Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 40 of 125

"Allah ya isa tsakanina dake Maryama, wallahi ba zan yafe miki ba. Kin hanamun natsuwa, kudin dana tara ma kina neman sakani asarar su wajen malamai, me nayi miki haka?"

Ayya ta dinga fadi tana juyi har wayewar gari, kan kunnenta aka kira sallar asuba. Dakyar ta mike tana gabatar da sallah, addu'ar nemarwa yaranta tsari tayi tana mikewa ta wuce kitchen tunda tasan Rukayya ko da zata fito sai ta gama karatun Qur'ani da azkar dinta na safe. Kuma tana son su Bilal suci wani abu kafin su fita, akan ce

"Mayu sunfi samun damar kama mutum idan ya fita baiyi karin safe ba"

To su da Mayya zasuyi tafiyar tasu kacokan, gara ta basu duk wata kariya da zata iya, kafin ta samu ta kira Hajiya Dije dan samun mafitar wannan bala'in, farraku take so ayi ma Layla tsakaninta da Bilal da Rayyan. Gara ayi musu katanga ta bakin karfe yanda zata sama musu lafiya duk kowa ya huta. Ko nawane kuwa zata kashe dan ganin an rabasu, da ita Mami take magana.

"Mu zuba mugani Maryama. Ke din banza"

Ta fadi tana kara cigaba da fere doya. Saboda tana tunani sai taga aikin yayi mata sauri sosai, dan harta soya doya da kwai kafin wani lokaci. Aikam kamar daga sama taga Rayyan ya fado kitchen din

"Ayya yunwa nake ji"

Ya furta da wani yanayi na rauni a muryar shi. Magungunan da yasha ne yasan suka wawake mishi ciki haka, kuma rabon shi da abinci tun jiya da rana, baici na dare ba saboda bayajin dadi. Yau dakyar ya fita masallaci, a hanyar dawowa kuwa har wani haske yake gani yana gilma mishi ta cikin idanuwan shi, a daddafe yayi wanka ya sake kaya yana yanke shawarar zuwa wajen Ayya din ta bashi koma meye yaci kafin yunwa ta kashe shi

"Ga doya na soya muku daman, in hada maka shayi?"

Ayya ta bukata tana kallon fuskar Rayyan din, dan gani takeyi kamar zai iya juyawa kowanne lokaci yace tafiya zaiyi. Yaushe rabon da tagan shi da sassafe haka. Kai kawai ya daga mata yana bude kular ya dauki doya daya yana sakawa a bakin shi. Yunwa yake ji sosai, shayin Ayya take hada mishi, batare daya kalleta ba yace

"Kar ki saka mun sikari da yawa Ayya"

Bata saka mishi din ba, tana gama hadawa ta sami faranti ta zuba mishi doyar a ciki, da kanta ta dauko mishi zuwa falo yana biye da ita da kofin shayin shi a hannu. Ajiye mishi tayi, dai-dai lokacin da Rukayya ta fito daga dakin

"Hamma..."

Ta furta cike da mamaki tana dorawa da

"Ina kwana"

Kallonta Rayyan yayi

"Rukayya. Lafiya...ya kika tashi?"

Wani murmushi da tayi mishi sai tasa yanajin wani iri, saboda tanayi kamar ya bata wani abu. Taji dadi har ranta, rabon dayayi magana mai tsayi da ita harta manta, yaushe ma tagan shi balle yayi mata magana

"Alhamdulillah, yau zaku koma makaranta ko?"

Zama Rayyan yayi yana jin kurbar shayin hadi da kallonta, idan tasan yau zai koma meyasa take kara tambayar shi, shisa bai son a fara wasu kananun gaishe-gaishe, suna jan surutun da bai kamata ba. Kai kawai ya daga mata yanaci gaba da karyawa abin shi

"Allah ya tsare muku hanya ya kaiku lafiya"

Kallonta ya karayi dan shine kawai amsar da zata samu yana cigaba da abinda yakeyi, itama kitchen ta wuce abinta. A hakan ma itace da godiya yau tunda har an kulata anyi magana da ita. Yana karasa cinye doyar ya tashi da kofin da plate din a hannun shi, daya shiga kitchen saida ya wanke su yana mayarwa inda yaga Ayya ta dauko su tukunna ya fito, ita kuma tana bakin kofa tana kallon shi, zuciyarta cike taf da kaunar yaron nata, yanzun take kara tabbatar da duk a yaranta babu mai sanyin hali irin na Rayyan, tun yana dan karamin shi yake da sanyin hali, lokaci daya ya canza, tayi sakaci da ta dauka abinda yasha ne, sam bashi bane ba. Mami ce ta shiga tsakaninta da yaronta ta juyar dashi ya koma haka.

