Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 50 of 125

Can kasan makoshi ta amsa shi da

"Bakomai"

Kashe wayar yayi a kunnenta, abin ya mata zafi, ta kirane taji lafiyar shi tunda taje neman shi har ajin su bata gan shi ba. Ya hanata magana da kowa a cikin ajin, shisa bata tambaya ba, wanda suka gwada mata magana ma bata amsa su ba ta wuce abinta. Sai dai ya bata mata rai kamar ko da yaushe da yanayin yanda ya balbaleta da fada dan ta kira shi, babu kalar abinda bata fada ba kafin bacci ya dauketa, na yanda zai sani, yanda ba zata kara neman shi ba, itama tayi fushi, amman tana tashi da safe bayan tayi sallar asuba wayar shi ta fara nema taji a kashe.

"Ka huta ai, kawa kanka Hamma"

Ta furta tana jin babu dadi a ranta, har suka shiga jarabawa tana gwada kiran shi amman wayar a rufe take jinta. Ta kira Bilal yace mata yana makaranta, idan ya gama jarabawa shima zai zo ya dubata. Rayyan na karasowa abokanta da suke tsaye ya fara tsarewa da idanuwa yana musu wani irin kallo kamar zai rufe su da duka, yaran ko sallama basu tsaya yiwa Layla ba suka kama hanya suna wuce wa

"Ina wuni..."

Yarinyar da take kokarin labewa kusa da Layla ta furta cikin siririyar murya, itama idanuwan Rayyan ya kafeta dasu, tana sadda kanta kasa ta juya tabi bayan sauran

"Hamma..."

Layla ta kira tana son tambayar shi dalilin da duk zai kokarar mata abokai haka, amman yanayin fuskar shi ta hanata furta komai

"Layla"

Wani saurayi daya zo wucewa ya kira da murmushi a fuskar shi yana dorawa da

"Ya jarabawar?"

Murmushin karfin hali tayi mishi, zatai magana Rayyan ya damqi hannunta yana kallon saurayin

"Bata son magana da kai"

Ya fadi yanajin wutar da take kirjin shi tana karuwa. Murmushin shi saurayin ya fadada yana wucewa batare da yace komai ba

"Uban kowa kulawa kikeyi? Bakya jin magana ko Layla?"

Kai ta girgiza mishi tana kokarin kwace hannunta da take ji ya rike shi kamar zai tsage mata kashi, kamar hakan yaji ya saki hannun nata yana kamo kunnenta guda daya yana sakata fadin

"Wayyoo Allah na Hamma...zaka tsigemun kunne... Hamma dan Allah"

Ta karasa muryarta na karyewa, sake murda kunnen ta yayi yana mangare mata kai, dai-dai lokacin da idanuwanta suka sauka cikin nashi tun karasowar shi wajen, saboda ya dade da koyon kallon fuskar ta batare da idanuwanta sun hadu ba, kwalli ta saka da eyeliner da yasa idanuwan nata kara gudun bugun da zuciyar shi takeyi

"Bar nan, mayya kawai"

Ya fadi yana sauke idanuwan shi daga cikin nata, idanuwan Layla cike taf da hawaye ta raba shi, tana kasa yiwa Bilal da yake tsaye bayan Rayyan din magana saboda kukan da yake shirin kwace mata. Shima baice mata komai ba, kusan ya riga Rayyan karasowa department din su Layla din, ya tsaya gaisawa da wani abokin shine daya kwana biyu basu hadu ba, akan idanuwan shi komai kuma ya faru. Sai da tabar wajen sannan yace

"Ka kori wanda suke tare, ka kuma kore ta itama"

Juyawa Rayyan din yayi yana kallon Bilal

"Bana son ganin ta da wasu"

Yana dorawa da

"Kuma ba kullum nake son ta a kusa da ni ba"

Rayyan ya karasa maganar kirjin shi na zafi har lokacin, juyawa yayi yana bin bayan Layla da sauri. Bilal ya bishi da kallo yana ganin Ikon Allah, da dan gudu ya hada har ya taddo Layla da ya kama hannunta tana fisgewa, sake kamata yayi yana yin gaba ya soma janta. Zuwa wannan lokacin Bilal kuma baisan kalar tunanin daya kamata yayi ba. Abu daya yake ganewa a halin yanzun, yanda zuciyar shi take zafi kamar zata fito daga kirjin shi. Kiri-kiri yake ganin shakuwar da soyayya mai zafi ce zata haifar a tsakanin Rayyan din da Layla amman Rayyan ya karyata.

