Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 64 of 125

"Ban wayar nan Bilal..."

Zai saka a key ya ajiye yana fadin

"Na ajiye Allah kuwa Hamma"

Sanin halin shi yake saka Rayyan din kin yarda, sako na shigowa zai sake dauka, shisa yakan mike ya dauki wayar ya ajiye a gefen shi

"Kayi abinda yafi danna wayar muhimmanci"

Yakan fada mishi, ya rasa dadin me suke ji shi da Layla kan danne-dannen wayar nan. Ji yake kamar ya tsaya a hanya ya samu wata motar da zata juya da shi Zaria saboda rashin natsuwar da yake tare da ita.

"Allah Ka san halin da nake ciki, Ka san damuwa ta, Ka san zuciyata ba zata iya daukar wani abin ba. Allah Ka sa lafiyar su"

Shine abinda yake fadi yana maimaitawa, duk inda network zai dawo mishi sai ya gwada lambar Bilal da ta Layla, amman duka tana shiga basa dauka ne. Yana sauka a tashar ya tsaya ya kira Bappa da bugu daya ya daga yana sallamar da bai jira Rayyan din ya amsa ba ya dora da

"Har ka karaso ne? Ka jirani a tashar in zo yanzun"

Rayyan din dan dakuna fuska yayi, saboda Bappa nayi kamar sun san juna, kamar sun saba ba yau bane farkon maganar su

"Eh, ok tam"

Rayyan ya iya cewa yana sauke wayar daga kunnen shi, fita yayi daga tashar zuwa bakin titi. Anan yayi tsaye, masu mashin da napep na ta mishi magana, harya kawo iya wuya, ga shi gari yayi duhu tunda sai bayan Magriba suka sauka.

"Alhaji tafiya ne?"

Wani mai mashin ya fadi a karo na biyu, kamar bai ga ya girgizawa mutane wajen hudu kai cikin alamar a'a ba.

"Sai ka daukeni ka dorani, me yasa dole sai kun sa mutane magana ne?"

Jinjina kai mai mashin din yayi

"Allah ya baka hakuri, daga tambaya"

Wani irin kallo Rayyan ya watsa mishi, dai-dai lokacin da wata mota baqa, kirar Honda Accord DC V6 ta tsaya a gaban shi. Gilashin aka sauke daga bangaren da yake, kafin aka kunna fitilar cikin motar haske na gaurayewa

"Rayyan?"

Bappa ya fadi daga cikin motar, Rayyan din na jinjina mishi kai

"Muje..."

Cewar Bappa, hannu Rayyan yasa yana bude murfin motar ya shiga, batare da yace komai ba ya rufe. Bappa ma baice mishi komai ba yaja motar, hankalin shi sam ba'a kan titi yake ba, shi dai yana garin Bauchi, zaune a cikin motar Bappa da sai kamshi takeyi. Amman hankali da natsuwar shi suna garin Zaria. Baisan anyi parking ba sai da Bappa yace mishi

"Mun zo"

Budewa yayi yana fita, in da duk Bappa ya sa kafar shi nan Rayyan yake mayarwa, ko sunan Hotel din bai duba ba, daga yanayin shi bayan sun shiga ya dan gane ko ina ne, ciki suke shiga sosai har suka karasa daki mai lamba 19, inda Bappa ya zaro mukulli daga aljihun shi yana bude dakin. Da sallama ya shiga, Rayyan na biye da shi, ya mayar da dakin ya rufe, akwai haske gauraye da dakin, babba ne da tanqamemen gado sai tv da take ta aiki, amman babu magana, anyi kasa da ita. Har da kujera doguwa a cikin dakin. Yayi kyau sosai da sosai. Ko ina a gyare tsaf, da alama zaiyi tsada

"Na san ka kwaso gajiya, ga sallah kuma da wahala kun tsaya..."

