Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 54 of 125

"Bani wayar ki kwanta dan ubanki, marar hankali kawai"

Wani irin bugawa zuciyar Layla tayi, muryarta na rawa tace

"Dan Allah Mami kiyi hakuri, wallahi caji zan saka in kwanta yanzun daman..."

Layla ta karashe tana dauko wayar daga karkashin cinyarta, hannuwanta rawa suke sanda ta fita daga WhatsApp tsabar tashin hankali. Gabaki daya wayar ta kashe ta janyo cajar ta da take makale a bango ta saka wayar ta dora kan durowar gefen gadon. Tana jin idanuwan Mami akanta

"Akan wannan raba daren na kusa haramta miki wayar nan gabaki daya. Taya ba zakiyi fama da ciwon kai ba? Kullum ba zaki samawa kanki hutu ba"

Ita dai Layla kwanciya ta gyara tana jan bargo ta lullube har wuya, zuciyarta banda bugawa babu abinda takeyi, duk fadan Mami bakomai yake karasawa kunnuwanta ba, yanda ba zata sake kuskuren barin kofa a bude ba take tunani. Har Mami ta kashe mata kwan dakin tana ficewa hadi da ja mata kofa. Wucewa dakinta Mami tayi, amman har yau abin yayi mata tsaye a rai. Tana tunanin ko Layla ta fara kule-kulen samarine da suke riketa da hirarraki har cikin dare haka. Duk da tana tunanin akwai wani abu da yake wanzuwa a tsakanin Layla da Rayyan da su kan su basu fahimta ba har yanzun. Tsoro ne fal a ranta, saboda a lokaci irin wannan ba yara mata bane matsalar, su daman masu rauni ne, mazan ya kamata iyaye su tsawatarwa.

Allah ya sani saboda Layla take kokarin bin diddigi akan su Haris, tasan shi bashi da matsala, budurwar shi guda daya. Yar gidan Yaya Ayuba ce kuma, tasan baya kule-kule. Jabir ne damuwarta, kullum cikin mishi nasiha yake, idan wasu yake yaudara zai iya dawowa kan Layla

"Dan Allah Jabir ka kula, kaga kana da kanwa, ka tayata kare martabar ta wajen mutunta yaran wasu, karka cutar da 'yar kowa..."

Dariya yakan yi sosai

"Malama Mami"

Ya kan fadi yana dariya, har sai ta zage shi ko yaga tana shirin daukar wani abin dan ta kwada mishi tukunna yake tashi ya gudu daga dakin yana mata dariya. Tasan ba zata raba Layla da samari ba, ko dan yanda take da kyawu. Dan ta hanata raba dare tana hira abinda zasu fada din idan na banza ne har da rana ma sai su fade shi. Tana hana danna wayar daren ne dan ta kwanta ta samu wadataccen bacci, saboda yanda take yawan mitar ciwon kai. Sosai Mami na ganin wautar masu yankewa yaran da zasu gani tsakiyar dare suna chatting hukunci marar kyau.

Ba lallai maganganun banza sukeyi ba, maganar banza bata bukatar lokaci, zai iya yiwuwa hira suke ta yau da kullum da abokan su, kamar yanda kake zama kayi hira sosai da naka abokan, ko idan kayi baki hira tayi muku dadi sai a raba dare ana zantawa, zai iya zamana baccine ya kauracewa idanuwansu, zamani da yai musu sabo da waya yasa suka dauka suka shiga dan duba tsofin sakkoni su rage kewa, watakila, watakila dalilai ne mabanbanta. Akwai munafunci da son kai a yanke hukuncin cewa maganar banza yaran sukeyi da tsakar dare. Saboda kai me kakeyi kenan? Me ya kaika shiga manhajar da tsakar dare? Me ya kaika bincikowa kaga ko suna online ko basa nan? Gulma?

Addu'a Mami tayi sosai da ta dan sama mata natsuwa. Da yake tun dawowar Layla bata barinta yin wani aiki, ita take su girki da gyaran gidan tunda bata da kwiya. Magriba da aka kira yasa Mami kiran sunan Allah tana mikewa dan taje ta gabatar da sallah.

