Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 41 of 125
Bilal kuwa wajen Ayya yaje sunayin sallama, da nauyin jiki ya fito saboda tana kara fada mishi ya kula da kan shi, ya kula da Rayyan. Tana kara mishi nauyi akan wanda Abbu ya dora mishi. A hanya ya hadu da Layla da ta saka hijab, sai yaga tayi mishi kyau sosai, fuskarta fayau babu kwalliya yau.
"Hamma ina kwana"
Ta fadi da bacci cike da muryarta, bata ma jira ya amsa ba ta wuce. Zumudi ya hanata bacci daren jiya. Sai wajen karfe uku da rabi na dare, sai taga kamar tana rufe idanuwanta Mami tazo ta tasheta, ta samu tayi sallah. Nasiha tun da Abbu ya amince da tafiyarta Mami takeyi mata, yau dinma tana gama shiryawa taga Mami a ranta tace
"Ni kam naga ta kaina... Wa'azi da asubar nan"
A fili kuwa murmushi tayiwa Mami har hakoranta suka bayyana. Mamin ma murmushin tayi
"Yar nema, yau ni akeyiwa wannan murmushin da bai kai zuci ba ko?"
Dariya Layla tayi sosai, wani lokacin yanayin kular Mami har mamaki yake bata
"Dan Allah ki rufamun asiri Layla, ki kula da kanki, karki ji tsorona, karkiji tsoron me zance, kiji tsoron Allah dan Shi yana ganin ki a inda ni bana ganin ki. Ki kula da kanki, idan duk kina da matsala kinsan kirana kawai zakiyi ko?"
Kai Layla ta daga mata, yanayin muryar Mamin na sanyaya mata jiki
"Allah ya tsare mun ke a duk inda zaki shiga. Allah ya taimake ki ya baki sa'a, Allah ya banj aron rayuwa inji ki a gidan Radio din da kike buri"
Da sauri ta matsa tana fadawa jikin Mami din
"Karyani Layla"
Mami ta fadi muryarta na rawa, kwalla cike da idanuwanta, a kasan kewar Layla akwai tarin shakku da tsoro da ta kasa kawarwa daga zuciyarta. Babu yanda zatayine, Layla da Abbu sun rinjaye ta, sunki fahimtar tsoronta. Shisa ta zabi ta bi Layla da addu'a kamar yanda Abbu ya fadi
"Allah Shi ne yake tsarewa, Shi ya tsare mana su har zuwa wannan lokacin...ba tsoron mu ko dabara ba"
Numfashi ta sauke a fili tana zagaya hannuwanta ta rike Layla a jikinta sosai.
"Ina son ki Mami, da yawa fa"
Dariya kawai tayi, da Layla da Jabir basa gajiya da fada mata suna sonta, ko a gaban waye Jabir zaice yana son ta, musamman idan tayi mishi abinda yaji dadi. Kalaman na sanyaya mata zuciya ko da bata mayar musu ba, abune da bai yawaita a al'adar mu ba. Su kam sun mayar da shi kamar tun tasowar su sun sabajin ana fadin kalaman a tsakanin iyaye da yaran su. Tana son yaran, tana jin su a ranta, kawai batason dabi'ar nasaran da suka daukarwa kan su.
Musamman Jabir ma yanzun da yake ganin sai ta daga kai take hango shi, kuma kai tsaye zasuyi magana batare da sun tauna ba, suna ganin sun kai matsayin da zasu fadi duk abinda yake ransu, ga taurin kai, idan har suka kafe akan abu dai-dai ne to babu wanda ya isa yace musu ba haka bane ba. Halayen turawa shi suka daukarwa rayuwar su, kamar da suka shiga islamiyya haka suka fito batare da islamiyyar ta ratsa su ba. Addu'a ita take bin yaranta dasu har na Ayya ma, Allah ne shaida bata tashi daga wajen sallah bata hadasu duka a addu'o'inta ba.
Haka sukayi sallama da Mamin, bacci take ji idanuwanta har wani yaji-yaji yakeyi. Shisa sanda Bilal yazo daukar kayanta bata samu ta gaishe dashi ba sai yanzun. Abbu ya gaya mata ya basu mota, kuma tasan motar, tana zuwa ta bude bayan motar ta shiga. Ko kadan batayi tunanin Rayyan yana ciki ba harta ja murfin ta zauna. Numfashi ta sauke, Rayyan kuma idanuwan shi a lumshe suke, dan yasan yau zai samu yayi baccin safe tunda motar gida ce bata haya ba. Kawai yaji ana shigowa, hakan yasaka shi bude idanuwan shi, gyara kwanciya yayi yana juya kan shi ya kafa ma Layla ido.
