Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 14 of 125

Ko bayan Magriba da ta jiyo hayaniyar su bangaren Maimuna suka wuce, abin sai da yai mata wani iri, kamar ta aika Marwan ya kira su, shima sunata wasa da Layla tun dazun. Ganin Ahmadi ya sanyaya mata zuciya, da murmushin nan nashi ya shigo bangarenta

"Mutanen Kankia..."

Yai maganar cikin sigar tsokana, dariya tayi tana mishi sannu da zuwa, yana zama idanuwan shi akan Layla suka fara sauka

"Ina kika samo mana yarinya haka?"

Zuciyar ta taji ta doka, duk da babu alamar komai a muryar Ahmadin

"Yarinyar wajen Margayiya Mannira ce"

Dan ware idanuwa Ahmadi yayi

"Allah Sarki... Girman dan mutum ba wahala, rayuwa kenan"

Ya karasa maganar cike da tausayawa, yasan zafin rashin iyaye, duk da bai taso cikin rashin kulawa ba, musamman ace mahaifiya. Ita kuma Maryama kallon shi takeyi, ko zataji yayi magana kan idanuwan Layla din, amman wata hirar yajata da ita yana tambayarta hanya kuma yanda ta baro mutanen can din. Hira suke kamar sunyi satika basu ga juna ba, kirki irin na Ahmadi yakan bata mamaki duk tsayin shekarun nan da sukayi a tare.

Bai tashi daga bangarenta ba sai da aka kira sallar isha'i. Tasan sai washegari zata karbi girki, dan haka sallama sukayi. Sai kuma lokacin taga su Haris da suke mata sannu da zuwa

"Ba kun manta dani ba Haris?"

Dariya yayi

"A'a Mami, Ayya ce tai mana masa, shine mukace bama so da miya sai ta saka mana sikari, yayi dadi sosai ko Jabir?"

Haris ya fadi, Jabir din ba daga mishi kai, surutun su suka cigaba dayi mata tana biye su dan bata da abokan hirar da suka wuce yaran nata, Haris ne kawai bai tsareta da tambayar inda ta samo Layla ba, su Jabir kuwa sai tambaya sukeyi tace kanwar su ce

"Idon ta wani iri... Me yasa ba kalar namu ba?"

Jabir ya tambaya yana saka Maryama dogon nazari kafin tace

"Kowa da kalar nashi, kaima idan ka duba naka ba iri daya bane da na Naadir"

Cike da rashin fahimta Jabir din ya leka idanuwan Naadir

"Iri dayane Mami, ki kalla kiga"

Kai ta girgiza mishi

"Ba zaka gani ba sosai yanzun..."

Hakura yayi ba dan yagane ba

"Anan gidan zata zauna? Zamu dinga wasa tare?"

Dan jinjina kai Maryama tayi

"Nima ban sani ba"

Wannan karin su duka suka hada baki harda Haris

"Dan Allah Mami kibarta anan"

Dariya kawai tayi, ba zatai musu wannan alkawarin ba sai ta fara yin magana da Ahmadi tukunna, idan ya amince mata zataji dadi, ita kanta tana son ta rike Laylar, batasan ko tana da rabon samun 'ya mace ba. Tunda ga maza nan har hudu a gabanta.

*

"Saboda na kawo Bilal? Shisa itama taje ta dauko yarinya kenan? Ahmadi mayyar zaka bari ta zauna mana a gida? Wannan yarinyar mai idanun mage zaka hada mana a cikin yara?"

A tsayin shekarun nan ya zaice ya saba da rigimar Maimuna, ta karfi ta mayar da shi mafadaci, dan wani lokacin saiya balbaleta da fada yake samun kanta, wani lokacin kuma ficewa yake yabar mata gidan gabaki daya. Bako yaushe take bata mishi rai ba, saboda duk yanda yake jin Maryama, Maimuna daban take a zuciyar shi, ita dince karfin gwiwar shi, har yanzun ko matsala ya kwaso wajenta yake fara nufa, saboda yasan idan bata da shawarar da zata magance mishi matsalar shi zata raba nauyin matsalar tare da shi.

