Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 125

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Ya furta a fili yana kasa kwankwasa kofar dakin jin warin sigarin da zuciyar shi taki taya kwakwalwar shi karyata cewa ba daga cikin dakin su Rayyan warin sigarin yake kara fitowa ba. Wani irin bacin raine da yake shirin danne firgicin da yake ciki ya saka shi tura dakin batare da sallama ba, haske ne gauraye da dakin saboda akwai wutar lantarki. Rayyan na zaune akan kujera ya dora hannayen shi kan teburin da yake gaban shi, Bilal na tsaye, inda ya juyo saboda turo kofar da su duka suka ji anyi

"Abbu..."

Bilal ya kira da wani irin yanayi da yafi tashin hankali a muryar shi, Ahmadi kuwa kallon su yake, dan yanzun ya kara tabbatar da cewa daga dakin su warin sigarin yake fitowa. Tunda gashi nan cike da shi

"Sigari, Rayyan sigari kake sha yanzun kuma?"

Cewar Ahmadi da wani irin bacin rai da disappointment na gaske tattare da muryar shi, yanayin da ya saka Bilal fadin

"Ba shi bane Abbu, ba Hamma bane"

Da wani yanayi Ahmadi yake kallon Bilal, Rayyan kuwa yana zaune inda yake, ko motsi baiyi ba balle wani yai tunanin zai tanka, asalima idan ka shigo dakin zaka rantse da Allah abinda yake faruwa bai shafe shi ba, wani ma zai iya cewa bai taba sanin Bilal din da Ahmadi ba ballantana yabi takan abinda suke tattunawa

"Kar kaimun karya Bilal, warin sigari tun daga wajen dakin nan anaji, karka ce mun daga kofar gida ya taso ya zabi ya tattaru cikin dakin ku"

Kai Bilal ya girgiza

"Ba ina nufin ba'a sha sigari bane, ina nufin ba Hamma ya sha ba"

Duk da alamu sun nuna Ahmadi bai gama yarda da zantukan Bilal din ba, amman akwai wani hope daya cika idanuwan shi, da gaske so yake ko yane a karyata mishi zargin shi. Abin zai mishi yawa idan ya zamana Rayyan dinne.

"Bilal..."

Ahmadi ya kira cike da kashedi, sauran karshen sigarin daya rage Bilal ya dago hannun shi yana nunawa Ahmadi da fadin

"Ba shi bane Abbu, ni ne"

Ya karasa maganar muryar shi na fitowa can kasan makoshi

"Bilal"

Wannan karin da mamaki Ahmadi yai maganar, badan baya ganin samari sa'annin su Bilal da wanda ma basu kaisu ba da shan abinda yafi sigari, sai dan haline da ko a mugun mafarki bai hango Bilal din dayi ba

"Sigari Bilal? Ina kuke so in saka raina, kamar Rayyan bai ishi sakani juyi duk dare ba, sai ka fara kaima ko? Hawan jini kuke son ganin na samu? Kun kyauta mun kenan yanzun? Um? Bilal ka kyauta mun?"

Kan shi Bilal ya sadda kasa, yanajin wani abu na taso mishi tun daga dan yatsan kafar shi har zuwa kirjin shi inda yai mishi karan tsaye a zuciyar shi.

"Allah ya kyauta"

Ahmadi ya fadi yana juyawa ya fice daga dakin, zuciyar shi zafi takeyi, duk da wani bangare na zuciyar shi da yake jin kamar bai kyauta mishi ba wajen jin dadi da ba Rayyan bane ya sha sigarin, a lokaci daya wani abu da baiyi tunani bane yaji ya karya a zuciyar shi, kamar Bilal ya karya yardar da yayi mishi ne. Saboda ko a cikin mutane yakan yi alfahari da halayen Haris da Bilal, yakan ce zai shaidi yaran nashi su biyu akan komai. Idan shima yace zai fara rashin jin nan baisan inda zai saka kan shi ba.

Da yawan mutanen da suke zagaye da shi kanyi zaton hakurin da yake da shine raunin shi, yana mamaki yanda mutane suke daukar hakuri a matsayin rauni. Sam hakuri ko da yayi yawa baya taba zama rauni, idan baka da karfin zuciya ba zaka iya hakuri akan lamurra da yawa ba, sai juriyarka ta kai wani mataki ne zaka iya kauda kai akan wasu abubuwan. Hakurin shi ne karfin zuciyar shi, yaran shi sune raunin shi, yaran shi sune cikon farin cikin shi, tunda ya same su duk inda zai juya da tunanin su manne da zuciyar shi.