Amman Allah yana nan

"In zuba maka ka tafi da itane? Ko zakuci a hanya?"

Dan jim Rayyan yayi, doyar tayi mishi dadi, yasan kuma inba gida ya dawo ba, babu wani abu da zaici mai dadi. Girkin Bilal hadiyewa kawai yake batare daya tsaya yaji dandanon a bakin shi ba saboda yanda yake a hargitse. Amman gara rashin dadin girkin tunda a gaban shi akayi, ya kuma daina cin abinci a waje yanzun tunda Bilal din yana girka musu. Kwanaki yace

"Bansan zan kewar Hamma Haris ba sai yanzun. Bilal kasheni zakayi? Meye wannan ka dafa?"

Harara Bilal din ya watsa mishi, duk da shima a lokacin kawai yana tura taliyar ne badan yana gane kanta ba

"Surutun duk da ba'a so kayi shi kakeyi, wallahi zan daina dafawa in dinga siya a waje"

Hakan da Bilal ya fadi ne yasa Rayyan din yin shiru, amman da gaske yake yayi kewar Haris a makarantar. Tunda abincin shi da dadi, kuma ranaku dai-daine baya dafawa ya kawo musu, wani lokacin ma har miyar da zasu kwana biyu idan yazo yana musu. Amman abinda Bilal yake dafawa yana da tabbacin ba abincin mutane bane ba.

"Akwai ne?"

Ya bukata yana kallon fuskar Ayya, saboda bayason su wanda zasuci a juye musu, kuma suzo sai sun sake dafawa

"Saboda ku na dafa daman ai..."

Ayya tayi maganar tana murmushi, shiru Rayyan yayi yana tsayawa. Hakan ya bata amsar da take bukata. Manyan robobin da takan zuba kayan miya ko saura abincin inta rage ta saka a firij ta dauko tana juye musu doyar ta fito ta bawa Rayyan din. Yana karba ya fice daga dakin, sosai zuwan shi ya ragewa Ayya damuwar data kwana da ita, gaskiya wannan Malamin ya cancanci duk tarin kudin daya amsa a hannunta, aikin shi mai karfine, ta dauka Mami tayi nasara. Dole ta kara komawa wajen shi yayi mata wannan aikin, tunda da tana tunanin tayiwa Hajiya Dije magana ne su sake wani Malamin da yafi shi zafi.

Rayyan kam dakin su ya wuce yana ajiye doyar da fadin

"Ayya ce ta zuba mana. Ni naci amman..."

Kai Bilal ya jinjina mishi, shi ba iya cin abinci yakeyi da sassafe haka ba. Jakun kunan su ya dauka ya kai mota, daman duk ya saka na Hindu a ciki. Ya dawo ya dauki robar da Rayyan din ya ajiye. Tun jiya da rana ya siyo ruwan roba tunda yasan Rayyan da shan ruwa kuma ba siya zai ya tafi da shi ba. To yanzun tunda motar su ce, duka ledar ya saka musu a ciki, ya dawo yana fadin

"Duka abinda zaka dauka ne ka fito da shi?"

Kai Rayyan din ya daga mishi

"Yayi kyau"

Bilal ya furta yana ficewa, tunda suka tashi Rayyan din yaga Bilal na sha mishi kamshi, yayi tunanin duniya ko yayi mishi wani abu ya kasa tunawa, shi bayason Bilal na mishi haka babu wani dalili. Sai yana saka shi jin babu dadi sam-sam. Mikewa yayi tunda yasan Bilal din zaije yayi sallama da Ayya ne, dakin ya kulle yana saka mukullin a aljihun shi. Wajen motar ya karasa, gajiya da yayi da tsayuwa ya saka shi taba murfin bayan motar yana samu Bilal bai rufe ba, nan ya shiga. Ba zai zauna a gaba Bilal din na mishi wannan kumbure-kumburen ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.