Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 56 of 125
"Amana ce ita din a wajena, rokon ka nakeyi ka rufa mun asiri, idan baka tayani kare martabar ta ba, karka taba ta, dan Allah Rayyan a karo na farko kayi abinda nace, badan ina so ba, sai dan shine dai-dai"
Shiru Rayyan yayi yana kara sadda kan shi kasa, dakyar Abbu ya iya mikewa, har jiri yakeji yana daukar shi sanda ya kai bakin kofa saboda kan shi da yake sarawa, har lokacin jin shi yake kamar yana yawo a duniyar mafarki
"Abbu..."
Yaji Rayyan din ya kira, da babu taimakon kofar da Abbu ya dafa tabbas da kafafuwan shi sun kasa daukar shi, rabon da yaji sunan shi a bakin Rayyan tun yana dan karami. Na rana daya ya kira shi haka bai taba ba
"Yaa Rabb"
Abbu ya fadi a cikin zuciyar shi, yana jin ko addu'o'in shi akan Rayyan dinne suka fara karbuwa, juyawa yayi yana kallon Rayyan da yake yawata idanuwan shi akan fuskar Abbun, akwai tarin abubuwa da yake so ya fadama Abbu amman kamar an shaqe shi haka yake ji. Idan bai fadi sauran da baisan ta inda zai fara ba, yana so ya fada mishi yanda tunanin zai taba martabar Layla yayi mishi ciwo sosai, yana kuma so ya tambaye shi ko shima a tsakanin shi da na shi mahaifin yana jin irin wannan abin da yake ji.
Yau yana so ya fadama Abbu abubuwa da yawa kamar yanda yake roke shi, ya fada mishi yanda yanzun haka yake ji kamar ana zare mishi rai kallon Abbun da yake, cikin tsokar jikin shi kamar an hura wuta. Amman ya kasa, babu kalma daya da zata iya fitowa daga makoshin shi da yake ji kamar an shaqe. Saiya sadda kan shi kasa kawai, numfashi Abbu ya sauke, ya dauki kiran da Rayyan din yayi mishi a matsayin amincewa da rokon shi.
"Nagode..."
Abbu ya fadi da sanyin murya yana ficewa daga dakin. Yau sai yake jin kamar akwai wata matsala mai girma tattare da Rayyan, matsalar da baisan ta inda zai fara shawo kanta ba. Amman addu'a, yana da yakini a kan addu'ar shi ba zata taba tashi banza ba, zai magana ta fahimta da Ayya, zai gaya mata da ta kara tsananta addu'arta akan Rayyan din, zai kuma yi magana da Mami itama dole. Rayyan ya kalle shi yau ya girgiza mishi kai a tambayar ko yana son Layla. Amman ya rasa dalilin da yasa ya kasa yarda, haka kawai zuciyar shi na mishi rawa akan abubuwa da yawa yau din nan.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Shine abinda yake furtawa yana karawa har ya kai daki
"Allah ka musanya mun kaddarar duk da zaka dora akan yarana, Allah ka fini sanin zuciyata, amman ni inaji kamar kowacce kaddara ba zata dauku a wajena ba in har ta hada da yarana..."
Shine kalaman shi a cikin sujjada, a tsorace yake da lamarin rayuwar gabaki daya. A tsorace yake da kaddarar da yake hangowa kamar tana kusanto yaran shi, kaddarar da yake son amfani da addu'a ya gina katanga a tsakaninta da yaran shi. Domin sune raunin shi, abinda zai taba su zai taba shi fiye da su.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Dec 5, 2020
16
Kwance take a cikin hostel a kan gado, ta lumshe idanuwanta, ba dan gadon yafi nata na gida ba, amman wani irin nishadi take ji yana shigar ta, nishadin da bata da kalaman misalta shi. Ta dauka ita da Zaria sai a mafarki, yanda Mami ta dauki fushi da ita har kasan ranta ta hakura da karatu a Zaria. Ta jigata, ta sha wahala, akan gwiwoyin ta da hawaye cike taf da idanuwanta ta tsugunna tana baiwa Mamin hakuri saboda bata ga abinda tayi mai zafin da zaisa Mami ta daina mata magana ba
"Ban san sau nawa zan jaddada miki MARTABAR MU a matsayin 'ya'ya mata ba kafin ki fara kare taki"
Mami ta fadi tana dorawa da
"Bance ki dubani ba, ki duba kanki da maraicin ki, yanzun mutunci ne ace kuna wannan rike junan ke da Rayyan?"
