Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 36 of 125
"Sanda zan bar Zaria fa lokacin zaki shiga aji uku, haka ni zan dawo gida ki barni da kewar ki"
Cewar Bilal da ta fada mishi inda ta cike
"Zaka gane yanda nake ji duk idan kazo zaka koma"
Dariya yayi sosai
"Ramawa kike sonyi shisa kika zabi Zaria kenan ko?"
Ya tambaya yana sata dariya itama. Yanzun ma hira sukeyi, Aisha ce kawai take rike shi da hira haka har baya sanin lokaci yaja. Mamakin jin kiran magriba da akeyi sukayi
"Aisha kingani ko? Nace ma Ayya kafin Magriba zan koma"
Yanayin yanda yai maganar ya sata yin dariya
"Laifina ne kenan?"
Kai ya daga mata. Dakyar sukayi sallama bayan ya mata alkawarin zai dawo gobe. Sai lokacin ya mika mata ledar da take hannun shi. Wasu takalma ne da yar ajinsu take siyarwa yayi mishi kyau, taki biyu ya sai mata kala daban-daban. Duk da batasan ko meye ba taji dadi har ranta, Bilal na da kyauta, lokutta da yawa inta juya cikin dakinta taga wani karamin abu da Bilal ya siya mata sai taji ya dan saukaka mata kewar shi. Anan masallacin unguwar su Aisha yayi sallar Magriba, sannan ya wuce gida.
*
Babu abinda Layla ta dauki gyaran da Mami take yawan yi mata kan kayan da take sakawa banda takura da rashin wayewa irin ta Mami. Ita ta kasa gane yanda duniya take tafiya da zamani yanzun sam. Lokutta da dama Mami na sakata jin daman ace ta fito a kasashen turawa ne, da yanzun ta kai shekarun da zata iya zabarwa kanta duk abinda take so, idan ma gidan zata bari tayi zaman kanta zata iya yin hakan.
Ko facebook data bude, yawancin shafukan da take bi na fina-finan kasashen waje ne, sai kuma na jaruman su. Musamman ma su Kim Kardashian, sai kuma mawaka irin su Rihanna, Drake, Chris Brown da sauran su, dan tafi son wakokin wrap. Takan ji wakokin kasashen sudan, yanayin al'adarsu na burgeta matuka. Lokutta da dama ita kadai a daki tana amfani da mp3 dinta tun kafin tayi waya ta saka earpiece tana gwada kalar raye-rayen da takan gani a fina-finai. Sosai zakayi zaton ta koyi rawa idan kaga yanda take karya gabobin jikinta.
Yanzun kuwa da tayi waya abin ba kama hannun yaro, videos ne da ita kaca-kaca, a jikinta take jin da ace tazo a kasar jamus ko amurka babu abinda zai hanata zuwa makarantar koyon rawa. Ana zuwa gasar da takan gani a fina-finai. Sosai abin yake mata kyau idan ta hasaso, musamman idan ta cire fuskar jaruman ta dora musu ta Rayyan. Wani lokaci abin na bata dariya matuka
"Hamma da rawa"
Takan fadi ita kadai, sai dai ko baiyi ba ita a kanta rawar tayi mishi kyau, musamman ace ita da shi a tare
"Perfect..."
Layla take tsintar kanta da fadi idan ta hango ta da Rayyan din, tun kafin ta gane ma'anar soyayya take kallonta a fina-finai, shisa sam bata sha wahalar gane me take ji akan Rayyan din ba, tunma kafin tasan da gaske son shi takeyi. Duk da wani lokaci yana fita daga ranta na yan dakika, wasu ranakun harna yini daya
"Mayya..."
Kalmar na bakanta mata rai sosai, kuma da gaske ne, akan shi ita din mayyar ce, kome zai mata zuciyarta har tsalle takeyi idan tagan shi, kuma bata fasa daga waya ta kira shi sai dai idan bata da kati. Ko da ace shi da Bilal basa ABU ita kam batajin zata zauna karatu a garin Kano, saboda babu yanda za'ayi abarta ta zauna hostel idan dai a BUK ko Polytechnic take. Shisa bata fadawa kowa ba sanda zata yanki jamb, zabinta na farko ABU din ta saka, tana son samun abinda ake kira "full high institution experience" a turance.
