Tmw Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: TMW BOOK 3.txt
Chapter 75 of 86
Tunda Assadiq ya fita ina falo nan, saboda kula da su Asif, kada na tafi daki su yi min barna.
Ammh su Dultana ba su fito ba ni dai ina ta jiransu saboda na basu abinci.
Sai da naga har La'asar ta yi na tashi na koma daki na yi salla.
Bayan na idar salla ne na kara Fitowa falo na iske su Asif na ta guje guje da Motocinsu har kuma Lokacin ban ji motsin Sultana ba.
Sai na koma kitchen daman Shinkafar na cikin kula da miyar farantai na had'a da Cokula a faranti na had'a na dauka sai dakin da na sauki Sultana.
Kofar ta na Rufe ne sai da na kwankwasa sannan Naja tazo ta Budemin ban shiga na mika mata Farantin hannuna ina fad'in"Ki zo ki daukar muku ruwa."
Tace toh ta shiga ta ijiye ta fito Falo ta Dauki Farantin Ruwa da lemun da na zuba musu tun dazu.
Kitchen na koma ina Tunanin abunda zamu ci da Daddare, Sai na yi tunanin na yi mana Tuwon shinkafa Miyar agushi da Nama.
Nan da nan na zage na fara aiki Daman Saboda wayar zamanin nan na Koyi girke girke da snkas masu dama a kafafen sada zumunta da suka kara taimakamin sosai.
Sai zuwa can Naji buruntu a falo da na leka sai naga Naja ce goye da Ummi ta duka ta na ta taya su Asif wasa da Motoci ganinta yasa sai naji dadi nasan zata kula da su.
Ina cikin yin girkin ne wayata a falo ta dauki kara ana ta kira ban ji ba.
Sai da Naja ta kawomin tace ana ta kirana, ina Dubawa sai naga Umma ce ta kirani har sau hudu.
Da sauri na wanke hannuna na bi bayan kiranta.
Bayan ta dauka mun gaisa ta tambayi su Asim kai tsaye nace"Umma su nan zuwa a karshen wata nan, yaye zan yi musu sun kusa shekara biyu."
Umma tace"Ma sha Allah, sai sun zo muna nan muna jiransu, ammh ki gayamusu kada su zo hannu Rabba na."
Ina ta dariya Umma na tayani sai can ta kira sunana na amsa cikin Sanyin murya tace"Ashe kuma yau kun yi bakuwa ko?
Kai Tsaye nace"Eh Umma suna nan tun dazu."
Umma ta yi shuru kafin tace"To ki yi hakuri Hasiya, nasan halin sultana da Rigimar tsiya da sakarci duk abunda zata yi kada ki Biye mata, ni ban ma san tafiyarta ba yar hatsaniya suka yi da Sajida yasa ta yi fushi da kowa ta taho nan Wajen ku."
Cikin mamaki nace"Subhanallah! Allah ya kyauta kada ki damu Umma lafiya lau zamu zauna har tagama kwanakinta ta dawo in sha Allahu."
Umma ta yi ta sakamin albarka kafin mu yi sallama..
Na cigaba da aikina ammh a gefen raina ina mamakin wai sultana da Anty Sajida suka yi yar hatsiniya? Lalle abun da ya baka mamaki watarana shi zai baka tsoro.
Ina da ganyen Allayahu da ganyen Ogun saboda Assadiq na san Abinci da ganye yana yawan siyomin ni kuma sai na saka masa ruwa na saka a leda na Masa masauki acikin Firiza.
Ni kad'ai na yi aikina kamar yadda na Saba Sultana ko ganinta ban sake yi ba.
Ammh naji muryanta a falo kamar ta na yi ma Naja mgana ne, sanda kuma na Fito ban ganta ba sai Najan tare da su Asif.
Ba goyon Ummin kila uwarta ta karbe'ta ne, Sai da na yi sallar mangariba na zo na kulla Tuwon a ledan Naja kuma nace su bar wasan su yi sallah sai na kunna musu Cartoon nace su kallah na kwashe kayan wasan na kai su dayan dakin da ke kusa da inda Sultana ta sauka.
Assadiq ya dawo ina wanka naji shigowarsa Bedroom dina sanda na Fito baya d'akin.
Lokacin da Tada sallar Isha'i ne ya sake shigowa shima ya Shiga wanka.
Na idar kenan sai gashi ya fito ina zaune saman darduma na yi masa sannu da zuwa ya amsa ya na kallo na kafin yace"Ya aikin? Ya baki kuma?
Kai tsaye nace"Alhamdulillah.'
Gayamin ya ke yi yaga su Asim sun samu abokiyar wasa naja, nace masa sai da na kwashe kayan wasan ai.
