Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 112 of 125

"Aikin banza, shisa rayuwar turawa tayi wallahi, babu wanda ya damu da kai ballantana"

Ita dai batace mishi komai ba saboda jikinta da yake a sanyaye. Haka mutane suka dinga shigiwa gidan, wasu da uzurin an kwana biyu ba'a gaisa ba, ko zasu wuce shine suka biyo. Murmushi Mami takanyi, tasan gulmace da tsegumi kawai ya shigo da su, idan basu ga Layla ba ta boye tana daki, lokaci zaizo da zasu shigo gidan kukan duk abinda zata haifa in dai ya taka duniya zai tabbatar da zargin su idan tantama sukeyi. Ta jima da daina gujema kaddarar da ta same su, idan tana boyewa babu abinda zai karawa Layla sai tarin damuwa fiye da wadda take ciki.

Ga duk zuwa awon da zasuyi sai likita ya kara musu kashedi kan kwantar mata da hankali saboda jininta da ya hau, abinda ba'a so a tare da mai ciki. Yan uwanta ma gulmar sukeyi, dan wasu yan unguwa sunyi bata ga laifin su ba, masu dalilin da zasuyi mata uzuri ma basuyi ba, kowa dan yatsa ya daga ma kaddarar da ta same su kamar su din sunfi karfin hakan, kamar su din suna da dabarun kaucewa abinda ya sameta. Dan akwai matar da tana shigowa gidan sun gaisa ta zauna sai ga Jabir shima ya shigo ya gaishe da matar yana wucewa kitchen.

Kallon sani Mami takeyi mata, amman ta rasa inda tasan ta

"Nasan baki gane ni ba ko? Matar Balarabe ce da muka zauna nan baya"

Kai Mami ta jinjina, shekaru wajen tara ba wasa bane ba, kuma ko da can din da suka zauna anan unguwar tasu in ba jaje ko barka ba, babu abinda yake hadasu

"Allah Sarki, shekarun ne da yawa shisa, duk ina yaran, ya wajen Salamatu"

Wata yar dariya matar tayi

"Kowa lafiya, na shigo unguwar ne nake jin rasuwar Bilal, nace aikam zan shigo in muku gaisuwa. Allah yayi mishi Rahma"

Bayan Mami ta amsa tana shirin mikewa kenan dan ta kawo mata ruwa tace

"Allah dai ya kara karemu, ashe haka abubuwa duk suka faru, ga yar wajen ki din nan da akace kina riko ya take da suna ita kuma ta dauko magana, abin ya bani mamaki kwarai..."

Kallonta Mami takeyi, kafin ta iya yin wani tunani Jabir ya fito yana fadin

"Menene abin mamaki?"

Ko ina na jikin shi bari yake da bacin rai, sosai yanzun mutane suke bashi mamaki, yana kuma sake jinjina ma Rayyan da tun da wuri ya gane halayen mutane ya nisanta kan shi da su. Shima abinda yakeyi kenan yanzun, saboda su din basa gajiya da yin abubuwan da zakayi komai dan ka gujewa zama jinsun su

"Jabir"

Mami ta kira, kai ya girgiza mata yana fadin

"Layla! Layla!!"

Yana kallon matar da take ta kifkif da idanuwa cike da tarin rashin gaskiya

"Layla!"

Jabir ya sake kira lokacin da yayi dai-dai da fitowar Layla da take rike da bayanta, idanuwanta na fara sauka akan Jabir da yake takawa ya karasa inda take yana kamo hannunta, bin shi take cikin rashin fahimta harya zo da ita tsakiyar falon yana tsayar da ita a gaban matar

"Ki daina mamaki yanzun, ki gani da idanuwan ki, saiki fita ki sake tabbatar musu idan akwai mai sauran mamaki ya bari, idan suma zasu shigone su ganta su shigo"

Kanta Mami ta sadda kasa tana kai yatsanta a hankali ta share kwallan daya taru a cikin idanuwanta, zuciyarta na wata irin kuna, mikewa matar tayi babu ko sallama ta raba Layla ta wuce. Har lokacin jikin Jabir bari yakeyi. Sakin hannun Layla yayi yana wucewa dakinta da kan shi ya dauko hijabi ya mika mata

"Hamma..."

