Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 61 of 125

Hannun shi ya mika mata da ta kama yana karasa jan ta kusa da shi, ya saka dayan yana rankwashin ta

"Wayyo Hamma, me nayi maka?"

Ta furta tana turo labbanta hadi da murza wajen daya rankwasa din

"Kira goma saboda mayya ce ke. Ina sallah waya namun ihu a kunne"

Dariya Layla tayi

"Ina ta kewar ka shisa"

Wani rankwashin zai sake kai mata ta kauce tana dariya. Kai kawai Rayyan ya girgiza

"Ina ta so in gan ka na roki Hamma ya kawoni"

Kai ya jinjina yana saka takalma a kafafuwan shi

"Naji muje"

Ya furta yana jan hannunta. Saboda ba karamin kokari yake ba, ba iya hannunta kawai yake son rikewa ba.

"Ba kai kadai zunubin yake tararwa ba Hamma, har da ita...idan kai ka roki yafiyar Allah wanne tabbaci kake da shi tana wannan tunanin?"

Sosai kalaman Bilal din sukayi mishi tsaye, suka kuma tsorata wani abu a tare da shi. Bayason wani abu ya sami Layla saboda shi. Babu kalar fadan da baiwa kan shi ba a satikan nan. Amman yana ganinta komai ya kwance mishi sai da yaji hannunta cikin na shi sannan ya dan nutsu. To a kirjin shi yake son jinta, idan tana tsaye kuma yaci gaba da ganinta abinda zai faru kenan. Shisa ya kama hannunta, gara Bilal ya mayar da ita a hostel. A soron gidan yai tsaye yana sakin hannunta

"Tam. Bye"

Ya fadi yana shirin juyawa. Ta gefe Layla ta rike shi a jikinta, sai da ya sauke wata siririyar ajiyar zuciya, kafin ya tureta yana fadin

"Mayya..."

Murmushi tayi kawai, a hankali ya korar mata ciwon da sunan yake yi mata. Ta gama yarda akan shi din da gaske mayya ce ita. Babu wani abu da zaiyi wanda zai rabata da shi kuma. Juyawa yayi, sai da ya bace ma ganinta sannan ta fice itama, inda tabar Bilal zaune a mota nan ta same shi, ta bude ta shiga ya juya yana kaita hostel.

*

Baisan me Bilal ya fadawa Abbu ba, bayan sunan shi ya fito a Bauchi, Wailo NYSC orientation camp din da yake a karamar hukumar Ganjuwa. Ana gobe zai tafi ne yace mishi

"Ga lambar da Abbu ya turo, ka kira shi idan kaje, yasan wajen da zaka biya kudin...da duk yanda za a sauya maka waje zuwa inda kake so"

Bilal din ya karasa yana daukar wayar shi ya saka lambar a ciki. Saving yayi zuwa Bappa, kamar yanda ya fada mishi sunan. Sanin halin Rayyan ya saka Bilal kiran Bappa da tashi lambar sukayi magana. Rasa yanda zaiwa Bappa bayani ya gane yayi, a daburce yace

"Zan turo maka da lambar dan uwan nawa. Dan Allah sai kayi hakuri da halin shi, wani irin baudadden mutum ne"

Dariya Bappa yayi sosai

"Karka damu, ba matsala in shaa Allah"

Bilal yaji dadin yanda daga yanayin muryar Bappa ya gane cewa yana da kirki. Duk da zai wahala Rayyan bai kure hakurin Bappan ba

"Dan Allah kana shiga Bauchi ka kira shi. Ka ga da ka iya tuqi sai ka tafi da mota"

Harya gama duk surutun shi in da yake Rayyan bai kalla ba. Shi babu motar da zai dauka ko da ya iya tuqi. Balle bai iya ba, ba yanda Bilal baiyi ba ya koya mishi, amman yaki mayar da hankali. Ran daren da zai tafi har cikin makaranta ya shiga wajen Layla ya ganta

"Yaushe zan kara ganin ka?"

Ta tambaya da wani yanayi a muryarta da yasa ka shi fadin

"Idan kika mun kuka ba zan dawo ba"

Runtsa idanuwanta tayi tana kokarin mayar da hawayen da suke shirin zubo mata

"Zanyi kewar ka da yawa..."

