Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 7 of 125
"Nayi kewar ki"
Cikin idanuwan shi ta kalla, ita kadai ce macen da take iya hada idanuwa dashi kai tsaye haka, har maza kance yana musu kwarjini, ko Maryama bata iya kallon shi haka. Maimuna kance
"Kai din nawa ne, nawa ne ni kadai Ahmadi"
Kuma ya yarda shi din nata ne, duk da bai kasance nata ita kadai ba kamar yanda taso, amman natan ne
"Kaji ka, abinda muna tare a gida daya ko da yaushe, me yasa kake magana kamar ka dade baka ganni ba?"
Numfashi mai nauyi ya sauke
"Dan Allah mu daina fada, ki daina mun rigima, mu koma zaman mu kamar da"
Murmushi tayi kawai, murmushin da yake ganin kamar yana da wata manufa data wuce nishadi. Haka suka kasance daren kamar satin amarcin su, har wajen biyun dare, da Maimuna lafe a jikin shi suna bacci. Da yake shi bamai nauyin bacci bane, kwakkwaran motsi ma yakan ji, cikin baccin yake jin kakarin aman da ya sashi bude idanuwa yana saurarawa, sosai yake jin ana kakarin, yaso zame Maimuna a hankali ba sai ta tashi ba dan ya fita ya duba, amman itama din ba nauyin baccin gareta ba
"Ina zaka je?"
Ta furta muryarta cike da bacci tana murza idanuwa
"Kamar Maryama ke amai, bakiji bane ba?"
Ya amsa kasa-kasa saboda dare, tsaki Maimuna taja
"Munafuncine kawai, dan Allah ka koma ka kwanta"
Da mamaki yake kokarin ganin idanuwanta saboda duhun da yake dakin. Rigar shi da yake tunanin tana ajiye wani waje kan gadon yake lalube har ya samota, kokarin sakawa yake a jikin shi Maimuna ta tashi zaune
"Fitar zakayi kenan?"
Ta bukata a harzuqe, hakafa kwanaki ta fito tana wannan kakare-kakaren, Ahmadi ya kwana zarya yana fita dubata. Shine yau daga dawowar shi dakinta zata sake bullo da wannan sanaben
"Kasan dai yau kwanana ne ko? Halin matane baka sani ba Ahmadi? Munafuncine ba wani abu ba"
Kai kawai ya girgiza yana sauka daga kan gadon
"Bari in dubata...."
Itama saukowa tayi, zuwa lokacin idanuwanta sun saba da duhun tana dan ganin shi, aikuwa hannu yaji ta riko mishi
"Babu inda zakaje fa, kanajin ma kamar ta koma daki. Wannan ai shiga hakki ne"
Fisge hannun shi Ahmadi yayi
"Me yake damunki ne wai? Ina tausayinki ya tafi? Ko ta tafi daki bazan duba yarinyar mutane bayan naji sarai amai tayi ba? Kinga Maimuna ki fita idona kafin in saba miki"
Ya karasa yana fara tafiya zuwa hanyar kofa, yanajin ta biyo shi, baibi takanta ba ya fice daga dakin, hasken farin wata ya haske tsakar gidan, ko takalma bai saka ba ya nufi bangaren Maryama, yana shiga ya sameta a zaune da fitilar kwai a dakin
"Maryama? Jikin ne?"
Kai ta girgiza mishi
"Aa wallahi. Amai ne kawai, inajin kankanar dana sha na kwanta ce ta juya mun ciki"
Kuma da gasken take, dan karatun littafin tarihin Annabi (SAW) Kamalalle takeyi bacci ya dauketa anan kasa inda ta saka filo, kawai farkawa tayi tana zufa, kafin taji wani amai ya taso mata, dakyar takai tsakar gida. Duk wani abu da yai saura a cikin nata kuwa saida ta fitar dashi, kuma garas take jinta banda yar galabaita da tayi. Ahmadi bai yarda da ita ba, tsugunnawa yayi yana saka hannu ya taba wuyanta ko da zazzabi, amman lafiya kalau yaji jikinta
"Sannu..."
Murmushi Maryama tayi
"Yawwa... Kaje ka kwanta, kaga da safe zaka fita, gara ka huce gajiya"
Kallonta yakeyi yana son tabbatar da lafiyarta
"Babu wani abu da yake miki ciwo dai ko?"