Kaddara ce ta bashi Layla da Bilal, duk da jinin shi na yawo cikin nasu, amman basu da gadon shi, shisa a duk cikin yaran Bilal ne kadai ya taba siyan fili da sunan shi, takardun na ajiye ko Maimuna bata san da shi ba, yana jin yaran inda yake jin su Haris. Da gaske yake wani abu ya karye a zuciyar shi, baisan wani zazzabin tashin hankali ya rufe shi ba saida ya watsa ma jikin shi ruwa yaji tsikar jikin nashi na mimmiqewa da alamun wani sanyi da yake ratsa shi.

Ko da Maimuna ta shigo yayi duk wani kokarin shi na ganin bata karanci damuwar da yake tattare da ita ba, abincin da ta kawo haka ya dinga saka shi a baki yana taunawa yana hadiyewa, lomar da yaji ta kakare a makoshin shi sai ya bita da ruwa. Da tayi magana kan canjin yanayin shi ca yayi mata

"A gajiye nake jina Maimuna, kamar gajiya ke son saka mun zazzabi"

Da ta bashi maganin zazzabi bai musa mata ba ya karba yana hadiya tunda da gaske yanajin zazzabin. Sai dai barawon bacci ma kasa samu yayi duk da ya raya daren ne da salloli yana rokama yaran nashi karin shirya, addu'ar tashi na yawaita akan Bilal, Rayyan da kuma Layla. Saboda yanda yake jin kamar duk wata kaddara da zata same shi ta bangaren yaran da wahala ta wuce kan su ukkun, tunda su kadai ne suke caja mishi kai har haka.

*

Tunda Ahmadi ya fice daga dakin babu wanda ya motsa a cikin su har lokacin, Bilal jin shi yake kamar iskar da yake shaka bata kaiwa cikin shi, kamar iskar dakin gabaki dayanta tayi mishi kadan, hakan ne yasa shi takawa yaje inda makunnin fankar dakin take yana kure gudunta gabaki daya. Tsaye yayi a wajen yana sauke numfashi cikin son yaji ya koma mishi yanda yake da kafin maganganun Abbu. Sai dai me, yana juyawa yaji komai ya jagule mishi, ganin Rayyan ya dauko zaro kwalin sigarin shi daga cikin aljihu yana zaro lighter din shi, ya bude kwalin ya zaro kara daya ya saka a bakin shi yana riketa a tsakanin labban shi, kafin yayi ma karshen sigarin rumfa da hannun shi ya kunna wutar lighter din gudun kar iskar fankar ta hure mishi

"Hamma..."

Bilal ya kira da duk wani bacin rai da zai iya dorawa a kan muryar shi. Satika ukku da suka wuce yana kwance Rayyan din ya shigo dakin, sai da gaban shi ya fadin jin warin sigarin da yake yi

"Hamma warin sigari kakeyi, daga ina kake?"

Shine tambayar da yayi wa Rayyan din yana mikewa zaune babu shiri, da wani yanayi a fuskar Rayyan din yace

"Da gaske? Warin kaji a jikina?"

Kai Bilal ya daga mishi yana tabbatar mishi, baice komai ba ya taka inda suke ajiye turarukan su ya dauki daya yana fesa ma jikin shi, hadi da dan daga hannayen shi yana shakar iskar ko zaiji warin sigarin da Bilal yace yaji yanayi

"Yanzun fa?"

Ya bukata, yana saka Bilal din binshi da wani irin kallo

"Daga ina kake? Me yasa kake warin sigari?"

Kujera Rayyan yaja ya zauna batare da yace komai ba, hakan yakan yi duk idan Bilal yayi mishi tambayar da yasan idan ya amsa mishi ita zai sake bude mishi kofar jifan shi da wasu sababbin tambayoyin ne. Daga waje yake, kuma yana warin sigari ne saboda ya sha, idan ya amsa Bilal zai fara tambayar shi dalilin da ya saka shi shan sigari, kuma shi da kan shi baisani ba, wucewa yazo yi yaga wasu gungun samari anan kasan layin su sun taru suna ta sha, baisan meye dayan abin ba, sigarin kawai ya iya ganewa, kuma haka kawai yaji a duniya babu wani abu da yake son yi banda ya sha sigari.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.