Labarin soyayya kala biyu zai bayar da kan shi a dage, muryar shi dauke da alfahari, shine soyayyar mahaifiyar shi, sai kuma soyayyar da Maimuna take yi mishi, shisa ya fahimci kishinta, tana mishi son da yake da yakinin yanzun a fadin duniyar shi baida na biyun sa. Amman a lokaci irin wannan yana rasa me yake lullube kwakwalwarta haka, me yasa soyayyar shi bata sakata zaben kalaman da zata furta mishi, kishin shi yasa ta daina gudun bacin ran shi sam.

"Ina manta cewa Bilal ba daga jikin mu ya fito ba wallahi, ki daina maganar nan dan Allah..."

Ahmadi ya fara cikin taushin murya, amman kai Maimuna take girgiza mishi, tun jiya da safe da ta fita tsakar gida taga Layla sai da gabanta yai wata irin mummunar faduwa, babu shiri ta koma daki tana karanta duk wata addu'a da zata zo bakinta, gashi yarinyar bata da haske can da zatayi zaton ko daga kasar turawa ta fado musu cikin gida. Babu kalar tunanin da batayi ba a ranta kan yarinyar, ko da Ahmadi ya dawo ta tambaye shi saiya fada mata ko wacece Laylar.

Bata manta lokacin da akaita surutun auren Deeni da Mannira a dangi ba, har Gwaggo bare na fadin

"Mugun abinsu ne ya fara koma musu, shisa yaje ya kwaso mayya... Watakila ta lashe mana kurwar Karime duk mu huta"

A lokacin abin dariya yayita bata, sanda labarin mutuwar Mannira ta riske su zatai karya idan bataji wani iri a ranta ba, duk surutun da ta dinga sha, ashe ma bata da rabon zama mai nisa a gidan auren, fatan samun Rahma tayi mata. Ta dauka tunda tayiwa Maryama gaisuwa a wancen lokacin ba zata sake jin ko da labarin Mannira bane ba. Sai ga yarta a cikin gidan ta, yar Mannira mai idanuwan aljanu, yarinyar da tun jiya ta kasa samun sukuni a cikin nata gidan saboda su Haris sun shigo mata da ita bangarenta.

Har ranta ta dauka ko Maryama tazo da itane ta kwana biyu ta mayar da ita, sai yanzun da Ahmadi yazo mata da wani bayani da babu abinda ta fahimta a cikin shi sai cewar Layla din zata zauna ne a cikin gidan.

"Ni dai ba zan zauna a gida daya da ita ba, sai kasan yanda zakayi da mu... Haka kawai muna zaman lafiya zata zo ta lashe mun yara"

Rai a bace Ahmadi yake kallon ta

"Wani lokaci sai ki dinga magana kamar baki da ilimi. Kina manta babu wani abu maita a addini ne, sai kambun baka... Kuma ita kadai kika fara gani da kalar idanuwa haka? Ko bakiga wanda aka haifa babu idanuwan bane gabaki daya? Kinsan karki fara mun fitinar da bata da karshe, na fada miki Layla zata zauna ne saboda girmamawa, ba wai shawararki nake nema akan hakan ba"

Wannan karon itace take kallon shi, yanda ya rufe ido yana datsa mata maganganu har yana kiranta da jahila a fakaice saboda wannan dangin mayun

"Ni kake kira da jahila? Ahmadi ni kake cewa jahila akan nace ba zan zauna gida daya da mayya ba?"

Numfashi ya sauke

"Kinga irin abin ko? Ni ban kiraki jahila ba, ki daina ce ma yarinyar mutane mayya tunda idan wani ya kira naki yaran da wannan kalmar ba zakiji dadi ba..."

Ido cikin ido take kallon shi

"Akan me za'a kira nawa yaran da mayu tunda basu hada hanya da maita ba? Ni dai na fada maka ba zan zauna gida daya da ita ba, ko ka kwashe ta da Maryaman kasan inda zaka kaisu, ko kuma ni kasan inda zaka kaini"

Murmushin takaici Ahmadi yayi yana binta da ido

"Kiyi duk abinda kike so, Layla kam zataci gaba da zama a gidan nan, in ba aure ko mutuwa ya rabata da shi ba..."

Idanuwan Maimuna cike taf da hawaye take kallon shi, tana son tabbatar da cewa da gaske yakeyi wannan yarinyar da tun jiya take firgitata zai bar mata cikin gida

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.