu tunda shi dai bai ji karan Ruwa ba, kuma yaganta da wankanta tas ba wanka ta ke yi ba, in ya gane daidai shi ne bata son gani.
Cikin wani yanayi ya fito daga Falon sai kuma ya had'e da Sajida da ta iso ba Dadewa sun had'a kai da juna suna ta kuskus.
Suna ganinsa sai suka yi shuru suna kallonsu kallo daya ya yi musu ya Dauke kai zai fita, daman su Sadiya sun gaisa da shi da ya shigo, Sajida ce dai daman ba su gaisa ba.
Har ya kama hanyar Fita Sajida tace"A'a Sadiq ba mgana ne abun?
Kamar zai wuce sai ya fasa ya Juyo ya na kallonta kafin yace"Sorry ban lura da ke ba ne, Sajida ya gida da yaran?
Bai jira amsawarta ba ya fice suka rakasa da kallon mamaki.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.