Bappa ya fadi yana saka Rayyan kallon shi, dogone dan da wahala idan bai mafi Rayyan din tsayi ba, sai dai shi siririne, da kasumba a fuskar shi, akwai abin sallah a goshin shi, wata natsuwa Rayyan yake gani a tattare da Bappa, duk da kananun kayane a jikin shi yayiwa Rayyan din kwarjini. Mutanen da suke mishi kwarjini basu da yawa, duk izzar da kake tare da ita kuwa. Da hannu Bappa ya nuna mishi bandaki

"Ga toilet din nan"

Jakar da take rataye a kafadar shi Rayyan ya sauke akan kujera, bandakin ya karasa yana zira takalman da suke ajiye a bakin kofa ya shiga sosai yana rufewa. Har ruwa ya watsa, sannan ya daura alwala. Sanda ya fito sai yake jin shi ya samu yar natsuwa. Sai kan shi da yake ciwo kamar ganga ake bugawa a ciki. Baiga Bappa ba a dakin ya dai shimfida mishi darduma, sun tsaya sukayi azahar inda akaci abinci, shi banda nutri-milk da biscuit babu abinda ya sakawa cikin shi, shima dan yana bukatar wani dan karfi ko ya yake kafin zullumi ya saka shi faduwa.

Sallolin shi yayi a nutse yana zaro wayar shi ya duba, ganin lokacin isha'i yayi ya saka shi gabatar da ita. Zaune yake akan kafet din yau ya rasa kalar addu'ar daya kamata yayi bayan rokon Allah da yasa daga Bilal har Layla lafiyar su kalau. Lambar Layla ya sake kira

"Dan Allah ki daga"

Ya fadi a hankali, amman bata daga din ba, haka Bilal. Rasa abinda yake mishi dadi yayi a duniya, saboda zuwa yanzun ya aminta da zuciyar shi, tabbas wani abu ya faru, babu yanda za'ayi yayi tafiya haka ace ko sau daya Bilal bai neme shi ba. Lakca zai tafi yayi yamma, in har bai fada mishi zaiyi yamma ba ya dinga kira kenan har sai ya mishi text cewar yana aji

"Wai ni karamin yaro ne Bilal?"

Ya taba tambayar shi wani lokaci da yayi mishi kira goma akan shidda tayi ina ya tsaya bai koma gida ba

"Ni dai ka dinga fadamun in ka san zaka biya wani waje"

Bilal din ya amsa cike da damuwa a muryar shi, amman yau ya tafi wani waje mai nisa haka ace ko sau daya Bilal bai neme shi ba, da gaske ba lafiya ba, wani abu ya faru, ko da shi ko Layla. Saboda tunanin Rayyan din sam bai kai gida ba, kallon wayar shi yake kamar yana so ta taimaka mishi da wata maslaha. Amman shiru

"Ayya..."

Zuciyar shi ta ambata, a karo na farko a tsayin rayuwar shi da yaji yana son ya kirata da kan shi, yana kuma bukatar taimakonta, watakila ita tayi magana da Bilal a tsayin ranar. Ko Bilal baiyi magana da kowa ba, tabbas zaiyi da Ayya, lambarta ya lalubo ya kira, zuciyar shi banda dokawa babu abinda takeyi mishi, tana dagawa bai jira ta gama sallamar ba yace

"Ayya kinyi magana da Bilal?"

Dan jim da tayi ya sa Rayyan din kiran

"Ayya"

Yana jin numfashin da ta sauke

"Rayyan?"

Ta kira sunan shi kamar tana shakkun cewa da gaske ya kirata, da gaske tana magana da shi

"Kunyi magana? Bilal..."

Ya sake maimaitawa

"Ina ta kira bai dauka ba, tun da safe da yace mun ya kaika ta sha, yace yana da lakca da safen da, amman ba za'ayi ba zaije gida ya kwanta yayi bacci, har yanzun bai kirani ba, na kira shi yafi sau hamsin bai daga ba. Na kasa samun natsuwa"

Runtsa idanuwan shi Rayyan yayi yanajin kamar bangwayen dakin na hadewa da shi a ciki saboda wani irin tsoro daya taso mishi

"Kai ma bai neme ka ba?"

Ayya ta tambaya da wani irin yanayi a muryarta, kai Rayyan yake girgiza mata, tashin hankali bakon abune a wajen shi, ya san kunci, ya san rashin natsuwa, yasan bacin rai, har tsoro ya sani saboda yana jin shi idan ya ga mage, yana kuma jin shi duk idan ya sauke idanuwan shi akan Layla, ya san abubuwa da dama, tashin hankali bakon shine, musamman mai hade da firgici irin wannan. Kafin wasu dakika ya fara kokawa da numfashin shi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.