Kai ta jinjina mishi
"Kin tabbata? Ki fadamun dan Allah"
Murmushi takeyi sosai
"Allah babu inda yake mun ciwo...dan Allah kaje ka kwanta"
Numfashi Ahmadi ya sauke
"Shikenan, Allah ya kara lafiya, idan da wani abin dai kizo ki tasoni kinji ko? Allah ya tashe mu lafiya..."
Kai Maryama ta jinjina mishi, tana kara ganin dalilin da yasa kaf dangi kowa yakejin daman yar shi ce a gidan Ahmadi, ba zata gaji da godewa Allah da wannan damar da ta samu ba, har zai fita ya kara juyowa
"Ko in miko miki ruwa?"
Kai ta girgiza mishi tana nuna kwanon sha da yake a rufe
"Kagan shi nan na dibo fa tun dazun..."
Sannun dai ya sake yi mata kafin ya fita, ya gyara mata labulen dakyau saboda sauro. Kafin ya wuce inda ya samu Maimuna a bakin kofar dakinta tsaye
"Idan cin amana dai kasa a gaba babu inda zai kaika wallahi"
Ta karasa maganar ranta na suya, sai takejin kamar kamshin turaren da Maryama kan hayaqa a zuwan turaren wuta a jikin shi. Watakila wata sa'ar Malamin ta ya bata na fito da Ahmadi tsakiyar dare ta goga mishi wannan shu'umin turaren
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Dan girman Allah Maimuna ki saka ma ranki salama"
Ahmadi yai maganar cike da gajiya, yana mamakin kishi irin nata, wani lokacin yana jin daman ya hakura sun rayuwa su kadai kamar yanda taso, daya kaucewa duk wannan rigingimun
"Ta ina zan fara sakama raina salama bayan baka bani wannan zabin ba? Bance maka munafunci bane, kawai bata kaunar ganin na kebance dakai saita tsiri wani abin da zaka ha'ince ni"
Rabata yazo yi, gara ya wuce ya kwanta, inya tsaya biye mata zaiyi. Kamar ba ita bace tagama mishi alkawarin zasu zauna lafiya dazun nan. Amman sai ta tare kofar, wani irin kishine turnuke da zuciyarta, kamshin turaren Maryama da hancinta yake jiye mata sai take ganin kamar wani abin sukayi a yan mintina daya dauka a dakin nata da sukai mata nisan awanni, tare mishi hanya tayi
"Ka koma dakin nata mana, ka koma inda ka fito Ahmadi tunda haka kake so tun daga farko"
Ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata, yana da nashi dakin, kudine da sun shigo hannun shi akwai hidimar da zaiyi dasu, bai karasa bangaren ba, kuma duk da haka akwai wani dakin da zai iya zuwa ya kwanta a bangaren Maimuna, dakuna uku yayi mata, harda dakin girki, bangaren Maryama dakuna biyu itama da na girki, har lokacin akwai tankamemen fili da katanga kawai yaja mishi, banda filin tsakar gida, wannan sai a hankali zai dinga gine kayan shi tunda ba sauri yake yi ba. Hannun ta ya kama ya cire daga kofar yana shigewa cikin dakin da ta bishi.
"Wallahi Allah zai kamaka idan baka mana adalci"
Runtsa idanuwan shi yayi yana bude su hadi da sauke numfashi, kukan da takeyi na kara taba zuciyar shi
"Kamshin turarenta kakeyi fa, Ahmadi kamshin turarenta kakeyi ranar girkina. Wanne irin rashin adalcine wannan? Ko cikin da take dashi ne yasa kake wannan rawar kafar?"
Juyowa Ahmadi yayi yana kallon Maimunar da mamaki
"Ciki kuma?"
Hawaye ne suka kara tsiyayo mata
"Kana nufin kace mun baka sani ba?"
Mamaki yake kan mamaki
"Maryaman ce take da ciki?"
Ya kara tambaya, kai kawai Maimuna ta jinjina tana rabashi ta wuce kan gado ta kwanta. Ya dade a wajen yana jinjina maganar, ko dan ita Maimuna macece shisa ta gane Maryama na da ciki. Har ran shi kuma yaji dadi, yanzun yake fahimtar kwadayin manjan da ake ta mishi abinci da shi kwana biyu. Murmushi kawai yayi yana karasawa kan gadon. Kukan da Maimuna takeyi na kara dagula mishi lissafi, matsawa yayi daf da ita yana rikota jikin shi, tun tana kwacewa harta hakura
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.