Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 101 of 125
Sai dai rashin ganin hoton bai rage mata zafin rashin Bilal ba, bai kuma hana mata ganin shi a cikin idanuwanta ba, ko suna rufe ko suna bude. Yanzun ma hannunta ta dora saman cikinta tana shafawa a hankali. Tudun shi na tabbatar mata da yana nan, da dane yake girma a cikinta, abinda har yanzun ya kasa samun wajen zama a kwakwalwarta. Gyara kwanciyar ta tayi, tana jin hawayen da ta saba dasu yanzun suna silalowa ta gefen idanuwanta zuwa kan filon da take kwance a kai. Akwai tarin abubuwa da har yanzun basu gama zauna mata ba, taji ciwon su harta san yanda zata fara jinyar ciwukan balle kuma ta fara hango ranar warkewar su.
Tunanin Rayyan ne ya kara dirar mata, yana saka hawayenta cigaba da gudu. Rayyan da ya samu dakyar ya raba jikin shi da gado ya fito yana nufar bangaren Ayya dan ya dauko ruwa, babu wanda yayiwa magana ya wuce Kitchen ya dauki ruwan ya sake ficewa. Ayya ma da take zaune kan kujera bin shi tayi da kallo. Rukayya take ce mata ruwan saura leda biyu ajiye a kasa, na cikin fridge din kuma wasu duk sunyi kankara, batama iya amsa Rukayya ba, wayarta da take gefe ta janyo da nufin ta kira Bilal tace mishi ya kira yan gidan ruwan kai tsaye yaji idan zasu shigo yau suna so. Da yake nan makotan su ta gefe matar na siyar da ruwa, zobo da kunan Aya.
Harta dauki wayar ta cire daga key zuciyarta tayi wata irin dokawa, komai na dawo mata. Tana tunanin yanda zata fara rayuwa babu Bilal a ciki, babu yaronta. Saboda bata hango ranar da komai zai dawo mata dai-dai ba. A rayuwar ta gabaki daya ko a mugun mafarki batayi hasashen daya daga cikin yaranta zasu barta ba, duk yanda takan hango rayuwa mai karewa ce, ita take ganin zata mutu tabar su, kamar yanda nata iyayen suka mutu suka barta. Sai dai mutuwa ba zabe takeyi ba, lokaci me kawai abinda take dubawa, babu ruwanta da yanda makusantan wanda ta dauka zasu kasance cikin jimami da radadin rashi.
Da mutuwa na duba wannan da tabar mata yaron ta. Yanzun ta dandani zafin rashi na daban, ta san yanda kakeji idan ka rasa danka. Sai dai bakowa bane zai fahimci yanda kakeji idan kayiwa dan da aka fada maka ka rasa batare da kaga gawar shi ba kuka. Saboda bata jin har abada wani bangare na zuciyarta zai aminta da ta rasa Bilal, zataci gaba da kallon kofa, da tsammanin shigowar kowa a matsayin danta, saboda bata ga gawar shi ba, bata kalle shi a shimfide a gabanta ba. Shisa mutuwar shi take mata wahalar dauka.
Jiya ma Abbu sai da ya fara mata wani wa'azi da bata fahimta, tace mishi
"Ahmadi ba ganewa zanyi ba wallahi, ka kyaleni inyi kuka ko zuciyata zatayi mun sauki..."
Kyaleta din yayi kuwa. Yanzun ma hannu ta saka tana goge hawayen da suka tarar mata a gefen idanuwanta. Hakuri ya zame musu dole ta sani, amman yanzun zatayi kuka, zataji ciwo, hakurin zai biyo bayan su. Wayar da ta ajiye ce ta dauki ruri, ta dan kalleta, ganin Hajiya Dije rubuce a jiki ya sakata daukar wayar, cikin sanyin murya tayi mata sallamar da ko amsawa batayi ba
"Ya karin hakuri Maimuna?"
Numfashi Ayya ta sauke, kiran na tuna mata da sau daya Hajiya Dije din tazo mata gaisuwa. Abin na kara bata mamaki duk kusancin su.
