Best / Popular Hausa Novels

Tmw Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: TMW BOOK 3.txt

Chapter 42 of 86

Hannunsa kuma sai dai aka sakamai jakar sagala hannu aciki, kullum yana sanye da gajerun wando saboda Kafarsa, kuma Alhamdulillah kowa yazo yaga Sadiq sai yace ba shi da kyamar jiki ganin cikin Lokaci har ya fara tafiya da taimakon sandunan asibiti. Kuma su kansu likitocin sun ce sun yi mamakin saurin mikewarsa suka yi musu albishir di'n Cewa bazai jima za su sallameshi ya koma gida ya cigaba da kula da kansa.

Auwalu ke Daukan Hotonsa yana Turama yan'uwansa mata suna gani suna jin dadi, Sultana kuma koda yaushe cikin kira waya ta ke yi, in aka basa daga gaisuwa da tambayan ya jiki shikenan ya ke yi mata shuru itama sai ta rasa me zata ce ganin yadda ya yi mata gim da shi, har Umma ta gayamawa ita kuma tace ta yi masa uzuri saboda halin ciwo, ita kuma tana son shi, shiyasa har aranta taji ta tsani Hasiya umma kuma ta bata tabbacin da ita kad'ai Sadiq zai cigaba da zama a matsayin matarsa.
Hatsarin nan da Sadiq ya yi sai ya rage magana kamar ba shi ba, ya koma wani shuru shuru mgana sai in ta zama dole.
Fatansa kawai ya samu saukin da zai iya tafiya yaje ya duba Siya yaga Halin da ta ke ciki, in ya lissafa dai dai cikinta ya fita wata na tara ya shiga goma kuma yasan Edd dinta tun 19 ga watan jiya ne.
Ga shi ba waya a hannunsa da ya yi mganar wayarsa sai aka gayamasa ta lalace ta fashe a had'arin da ya yi, tare da motarsa da bazata gyaru ba saboda yadda in jin Motar ya tashi aiki Abba yace a saidata kawai tunda bazata gyaru ba.
Shi dai bashi da tacewa sai shuru, tunda ana ganin yana kwance ba shi da lafiya in ya matsa da mgana sai kuma ace shi da ba shi da lafiya.
Ammh ya shirya yin abunda rai bazai so ba, matukar ya warke yaga abunda bashi ne ba.
Jinya dai ta yi tsawo kad'an ba da yawa ba, tunda har kusan wata Biyu Sadiq yana asibiti sannan aka sallameshi lokacin yana da wajen kwana sittin da wani abu a gadon asibiti yana jinya.
Direct daga nan sai Gusau gida aka wuce da shi, a kuma bangarensa yace a kaisa tunda Abba ya basa zabin cewa ko gidansa za'a wuce da shi yace a'a a wuce dashi gida.
Kafar ne kawai ta rage hannu kuma ya warke shima sai kad'an da ba'a rasa ba kuma an cire masa wannan Jakar kafar ne ya ke tafiya da taimakon sanda har a lokacin.
Dayake tun a asibitin ana yi masa aski, da ya dawo gida wanka kawai ya yi, sai kuma aske gashi nan da suka taru a jikinsa har kuma Lokacin Auwalu na tare da shi duk Sadiq din yace ya koma gida zai iya kula da kansa ammh yaki yace yana tare dashi har sai ya warke gabadaya.