Bilal ya rasa wa Rayyan yake kokarin karyatawa, kan shi, shi din, ko kuma soyayyar da take tsakanin su da alamu suka nuna basu da iko da ita. Lumshe idanuwan shi Bilal yayi yana sauke wata irin ajiyar zuciya. Yana bukatar Aisha a irin lokacin nan, idan tayi mishi hirarta zuciyar shi zatayi sanyi ya sani. Yau kanta ciwo yake yi, dan sai da ya fara rakata kofar hostel tukunna, tace mishi zata kwanta. Idan ya kirata ba zataki dagawa ba, idan kuma yace yana son suyi magana ma ba zata ki fitowa ba. Zai zamana mai son kan shi da yawa, hakan ya saka shi tafiya kawai.

Motar da Abbu ya basu ta zamana kamar horo yanzun. Kiri-kiri abokai suka durfafeta, sai a tafi yawo a kone man ba za'a zuba wani ba, ga yanda Bilal yaga suna wujijjigata tunda basu san ciwonta ba, shisa ya kira Abbu yaji ko akwai inda zai iya zuwa ya ajiye motar, duk idan bukatar amfani da ita ya tashi sai yaje ya dauko. Akwai abokin Abbu din anan Zaria, kuma da yake Samaru ne, sai babu nisa. Can din ya kaita ya ajiye. Rayyan bai ko tambaye shi ina motar take ba, tunda ko kafin ya kai haka yakan shirya ya taka zuwa makaranta. Sam abin hawa bawai ya dame shi bane ba.

Yanke hukunci tare machine yayi zuwa gida, ya hango kamar Rayyan tsaye ta wajen gate, karasawa Bilal yayi.

"Hamma..."

Ya kira, a gajiye Rayyan ya kalle shi

"Ina ta jiran ka tun dazun"

Ya kamata ace ya daina mamakin halayen Rayya

"Ni kake jira?"

Kai Rayyan ya daga mishi da ya saka shi jan numfashi

"Da ban biyo ta nan ba fa? Na samu machine daga cikin makaranta? Sai kayi ta jira anan din? Me yasa baka kira wayata ba?"

Kafadh Rayyan ya daga mishi kawai, bayason wata doguwar magana. Wayar shi baisan caji ya kare ba sai dazun, kuma ya ajiye a gidane. Ba wasu masu kiran shi yake da ba, amfanin wayar kalilan ne a wajen shi. Juyawa yayi ya fara tafiya, Bilal na bin shi suka jera suna fita daga cikin makarantar. Hannu ya saka a aljihu ya dauko kwalin sigarin shi

"Dan girman Allah Hamma kar ka sha, idan baka kokarin ragewa ba zaka iya daina wa ba sam"

Bilal ya fadi, yana kallon yanda lokaci yasa labban Rayyan har sun fara duhu saboda hayakin da yake bukama cikin shi, yau ma tunda sassafe da sigarin ya karya. Allah ne shaidar Bilal har a sallah yanzun addu'ar barin shan yake wa Rayyan. Kara daya ya zaro yana sakawa a bakin shi kafin ya mayar da kwalin aljihun shi, ya dauko lighter ya kunna. Sai da ya zuqa ya fitar da hayakin sannan yace

"Ka barni Bilal, bana jin dadi"

Numfashi Bilal ya fitar

"Sai aka ce sigari ce jin dadin?"

Kara sauri Rayyan yayi yana cigaba da zukar sigarin cike da kwarewa

"Allah ya kyauta"

Cewar Bilal da zuciyar shi take kara yin zafi. Kafin su kai gida sai da Rayyan din ya sha kara hudu na sigarin. Shayi suka sha da cin cin din da Layla ta kawo musu. Bilal na daukar takardun shi ya fice daga dakin dan karatu zai koma cikin makaranta yayi, tsallaken kwana daya yake da shi kafin jarabawar shi da ita kadai ta rage a zangon. Rayyan kwanciya yayi yana runtsa idanuwan shi da suka fara nauyi da alamun bacci, duk da yamma tayi. Idan baccin ya kwace mishi yasan sai dai wani ikon Allah zai samu ya runtsa da dare. Kuma kwakwalwar shi na bukatar hutun. Akwai tarin abubuwan da yake bukatar saka mata na jarabawar shi ta gaba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.