"Alhamdulillah"
Ayya ta sake amsawa har lokacin muryarta a sanyaye
"Ina ta so in shigo dan mu samu mu zauna. Ranar naga ga mutane ga shi kuma rasuwa na tabaki"
Shiru Ayya tayi tana jin Hajiya Dije ta cigaba da fadin
"Wallahi sai kin tashi tsaye sosai. Kinga me nake fada miki ko? Haka ake so a kada miki kan yaran duk su cimma ajalin su. Kudi zaki turo inje miki wajen Sharu dana samo kwanaki"
Dan dafe kai Ayya tayi, tana mamakin hali irin na Hajiya Dije da yanda akayi bata ga kuskuren da yake tare da duka shawarwarin da take bata a baya ba. Danta ya mutu ba zata ko barta taji da abinda yake damunta ba, tana son nuna mata cewa mutuwar Bilal din ma ba daga Allah bane ba. Bata ce babu sihiri ba, amman duk abinta tasan abubuwa da yawa daga Allah ne. Da Malaman na da amfani da sun hana ma Mami aure mata miji, sun taimaka mata ta fitar da ita daga gidan. Amman da yake abin duk bigene ga Mami nan zaune daram a cikin. Ita da suna wani aiki duk bugun kasar da sukayi mata da sun hango mata kaddarar Layla da Bilal.
"Ba wannan bane a gabana Hajiya Dije. Banda duk wannan lokacin yanzun"
Ayya ta furta wani abu na tokare mata makoshi
"Bangane baki da wannan lokacin ba? Kar dai an saka miki shashatau ni Dije..."
Dan karamin tsaki Ayya taja a cikin ranta
"Wai ke babu wani abu da zai faru da ba asiri bane ba? Idan ma shine na bar mutum da Allah. Dan Allah ki kyaleni inji da abu daya"
Bata ma jira Hajiya Dije ta amsata ba ta katse kiran. Tana jan tsaki a fili, kawai sai taji ranta na baci da abinda Hajiya Dijen tayi mata. A lokaci daya hawaye masu zafi na zubo mata. Bilal da zai mata hirar shi sai ya ga tayi dariya ma baya nan. Mikewa tayi ta shige daki, ta dan fito ne ko zata sami saukin abinda take ji daman.
*
Ruwan ya ajiye a gefe, tun jiya da dare ya kare mishi. Haka ya dinga juyi a gado, ya tashi yaje ya dauko abin na mishi wani iri. Guda daya ya fasa ledar ya dauka, anan tsayen ya shanye, yana jin muryar Bilal kamar yana dakin
"Ba kyau shan ruwa a tsaye, ka samu waje ka zauna, ka juye a kofi"
Da dafe kan shi yayi, kirjin shi na daukar zafi. Karasawa yayi kan gadon ya koma ya kwanta. Gobe ne ya saka ranar da zai koma Kaduna. Saboda sati daya suka bashi, har gida Bappa yazo musu gaisuwa shi da Baba da yayi ma Rayyan din nasiha mai shiga jiki ganin yanda ya rame yayi duhu. Nasihar da bata kai mishi daren ranar ba ya nemeta ya rasa. Kusan kullum ma kuka yake yanzun, daren jiya wando zai dauka ya ga rigar Bilal, kawai yaji idanuwan shi sun cika da hawaye. Yanzun ya yarda da maganar Bilal da suna kallon wani film yana mamakin yanda hawayen jaruman mazan suke a kusa
"Kuka fa shi yake yin kan shi Hamma, karka yi mamakin ganin kana hawaye kamar karamin yaro"
Kai kawai ya girgiza, saboda yasan suna da bambanci mai nisa da turawan da suke kallo, yanayin rayuwar su, da komai daban ne. Sosai ranar ya dinga tunanin a duniya abinda zai saka hawayen shi zuba. Sai gasu yanzun, kila duk wanda suka taru ne shekara da shekaru suke fitowa gabaki dayan su yanzun. Wayar shi ya mika hannu yana dauka. Da yake ya kashe karar gabaki daya, baima bi ta kan tarin kiran da aka dinga yi mishi ba. Ya san ba zai wuce Layla ba. Bai ganta ba tun rasuwar, baya so ya ganta saboda yayi waje a kasan zuciyar shi ya dannata. Mutuwar Bilal ce a gaban shi, bayason tunanin komai.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.