Umma tafi kowa Farinciki da dawowar Sadiq gida ya ji sauki gida haka ya ke cika da yan'uwansa duk kuma a bangarensa ake zama Har Innani ta koma yini a bangarensa.
Shi dai baya mgana Sosai sai dai ya bisu da ido kawai kuma sai ma da ya dawo gida ya kara tabbatar da zarginsa.
Siya suka dorama alhakin duk abunda ya sameshi.
Abba ne ma daya dawo hayyacinsa a kwanakin baya ya yi ma Surayya mganar Hasiya ita kuma ba kwana kwana ta sanar da shi abunda Umma ta aikata da taimakon ya'yanta.
Abba ya shiga tashin hankali yace maza maza ta sake komawa Zariya ta tabbatar ta samu Hasiya domin taga Halin da ta ke ciki.
Ita kuma a ranar data shirya zata koma Zariya uwar mijinta ta rasu ba Halin tafiya kuma sai abun ya shafe a ranta gabadaya.
Shi Uban gayyar bai manta ba sai da ya yi kwana hud'u da dawowa gida sannan Tahir ya zo dubashi, kuma akaci sa'a Tahir yazo da mota kirar Camry, Motar uban gidansa ba ya kasar shine ya ke zirga zirgan shi da ita.
Yana zuwa Sadiq yace zai kai sa wani waje a motar don Allah, shi a tunanin Tahir nan kusa ne shiyasa bai ce a'a ba, Sadiq ya shirya cikin riga da wando na wani farin yadi, sai ya nannad'e kasan wando, saboda Kafarsa ta dama kuma Tahir yaga harda Hula ya saka baki sake yace"Wai ina zaka je ne?
Kai Tsaye Sadiq yace"Kai dai muje zaka ganin ma idanuwan ka"
Ba musu Tahir ya tashi suka tafi, kuma abunda Sadiq ya shirya ba wanda yasan ya fita ya riga ya gayama Auwalu duk wanda yazo dubashi yace yana ciki ya kwanta Malam Taju megadi Sadiq ya fad'a masa ko Abba kada yasan ya fita.
Sai da suka dauki hanya ne Tahir yace ina zamu je?
Sadiq yace"Zariya."
Tahir ya saki baki kafin yace"Ka yi me a Zariyan?
Kai Tsaye Sadiq yace"In yi me kuma? Ai kasan dai ina da wata matar acan."
Tahir sai ya kasa mgana duk da Big sis bata gayamasa komai ba ammh yasan akwai matsala kuma dai maganar gaskiya shi bai ganta ba, a ransa yace to Allah yasa ba rasuwa ta yi wajen haihuwa ba sai yaji a ransa yana fata da addu'an komai lafiya saboda yasan yadda Sadiq ke girmama waannan zabiyar matar tashi.

Sai ga su a Zariya har kofar gidan da Hasiya ke zaune cikin kuma sa'a suka ga Maman suhailat a waje an kawo mata sakon kaya daga kano.
Tana ganin Sadiq ta iso wajensu bakinta har kunne ta na Fad'in"Barka da arziki Abubakar Allah sarki daman nace in dai kana raye zaka tako kafarka wajen Hasiya."
Mirmishi kawai ya yi mata sai barka da arziki ta ke yi masa ganinsa da Sanda har tana kwallah.
Tun kafin ma ya yi mganar Hasiya maman suhailt na sharan kwallah ta kwashe duk abunda ya faru ta gayamasaa.
Cikin tashin hankali yace"Yanzu ina Siya ta ke?
Maman suhailat tace"Ta na gidan yayarta din nan fati, ba ta ma jima da dawowa ba da farko ta na wajen mahaifiyar tasu ne kasan yayar mahaifiyar ta su ce ta rasu kwanakin baya."
Har tana gayamai itama daga baya ta koma sai ta samu Hasiyar ta dawo nan cikin Tausayi tace"Abunda zai baka sha'awa da yarinyar nan duk abunda ya faru bata gayama yan'uwanta komai ba, cewa ta yi kayi tafiya baka gari ita kad'ai ce ta kunshi wannan bakincikin baiwar Allah.
Ai Sadiq bai gama sauraranta ba ya fad'a mota saboda bacin rai baya ma gani sosai.
Huci kawai ya ke yi, Tahir ma ya shiga ya tada motar Sadiq na nuna masa hanyar gidan, Tahir ganin yadda Sadiq ke huci yasa ya kallesa yana fad'in"Ka bi a sannu Sadiq ka san dai baka da lafiya ko?
Sadiq kamar ya yi kuka yace"Tahir wannan wani irin tozarci ne? Ni ne basa son ganin farincikina ai shikenan dama a hatsarin da na yi mutuwa na yi da kowa sai ya duka ya Dauka."
Da Sauri Tahir yace"Subhanallah kada Bacin rai yasa ka yi Sabo mana."
Sadiq bacin ransa da Maman Suhailat tace har Surayya ta zo kuma ta gayamata ammh shine ta yi masa karya.
Ba dad'ewa sai ga su a kofar gidan Adda Fati Tahir ne ya buga sallama shi kuma Sadiq na gefe rike da sanduna zuciyarsa na faman Bugawa.
Mijin Adda Fati ne ya fito ganin Mijin Hasiya yasa ya fito da sauri sun gaisa sama sama shi da tambayan garin yaya ya samu rauni a bakinsa shima Sadiq a bakinsa da tambayar ina Hasiya?
Mijin Adda Fati ya yi ajiyar rai kafin yace"Suna asibiti da Hasiyar tun safe ta fara zubar da jini, ammh yanzu Yayarta ta kirani tace C.s Za su yi mata yanzu nan."
Sadiq ya ji kamar ya zura a guje saboda Tashin hankali cikin Sauri da rawan baki yace"Wani asibiti ne?
Yace"Kamar inda ta ke awo tace na manta  sunan asibitin."
Sadiq ya juya da sauri yana ce ma tahir yasan asibitin su tafi kawai.
Sai mijin Adda Fati yace shima daman can zai je, kawai sai suka rankaya gabadaya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.