*

Tsaye yake a bakin kofar dakin su ya dawo masallaci sallar isha'i. Wayar shi yake dubawa yana ganin sakonnin Mtn da suke ta cire mishi kudi na rashin dalili, harda su wani caller tune da baisan sanda yai subscribing ba. Karamin tsaki yaja, sakonnin ma duk sun taru sun cika mishi waya, ba dubawa ya cikayi ba. Ya goge duk na Mtn din. Ya shiga na bankin shi ma yana gogewa. Na Layla ya shiga, akwai wanda ma bai bude ba ashe, shifa waya sam bata dame shi ba. Balle kuma tunda suka dawo gida, in banda Layla babu wanda ya kira da wayar, sai fa Bilal da idan ya fita yana son gaya mishi wani abin ya kira shi.

Ya kara yawan kwayoyin da yake sha saboda ya daina samun bacci kwata-kwata, na ranar ma wahala yake mishi. Haushin komai da kowa yake ji, baison yin magana, ba kuma yaso ayi mishi. Surutun na kara mishi hayaniya cikin kan shi sosai da sosai. Yafi bukatar shiru akan komai yanzun. Sam baiji takun tafiyarta ba, sai hannuwanta da ta sakala cikin na shi tana fadin

"Hamma..."

Ba dan bata gan shi ba duk yinin ranar, ta gan shi bai dai kulata ba, inda take ma bai kalla ba, tunda suka dawo ya kara zama shiru-shiru

"Kaqi fadamun abinda yake damun ka ko?"

Ta furta da wani irin sanyin murya, saboda ta tabbatar akwai abinda yake damun shi, Rayyan na jinta a wajaje fiye da jikin shi, musamman da ta kara riko hannun shi tana dora kanta a damtsen hannun nashi, bai hanata ba, bai kuma daina duba sakonninta da yake dubawa ba, surutu takeyi amman tare da ita a jikin shi haka sai yake jin shirun da yake dan bukata a cikin kan shi, kamar karta raba jikin shi da nata, kamar ta zagaya duka hannuwanta ta bayan shi ta rike shi dam haka yake ji.

"Hamma..."

Layla ta kara kira tana jin kamar ta mayar da shi cikin ta saboda wani irin yanayi da taje ji. Da gaske tana son shi, tana kaunar shi da dukkan zuciyarta, a kwanakin nan tana hasaso rayuwa kala-kala a tare da shi. Wayar dai yake dannawa, yanda tayi luf a jikin shi da yanayin sunan shi da ta kira sun sa ya daina gane abinda yake karantawa. Su duka biyun suna wata duniya ne ta daban, har sai da suka ji muryar Mami da tace

"Layla?"

Cikin wani irin tashin hankali, dai-dai lokacin da Layla ta tittida kafarta tana son sumbatar gefen fuskar Rayyan din saboda yanda wata irin soyayyar shi take nuqurqusarta. Mami kuwa jikinta babu inda baya rawa, Layla din ta fito ta kira dan ta bata lambar Haris ta Etisalat din shi, wadda take ta kira taki shiga, ta tsammace ta wajen bangaren su Rayyan din daman, amman ba'a jikin shi makale ba, ba a cikin wannan mummunan yanayin da yasa numfashinta har tsaitsayawa yakeyi ba. Ga kafafuwan ta da taji suna barazanar kasa daukarta.

Tun da ta shiga aji biyu sakandire ta zaunar da ita tana kara jaddada mata yanda babu halaccin wannan rirrike rirriken a tsakaninta da duka mazan gidan. Har misali tayi mata da su Rukayya, da yanda ko su basa rike hannun Rayyan. Sosai ta tsawatar mata saboda ta ganta da ta Rayyan din yazo nemanta ta rike mishi hannu. Ta dauka tun a lokacin ta bari, tunda a gabanta Rayyan din ya fisge hannun shi har duka ya kai mata, sai Mamin taji sanyi. Idan ita Layla bata da hankali Rayyan yana da shi.

Amman ko da Layla tana tunanin Rayyan din Yayanta ne, wannan rikon da tayi mishi ya wuce na yan uwantaka, idan ba idanuwanta bane suka gane mata kamar sumba Layla take shirin mannawa Rayyan din

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.