Ta fadi muryarta na rawa, idanuwanta cike da hawaye, kai Jabir ya girgiza. Zuciyar shi sam ba zata iya dauka ba. Baice abinda Layla tayi bashi da muni ba, amman tsakaninta ne da Ubangiji, a cikin duk tarin mutanen da suke mata surutu, suke nunata da yatsa babu wanda za'a binne su a tare, sanda za'a kaita a rufo a barta da ayyukanta ba lallai su sani ba, addu'ar neman Rahma ma ba lallai bane su bita da ita. Baisan inda tarin mutanen suka shiga ba a lokacin da ta samu makaranta, lokacin da tayi saukar Al'Qur'ani mai girma, duka bai gansu sun shigo tayata murna ko jinjina ma su Mami kan kokarin su ba.

Sai yanzun da kowa yake tunanin sunyi kuskure a rikon Layla, sai yanzun da ita kanta Layla din wani abu mai muni ya sameta, tarin mutanen da basu da masaniya akan kominta sune a gaba wajen yanke mata hukuncin da basuda hurumin yin haka. Yana gab da fara sakawa mutane hannu idan yana gidan suka shigo, baisan me yasa Mami bata binsu da tabarya ba, shi bashida wannan hakurin sam

"Ba zaki kare duka rayuwarki a cikin bango hudu na dakin ki ba Layla, idan baki fita da cikin nan ba zaki fita da yaro ko yarinya. Mutane suna magana yanzun, ba zasu daina magana ba, karki barsu, karki bari su takura ki fiye da yanda kike a takure"

Jabir ya karasa maganar da wani irin yanayi a muryar shi da yasa hawayen da ke cikin idanuwan ta zuba

"Jabir ka kyaleta, me yasa baka da hankaline kai?"

Mami tayi maganar tana kokarin tarbe kukan da yake barazanar kwace mata, hijabin Layla ta karba tana sakawa a jikinta. Zuciyarta na wata irin dokawa kamar zata baro kirjinta. Mami bata hana su ba, tana kallo Jabir ya koma ya daukowa Layla takalmanta, fitar sukayi, daga farkon layin har titi, Layla tana jinta kamar babu kaya a jikinta saboda kallon da mutane suke binta da shi, kamar yanda Jabir ya fadane, ba zata cigaba da boyewa ba har abada, zancen ya rigada ya bazu, gara ta fara koyan yanda zatayi rayuwa da tabon da yake jikinta.

Sanda suka koma numfashi ma dakyar take fitar da shi, har bakin kofar dakinta Jabir ya rakata sannan ya tsaya yana fadin

"Babu hakkin mutane a kanki. Ba zan miki karya ba kin sani, duka rayuwar ki ta duniya ce ta samu tangarda, ba zancen zancen ki ba zai wuce a baku nan mutane ba, amman duk sanda zaki gifta zaki tuna musu abinda yake adane a zukatan sune, bansan al'adun mu na hausawa basawa mata adalci ba sai yanzun Layla, sai da rashin adalcin ya biyo ta cikin gidan mu...."

Wani irin numfashi Jabir yaja, bayason hawayen shi su zuba a gabanta, zai kara karya mata zuciya

"Ba zaki iya gyara tsakanin ki da mutane ba, ki gyara abinda kike da tabbas akan shi, ki gyara tsakanin ki da Allah, sai Ya tausaya miki ya gyara duniyar ki, karki bar su, karki bari su takura ki fiye da yanda kike a takure, kina jina"

Kai ta daga mishi tana goge hawayenta. Sai da yaga ta shiga daki sannan ya juya yana komawa wajen Mami ma da tun da suka fita tana zaune tana wani irin kuka mai cin rai

"Dan Allah ki rage sanyin halin nan Mami, ki daina barin mutane suna bi takan ki akan abinda baya karkashin ikon ki, idan ba zaki iya korar su ba Mami ki daina sauraren me zasu ce suna bata miki rai, dan Allah. Wallahi zuciyata zafi takeyi mun, sosai da sosai"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.