Batason sa idon Mami, rayuwar jami'a take son barjewa yanda ya kamata. Ta kuma yi sa'ar samun 181 a jamb din, ta tsallake dakyar. Tasan me take so, fannin turanci ne ta zaba saboda tana son samu aiki da wata babbar jarida ko gidan radio. BBC ne harinta, ko ba komai watakila tana da rabon zuwa kasar waje. Shisa ta gama tsara yanda komai zai fito, bata shiga tashin hankali ba sai lokacin da aka fara saida fam din jarabawar tace daliban da zasu sami gurbin karatu. Saboda gefe Mami ta koma tana fadin
"Duk makarantun da suke garin Kano? Sai kinje Zaria? Zubaida data gama karatunta kinga tabar gari. Khalifa kan shi cikin garin nan yayi nashi karatun, babu inda zakije, gara ma kiyi magana da Abbunku a sama miki gurbin karatu ko a legal ne idan BUK din ba zata samu ba"
Kuka tayi ranar kamar idanuwanta zasu tsiyaye, dan kiri kiri taga Mami na neman ruguza mata tarin burin da take da shi, a tsayin zamanta da Mami bata taba jin maraici ba sai ranar, watakila inda iyayenta suna raye zasu taimaka mata wajen ganin ta cika burinta ba suyi kokarin zame mata katanga a tsakaninta da abinda take son zama ba. Da Abbu yasa aka kirata ma kuka ta fashe mishi da shi
"Abbu dan ina mace bazan iya tafiya wani waje karatu ba? Dan ina mace bani da 'yan cin zabi? Me yasa Mami ba take son hanani? Karatu ne fa ba wani abu marar kyau ba. Ita ya kamata ta karfafa mun gwiwa in cika burina"
Ta karasa tana wani irin kuka, sosai yake kula da duka yaran. A duk gidan kuma daga Layla sai Jabir ne sukayi wata irin wayewa, rayuwar turawa ita suka saka a gabansu, garama Layla ba sosai takan nuna ba, amman Jabir sai da ya tabbatar har turancin shi ya gyara shi yanda idan yana magana zaka rantse da Allah ba'a kasar najeriya yayi karatu ba, to Layla ma yaji haka take lankwasa harshe
"Jabir turai"
Shine tsokanar da yakan yiwa dan nashi idan yaji yana magana wani lokacin, ko Layla yakan tsokaneta
"Ke da Jabir sai kun tauna harshen ku wata rana"
Kuma da gaskiyar shi, Jabir shine ya fara sakata son gyara turancin ta, haka suke zama kullum tsayin shekara uku suna wannan wahalar, Mami idan tagan su takan ce
"Ikon Allah, lallai sa kai wanda yafi bauta ciwo, da Qur'ani ne kukewa wannan nacin, ba'a kasar Kano ba, har zagayen Najeriya sai an san da zaman ku"
Dariya kawai sukanyi dan a ganin su ita ba zata taba ganewa ba. Ko Jabir din "Languages" yake karanta a BUK, kuma yanzun da yake shekara ta biyu, a tarihin department din ba'a taba samun dalibi mai kokarin shi ba. Abbu ma kance
"Da alama Jabir zaka samu gwamnati ta dauki dawainiyar karatun ka zuwa kasar waje in har kaci gaba da tafiya a haka"
Itama Layla wannan burin take da shi, amman Mami na neman hanata. Shiru Abbu yayi dan baisan me ya kamata yace ma Layla din ba. Har ran shi yana son su da karatu, a matsayinta na 'ya mace musulunci yayi mata wata daraja mai girma, suma kuma ya basu 'yancin kareta da dukkan karfin su. Ya fahimci Mami tunda sunyi zancen tun kafin yasa ta turo mishi Layla
"Kana kallon yanda nake fama da Layla kan wannan rayuwar turawan data dorawa kanta... Ina ga ta bar inda babu idanuwan kowa?"
Mami din ta fadi muryarta na karyewa, har ranta tana tsoron barin Layla Kano. Karatu duk inda kake zakayi. Shima kuma ya aminta da abinda tace din, amman yanda Layla take kuka a gabanshi ya karyar mishi da zuciya
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.