Itama zama ta gyara tana dan juyawa taga an mata quri
"Wayyoo Allah..."
Ta furta da karfi saboda gabanta ya fadi sosai
"Hamma"
Ta furta har lokacin da tsoro a muryarta
"Baki da hankali? Da safe zaki zo kina mun ihu a kunne?"
Ita bata neman tashin hankali, tasan ko tafiya zasuyi zai zauna a gaban mota ne. Shisa ma ta bude bayan motar ta shiga abinta. Baccine a idanuwanta har sun mata nauyi
"Kayi hakuri, dan girman Allah Hamma, wallahi bansan kana nan ba sam sam, ina kwana"
Ta karashe a gajiye, hararta yayi yana jan wani tsaki dai-dai lokacin da Bilal ya shigo motar ya zauna. Juyawa yayi yana kallon su hadi da sauke numfashi
"Me kuke nufi?"
Ya bukata, tunda shi yasan su duka Abbu ya baiwa mota, baice ya zama direban su ba balle su kame a bayan mota gabaki daya
"Wani ya dawo gaba"
Ya fadi yana kallon Rayyan daya kauda kai
"Magana fa nakeyi"
Cikin ido Rayyan ya kalle shi
"Kana shamun kamshi tun da safe"
Ya fadi kamar wani dan karamin yaron da kaiwa dukan tsiya kazo kuma kana yiwa dariya. Layla Bilal ya kalla, ita kuma ta kalli Rayyan din kamar tana neman izinin shine kafin ta koma, shikuma ya rigada ya lumshe idanuwan shi. Numfashi Bilal ya sauke yana runtsa idanuwan shi ya bude su a lokaci daya. Tuqi zaiyi, yana bukatar gabaki daya natsuwar shi, idan ya biye musu zasu birkita mishi lissafi, hakan yasa shi gyara zama, addu'a yayi yana jan motar suka fice daga gidan, sun kama hanyar da zata fitar dasu daga Kano kenan Rayyan ya bude idanuwan shi yana ganin Layla a zaune a kusa da shi
"Mayya ce ke? Dole sai inda nake zaki zauna?"
Wani abu taji ya tokare mata zuciya yanayin yanda Rayyan din yayi magana. Inda ta tashi ta koma gaba ya bude ido kamar yanda yayi tana da tabbas zaice wani abu, dole saiya nemi dalilin da zai sata dana sanin tafiyar nan, bayan tun da satin ya kama take tunanin yanda zata zauna mota daya da shi, nishadin duk da takeyi ya dishe mata shi
"Hamma ka tsaya in dawo gaba"
Layla ta fadi da wani yanayi a muryarta, ta mudubin gaban motar Bilal ya kalle su
"Na dora wayata a kujerar, kuyi zaman ku"
Kafin ta karayin magana ya kunna radio din motar yana kure maganar
"Ka fasa mana kunne Bilal!"
Rayyan ya fadi a masife, ko kallon su Bilal baiyi ba, balle kuma suyi tunanin zai saurare su, ba yanda za'ayi su rabashi da nutsuwar shi yana tuqi. Matsawa Layla tayi tana kara bada tazara tsakaninta da Rayyan din, jingina kanta tayi da jikin motar tana rufe idanuwan ta, duk yanda take jin ranta na mata susa bai hana bacci dauketa ba, Rayyan kallonta yakeyi duk da yasan bacci ya kamata yayi. Yanajin inama ace haka zata zauna, yanda zuciyar shi tayi wani luf a kirjin shi abin ya mishi dadi, amman yasan tashi zatayi, bude idanuwanta zatayi ta hargitsa mishi komai kamar yanda ta saba. Baisan me yasa zata zo da idanuwan mage ba.
Idanuwan shi na kafe a kanta, tana ta baccin ta, a cikin baccin ta juyo kwanciya, ganin da yayi kamar wuyanta zaiyi ciwo yasa shi girgiza kai kawai, babu wani abu da zatayi dai-dai, baccin ma ba zatayi shi dai-dai ba. Yana wannan mitar a zuciyar shi ya mika hannu ta baya dan ya dauko ruwan da Bilal ya ajiye, sai jin kan Layla yayi saman hannun shi, kamar ya mika ne dan ta kwanto, da dayan hannun shi ya tallabe wannan, yana zare shi a hankali, ruwan ya dauka sai ya dan janyo jikin shi yana gyara zama yanda kanta zai kwanta a kafadar shi da kyau.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.