Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 123 of 125
Shikam jin ana kiran sallah yasa shi shiga dakin Ayya ya dauro alwala ya fito
"Idan zakayi sallah ka tashi kayi alwala mu tafi masallaci..."
Juya kai Bilal yayi yana kallon Rayyan din
"Zan taho yanzun..."
Sosai Rayyan ya kalle shi
"Baka da hankali ne halan? Baka da 'yancin fita kai kadai, idan na tafi sai dai kayi sallah a gida"
Murmushi Bilal yayi cikin yanayin daya manta rabon da yayi shi
"Babu inda zanje Hamma"
Kai Rayyan ya girgiza
"Na manta yanda yarda da kai take, zai dauki lokaci kafin ta dawo, ka tashi"
Bai musu ba ya samu ya mike, yanajin jikin shi a wani irin mace, alwalar yaje ya dauro shima yana fitowa
"Daada..."
Nur ta kira cike da alamun tambaya
"Masallaci zanje Nur, yanzun zan dawo kinji?"
Sai da ta daga mishi kai sannan ya kalli Bilal da idanuwan shi suke kan Nur din, kallonta yake yana rasa abinda yake ji akan ta, saboda kaunarta ko akwaita baisan inda ta labe ba, ciwon da samunta ya haifar mishi kawai yake ji, ciwon da bata da laifin shi, tabon da sukayi wa rayuwar ta yake gani a tare da yarinyar
"Ki yafe mun, ki yafe mun kafin mu tsaya dake a gaban Allah, wallahi bani da hujja"
Ya furta can kasan zuciyar shi, kafafuwan shi na daukar shi dakyar lokacin da suka fita masallaci, ga wani tsoro da yake ji har ran shi. Gidan bai sake rudewa ba sai bayan da suka dawo sallah, saboda lokacin duk yan gidan sun zo, da yake asabar ne, yawanci har masu auren idan basu zo da matan su ba suna zuwa su kadai, haka matan gidan ma, su Zubaida suna zuwa, kusan duk asabar din duniya da wahala kaga basu hadu a gidan ba, dan Rukayya sun dade akanta kafin ta dawo hayyacin ta, tana ganin Bilal din ta mike, sulalewa tayi gabaki daya, ga ciki da yake jikinta.
Gabaki daya Bilal a rude yake jin shi
"Kuyi hakuri, dan Allah kuyi hakuri"
Shine abinda yake furtawa yana sake maimaitawa yana wani irin kuka da daga baya su suka koma suna lallashin shi. Layla itama sai da Rayyan ya riketa, duk kuwa kunyar da daga ita har shi basu san suna da ita ba sai bayan auren su, dan kujera ma in suka zauna a cikin gidan ko babu kowa sai sun dan bada tazara a tsakanin su. Ranar kuwa da ya rike hannunta ta yana daura mata agogo sun zo gidan zasu tafi saboda tana rike da Nur, sai ta rike agogon a hannu, sai ga Abbu ya fito sakin agogon yayi har ya fashe, saboda kunyar da yaji, ita kanta Layla kasa hada idanuwa tayi da Abbun. Murmushi yayi kawai ya rabasu ya wuce.
Amman yau gaban kowa ya riketa har kitchen ya jata ya dibi ruwa ya bata
"Ki rufa mun asiri Layla, babyna a jikin ki, dan Allah ki natsu"
Yake fadi, amman bata san yanda zata fara natsuwa ba, sai da ya kamata yana riketa a jikin shi, tafi mintina goma kafin numfashin ta ya dai-daita, sannan ta iya raba jikinta dana Rayyan, suka samu suka baro kitchen din zuwa falo, kan kujera suka samu suka zauna. Banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, ganin Bilal din ya nutsar da wani shimfidadden kalubale da take hangowa a gaba, ko ba komai tambayoyin da Nur zatayi mata wata rana ba ita kadai zata yiwa ba, yanzun addu'a takeyi Allah ya bama Bilal aron tsayin kwanaki tare da su, saboda ganin shi ya tuna mata akwai tambayoyin da koya Rayyan zai rike hannunta ba zai isa ba.
Sam Bilal da Rayyan basu samu wani lokaci su kadai ba sai da dare, sai bayan isha'i, sannan, kallon shi Bilal yake yi, amman maganganun Abbu suke dawo mishi
"Da yana nisa da iyayen shi haka Bilal?"