Shiru Rayyan yayi suna cigaba da tafiya, ganin ya fara hango gate kuma sanin ita kadai zata koma yasa shi cewa

"Ki koma haka"

Kai ta girgiza mishi tana kasa magana

"Zan kira ki, zamuyi waya"

Ya fadi, idanuwanta ta sauke cikin na Rayyan tana saka zuciyar shi wani irin dokawa, da sauri ya cire na shi yana tsayar dasu akan fuskarta

"Ba zaka kirani ba, haka kake cewa ko da yaushe, ni na san ba zaka kira ba"

Ta karasa muryarta na karyewa

"Zan kira ki"

Ya maimaita daga zuciyar shi wannan karin. Ba kiran nata bane baya sonyi wasu lokuttan, baisan abinda zaice mata bane, har yanzun bai fassara alaqar da take tsakanin su ba, bai shirya bata suna ba, yana da tarin abubuwan da yake son ya dai-daita tukunna yayi wannan tunanin. Ba yanzun ba, zuwa nan gaba

"Ki wuce kafin in watsa miki mari Layla"

Rayyan ya fadi yana cire hannunta daga cikin n shi. Kamar ya bata damar da zata rungume shi, matse shi tayi a kirjinta kamar tana son dibar duk wani dumi na shi da zata iya ta adana tana daukowa a lokuttan da baya nan. Hannun shi daya ya zagaya ya dan dafa bayanta. Wani abu yakeji yana kwancewa a zuciyar shi da baisan menene ba, sun kusan mintina uku, kafafuwan shi da yaji kamar suna neman yin sanyi ya saka shi dagota daga jikin na shi

"Dan Allah ka kirani"

Kanta ya mangare yana sata murza wajen da hannu

"Ki wuce Layla"

Ya fadi, labbanta ta turo gaba cikin yanayin da ya tsirga mishi yana saka shi dauke idanuwan shi daga kan fuskarta kafin yayi abinda zai dade yana juyi a kai. Juyawa Layla tayi, sai da ta dan bada taku hudu a tsakanin su, wata irin bugawa zuciyar ta takeyi kamar zata fito daga kirjin ta saboda hukuncin da taji zuciyarta ta yanke mata lokaci daya, tukunna tace

"Ina son ka, karka so kowa Hamma... Ni nake son ka, na riga kowa farawa, na riga kowa fadi"

Wani irin numfashi take saukewa tana dariya ganin yanayin da yake kan fuskar Rayyan din, wayarta ta daga da sauri tana shiga Camera ta dalle mishi fuska, ya dago hannu, kafin ya kare ta dauke shi, tana kara daukar wasu sun kai kala biyar da sauri

"Layla..."

Rayyan ya fadi tana takawa cikin kokarin hade space din da yake tsakanin su

"Ina son ka Hamma Rayyan... Ina son ka da yawa"

Ta fadi cike da wani irin nishadi da baisan lokacin da murmushi ya kwace mishi ba, da gudu Layla ta juya tana dariya

"Mayya"

Ya furta a hankali zuciyar shi na tsalle kamar zata rabo da kirjin shi, ga wani dumi da gabaki daya jikin shi ya dauka da kalamanta.

"Mayya... Mayya ta"

Ya sake fadi wannan karin yana dora hannun shi akan kirjin shi. Sai da ya daina ganin Layla tukunna ya juya. Murmushi yake har kumatun shi sun fara amsawa da rashin sabawa. Bai san menene asalin farin ciki ba, amman idan aka tambaye shi ko ya taba jin shi, tabbas zai ce eh, idan bai gajiya da surutun ba zai bada labarin wannan yanayin da yake ji yanzun. Zai bada labarin ranar da yaji zuciyar shi ta kumbura taf ta cika kirjin shi, ranar da murmushin shi ya fito daga wani bangare na zuciyar shi.

Har yaje gida kalamanta na amsawa a cikin kunnuwan shi. Ko dan babu wanda ya taba cewa yana son shi, ko da wasa kuwa, ya sha jin ana fadawa Bilal, ba kuma Aisha ba, har su Rukayya idan suna waya ya saka a speaker yakan ji tace

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.