Hawayen da suka tsiyayowa Layla ta goge da hannu
"Ni dai Mami dan Allah kiyi hakuri, nace ba zan kara ba, na daina, dan Allah kiyi hakuri"
Numfashi Mamin ta sauke
"In zakiyi hankali dai kiyi, dan an Abbun ku ya tambayi Rayyan din yace ba son ki yake ba..."
Duk wani abu da Mami ta fada bayan nan bai karasa kunnuwa Layla da suka toshe da kalaman Mamin na karshe ba, har kuma ta baro gidan bata samu wani nishadi ba sai yanzun da take a kwance. Kwananta hudu da wani irin zazzabi da ya wajigata. Mami bata taba mata karya ba tun tasowarta, amman kiri-kiri ranar ta tsinci kanta da karyata Mamin, saboda karta komawa Rayyan shisa tayi mata karyar da bakin shi yace wa Abbu baya sonta. Bata tsammaci ya sota ba, batama san da gaske ta daga burinta akan shi ba sai da Mami ta fada mata kalaman da taji kirjinta kamar an kunna wuta a ciki.
Kwana tayi tana kuka, da safe fuskarta kamar kwabin alkubus saboda yanda ta kumbura, Mami bata ce mata komai ba, ko wanke-wanke tanayi tana kuka haka ta karasa shi ranar. Kuma yanzun ma da ta tuno kalaman sai da taji wani irin daci ya taso mata yayi tsaye a karkashin makoshin ta.
"Mami sai dai kiyi hakuri, amman ni ba zan rabu da Hamma ba, ko ya rabu dani ni ba zan rabu da shi ba. Mayya ce, amman mayyar shi"
Ta furta a hankali, kalmomin "Mayyar shi" din na zauna mata. Abin ya hade yayi mata yawa, saboda har suka bar gidan Rayyan baya mata magana, baya kiranta ya saka tayi mishi wani abu. Idan daga nesa ya hangota zai kalli wani wajen, ita kuma tsoron Mami yasa ko a waya ta kasa kiran shi. Ranar da zata koma makaranta babu kalar wa'azi da nasihar da Mami batayi mata ba, duk da batasan me Abbu ya fadawa Mami ta yarda tabarta komawa Zaria ba. Amman tana da yakinin yana da alaka da yanda watanni shidda ne kacal suka ragewa Rayyan din ya kammala karatun shi gabaki daya.
A mota wannan karin gidan gaba ya zauna, daga ita har Bilal bai musu magana ba, Aisha ma da suka biya suka dauketa, da ta gaishe da shi Layla bata ga yayi alamar yaji ba ballantana ya amsa, muryar shi take son ji da dukkan zuciyarta, amman yayi shiru, cikin kujera ma ya shige yanda ko wuya ta dan leqa ba zata iya ganin shi ba har suka sauka. Bata gaji ba dan da ta sauka ta zagaya ta bangaren shi tace
"Hamma..."
Gilashin murfin motar ya daga yana jan shi sama ya jingina kai a jiki yanda ko fuskar shi ma ba zata gani ba. Za kuwa tayi karya idan tace abin bai mata zafi ba. Dakyar ta danne hawayen da taji suna shirin zubo mata, duk da kwakwalwar ta na son ta tirsasawa zuciyarta tuno maganar Mami, ta tauna taga ko da gaskiya a ciki taqi yarda, hakan zai iya barazana da zaman lafiyarta fiye da yanda take ciki yanzun. Ko Rayyan baya son ta bai fadawa Abbu ba, bai fada ba, tana da sauran buri akan zai kalleta da fuskar soyayya wata rana, idan ma baiyi ba ya aminta da tarin soyayyar da ita takeyi mishi, ya ishe su.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.