A idanuwan su yake ganin yanda bai kyauta ba, yayi tunanin su kafin ya tafi, amman tunanin kan shi yafi yawa, ba zai iya fuskantar su ba shisa ya zabi ya gudu. Amman gudun nashi bai canza komai ba, bai rage musu ciwo ba kamar yanda yayi tunani, asalima ya kara musu wani ciwon ne na daban
"Hamma kace wani abu"
Bilal ya bukata, saboda shirun yayi mishi yawa
"Me zance? Bani da wasu kalamai"
Numfasawa Bilal yayi
"Kace ka yafe mun"
Dan juyawa Rayyan yayi yana kallon shi, ba yafe mishi bane baiyi ba, ko da bai yafe mishi ba, dawowar da yayi ta wanke komai, amman ba zai fada mishi yaji ba dan yanzun, ya jira kamar yanda ya saka shi jiran shi duk tsayin shekarun nan.
"Da kana son ji da baka dade har haka ba"
Kai Bilal ya jinjina, yana son ji, zai jira duk lokacin da hakan zai dauka, zai jira, zai kuma nunama Rayyan din da gaske yakeyi ya dawo. Babu inda zaije, yana kallo Rayyan ya mike, Nur da tayi bacci akan kujera ya dauka yana sabata a kafadar shi kafin ya kalli Bilal
"Karka bar gidan nan, da gaske nakeyi Bilal, ko ina zakaje ka jira sai gobe idan Allah ya kaimu, ka jirani sai gobe mu tafi tare"
Kai Bilal din ya jinjina mishi kawai, yana hada idanuwa da shi, dan baisan kome Rayyan din yake nema a cikin idanuwan shi ba
"Ka rantse mun babu inda zakaje"
Saboda a tsorace yake, ji yake kamar kar su koma su kwana a gidan yasa ido akan Bilal din karya sake tafiya
"Ba inda zanje Hamma, babu inda zanje. Ka yarda dani, babu inda zani"
Numfashi Rayyan ya sauke yana wucewa ba dan zuciyar shi ta so ba. Bangaren Mami yaje yana yiwa Layla magana ta fito su tafi gida. Da yake Bilya ya dawo mishi da motar shi, ko kudin shima bai tura mishi ba saboda bashi da wadatacciyar natsuwa, sai dai inya isa gida tukunna sai ya samu yayi mishi transfer, kafin su karasa kira biyu yayi wa Bilal duk idan ya daga amsa daya yake bashi
"Ba inda zanje Hamma, ina nan"
Har sai da Layla ta dafa shi sannan ya sauke numfashi
"Ka yarda da shi ko yayane, babu inda zaije. Wannan karin ko da zaka rasa shi, rashin zaizo maka da tabbaci, ba zaka kwanta da rashin natsuwa ba saboda in shaa Allah"
Kai kawai ya iya dagawa Layla, saboda a zantukan akwai tunatarwa, dawowar Bilal baya nufin mutuwa idan ta tashi zata tsallake shi, a yanzun din ma zai iya sake rasa shi, amman duk firgicin da kalaman ta suka sake jefa shi sun zo mishi da wata natsuwa da ba zata misaltu ba, addu'a yakeyi ko da zai sake rasa Bilal din ya samu damar da ko bashi zai suturta gawar shi ba ya halarci jana'iza, ya ga ya binne shi, yayi mishi bankwana, sai ya dawo yayi jira hakurin da yake saukarwa kowanne bawa a yayin rashi, ya kuma shiryawa tashi mutuwar, tunda babu wanda zai tsallake, babu wanda zata bari, kowa cikar lokaci yake jira.
***
Hutun da baisan yana bukata ba shi yayi, satika biyun da basu dai-dai ta mishi komai ba, amman sun nutsar da rayuwar shi, sun dawo mishi da abinda ya rasa, sun dawo mishi da yan uwan shi. Duk da har yanzun Ayya bata daina kallon shi kamar zai sake tafiya ba. Ko sun gaisa da asuba idan takwas tayi bai sake fitowa ba sai ta kira wayar shi taji ko lafiya. Da yake satin farko yaci gaba da zuwa aiki dan karamcin da mai makarantar ya nuna mishi, sai ya tsaya har sati daya ya bashi damar neman replacement kafin ya dawo, sai lokacin sukaje da Rayyan ya tattara duka yan kayan shi da suke gidan da yake haya. Daman saura wata daya kudin shekarar ya kare, mukulli kawai ya kaiwa mai gidan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.