Shima yau a gida ya yi sallar isha'i ni kuma na fita falo na had'a mana Abinci saman Cafet Tunda Assadiq ya fi son cin Tuwo a kasa fiye da a zaman kujerun zamani.
Naja nace ta je ta kira sultana, yau ko su Asif ban samu yi ma wankan yammah ba kila sai munzo kwanciya, ni kuma na koma daki na taya Assadiq shiryawa cikin Saukakkun kaya na shan iska.
Muka fito tare na iske Hakima Sultana ta shab'a uban ado, Ta zauna saman kujera kafa d'aya kan d'aya.
Har ta zuba tuwonta ta cika Uban miya da Nama ta fara ci.
Naja da su Asim na gefe suna kallon Cartoon.
Mamakinta ya kamani sai dai ban yi mgana ba, Assadiq ne da ya zauna ya kalleta yana fad'in"Sultana shine baki jira mun zo an ci gabadaya ba."
Ba ta ko kallesa ba tace"Ni da gidan mijina ba sai na jira wata sannan zan ci abinci ba."
Ya kalleta cikin mamaki zai yi mgana na kateshi da kiran Naja da su Asim
Su daman nasan ba su cika damuwa da abinci ba Tea suke sha ko kuma su sha Goldenmorn.
Ammh na tattarosu na saka musu a filet d'aya har da Naja nace ta luramin da su kads su bata jikinsu da wajen.
Sai tace min zata rika basu ma a baki.
Abunda ya Hana Assadiq mgana kenan ya yi shuru kawai ya koma ya na kallon sultana Lokaci daya da mamakinta.
Shi na fara zubamawa sannan na zuba ma kaina, tare muka fara cin abinci shine kamar ya tuna da wani abu ya kalli Sultana ya na fadin"Ina kika baro Ummi?
Kai tsaye tace"Tana ciki ta yi barci."
Cikin sauri yace"Ita kadai kika bari a daki?
Ta tabe baki kafin tace"To me zai cinyeta?
Saboda sanin halinta na rashin kunya yasa bai yi mata mgana ba.
Muka cigaba da cin abinci, muna cikin ci ne aka kirasa a waya bansan waye ba naga ya bar cin abincin ya mike ya koma daki sai da ya jima sannan ya fito.
Sai ya iskeni sai ni kaad'ai sai yara a falo Sultana ta gama ci ta tashi ta barmin filet da komai ta koma daki.
Ina durkushe ina ta tattara kwanukan Naja na tayani Asif har ya yi barci Asim na kasa a kwance shima barcin zai yi.
Kai tsaye yace"Ina sultana?
Sai na nuna masa dakin da ido kafin nace"Ta koma ciki."
A zafafe naga ya shiga dakin ya Rufe kofa, ban matsa ma kaina sai naji abunda ke faruwa ba.
Tun kafin Assadiq ya gayamin Naja kanwar sultana ne na gane suna diban kama, sai dai ba Halinsu d'aya ba ita ba ruwanta ga hankali da taga zan yi abu zatace in kawo ta tayani.
Tare da ita muka kwashe komai zuwa Kitchen na barta ta na gyaran inda su Asim suka ba'ata ni kuma na kwashe su Asim zuwa daki zan yi musu wanka.
Har sun fara barci na shiga da su Tiolet daya bayan daya na yi musu wanka duk sun bata jikinsu da maiko da miya.
Na gama saka ma Asim wasu kayan ina kokarin sakama Asif sai ga Assadiq ya shigo ransa bace.
Bai yi min mgana ba ya shiga Tiolet sai ga shi ya fito sai kuma naga ya Bude dirowa ya dauko kayan barci ya koma Tiolet ya sauya.
Ya sake fitowa ya gyarama Asim kwanciya a tsakiya ya gyara Filo zai kwanta.
Sai da na gama saka ma Asif kaya na mika masa shi, shima ya kwantar da shi gefen dan'uwansa a tsakiya.
Kallonsa na yi naga ya juya ya Rungume ya'yansa.
Cikin mamaki nace"Assadiq ba anan zaka kwana ba fa?
Da sauri ya kalleni kafin yace"Sai a ina? Kai tsauye nace"A dakin Sultana mana, ai kana wajenta har ta koma Bisa adalci ita ke da kai, ni daman ai muna tare dakai kafin ta zo."
Shiru ya yi na wani Lokaci kafin yace"Yarinyar da ta zo da ita fa?
Kai Tsaye nace"Ta zo dakina mu kwana tare, kaga ai bazata kwana a falo ita kad'ai ba"
Sai ya jinjima min kai duk da yanayinsa ba dad'i haka ya mike ya Dauki wayarsa har ya kusa fita ya kara Dawowa ya Dauki karaman Computer dinsa ya fice bayan yace min sai da safe.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.