Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 125
Ba tsoron biye rigimar da Maimuna takan takaleta da ita a duk rana takeyi ba, kalaman Ahmadi ne suke tausarta
"Da bana sonki ba zan aureki ba Maryama, kamar yanda kauna ce tasani auren Maimuna kema haka. Idan ina da mutunci a idanuwanki zaki tayani kaucewa rigima da Maimuna, dan Allah ki kauda kai daga lamurranta, ki tayani wanzar da zaman lafiya a tsakanin ku gwargwadon iyawarki"
Tun kafin zama karkashin inuwar aure ya hadata da Ahmadi ta tabbatar da nagartar shi. Ta dauka tasan soyayya a iya tsayin lokacin da suka dauka kafin auren su, sai yanzun take ganin banbanci. Yanda Ahmadi yake kula da ita, yake gudun duk wani abu da zai sosa ranta ya kara daga daraja da matsayin shi a zuciyarta. Saboda shi zata cigaba da kauda kai daga halayen Maimuna har Allah ya fahimtar da ita cewa su dukansu zaman aure sukeyi, kuma ita da niyyar mutu ka raba ta shigo gidan, babu inda zata tafi.
Shisa take kokarin ganin bata shiga harkarta ba, bata taba ganin gidan da keda kishiyoyi kowa na abincinta daban ba tun tasowarta sai a nasu gidan. Ta dafa sau biyu, ba zatace ga abinda ya faru ba, Ahmadi ya ce mata kowa abincin shi zai dinga dafawa, abin har yanzun wani iri yakeyi mata. Ga yaran Maimuna da shiga rai, musamman Zubaida, ko dan Ahmadi har ranta take jin yaran. Kiri-kiri Maimuna ta hana mata rabarsu, ko inda take basa zuwa, buta wannan idan tata ce basa tabawa, in ta dan samu sunje kusa da ita to Ahmadi ya dawo gidan, kuma ranar itace da girki, shima kome zata basu kai suke girgiza mata a tsorace.
Yau ma kukan Rayyan da take tajine yai mata tsaye, taso ta share, amman taji shigar Maimuna bandaki, kuma tasan sauran yaran suna makaranta. Tunanin ko an dora shi a samane ya fado shisa yake wannan gigitaccen kukan yasata tashi ta shiga bangaren Maimuna din, komin yanda basa ga miciji yaron baisan me duniyar take ciki ba balle zafin kishi irin na mahaifiyar shi. Tana shiga taga kuwa wajen mitsilniya yaja zanin shimfidar ya nade fuskar shi da shi, samu tayi ta cire mishi, ta gyara ne zata dauke shi taji shigowar Maimuna, bangazar da tayi mata da babu bango a kusa zata iya faduwa. Rayyan din Maimuna ta dauka tana saka shi a jikinta hadi da jijjiga yaron
"Kashe mun shi zakiyi Maryama? Meya kawoki dakina?"
Kalaman Maimunan taji har ranta, sun mata zafi matuka
"Wacce irin magana ce wannan? Kukan shi naji yayi yawa, kuma naji kamar kin shiga bayi shisa nazo in duba"
Cike da rashin yarda Maimuna take kallonta, Gwaggo Bare tayi mata kashedi karta bar Maryama na rabar mata yara, kafin ta shafa musu abinda in rayuwar su bata salwanta ba za'a sabauta su. Yanda tayi nasarar mallake Ahmadi ba zata bari tayi nasara a kanta ba sam. Karfi da yaji jituwa ta musu karanci tsakaninta da Ahmadi, laifinta yake gani yanzun a duk wata karamar magana da zasuyi. Ranar da aka daura mishi aure da Maryama ne rana mafi muni da tashin hankali a rayuwarta. Ba zata manta bayan fitar su shi da Maryama daga dakin yanda ta dafe cikinta tanajin kamar zai fito duniya ranar saboda yasan kalar tashin hankalin da take ciki.
Kwanciya tayi a kasa tana sakin wani irin gunjin kuka zuciyarta kamar zata fado, a haka Ahmadi ya shigo dakin yana kamata
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Maimuna me kikeyi haka? Dan Allah ki rufamun asiri, kinga bake kadai bace ba... Kiyi hakuri, kiyi hakuri kisawa ranki salama, inda nasan kishinki yakai haka wallahi dana hakura da auren nan... Oh Allah na"
Yake fadin yana sake riketa a jikin shi ganin yanda numfashinta har sama-sama yake saboda kuka
"Wata zaka raba, Ahmadi wata zata dandani soyayyarka yau, dan Allah karkaje, karka hada mun jikinka da nata, karka cakuda kaunata data wata, Ahmadi mutuwa zanyi Allah idan nasan a wajen wata zaka kwana"
Maimuna take maganar kamar bata cikin hayyacinta. Har yau ba zatace ga yanda akayi ya sulalace yabar dakin ba, bama zata tuna ko ta runtsa ko bata runtsa ba, a satin farkon nan ta wahala. Tayi mamaki da mata suke kiran nakuda tafi komai ciwo a sha'ani na rayuwa. Zata zabi haihuwa goma a jere indai za'a koma baya a goge Maryama daga rayuwar Ahmadi, ko haihuwar Zubaida data kwana hudu cikin matsananciyar nakuda kamar ba zatai rai ba bai kai mata zafin ciwon da takeji a zuciyarta duk idan Ahmadi ya kasance a dakin Maryama ba.
A kwanakin bakwai bata tsaya tasan me suke ci shida Maryama ba, dan batai mishi karyaba washegari daya shigo mata daki kamar bai hada shimfida da wata ba
"Idan abin kari kake jira zaku wuni da yunwa daga kai har ita, wallahi zan zabi mutuwa akan in dafa abincin da Maryama zataci"
Da suka kwana bakwai ma ta karbi girki ko lafiyar kirki bata da ita, tana ganin Maryama da salo dan ta zuba mata wani abu tace zatayi girkin. Su Zubaida gidan Yaya Ayuba ta turasu sukaci abinci, itama daga can din aka kawo mata, washegari da taga ta shiga ta dafa tazo tayi mata maganar da ko amsa bata iya bata ba, Ahmadi na dawowa ya shiga dakinta da ya duba karfin jikinta tace mishi
"Ba zan iyacin abinda duk ya fito daga hannun matarka ba, yarana ma ba zasuci ba ballantana a barbada mana abinda aka baka aka mallake ka"
Yanda yake kallonta rai a bace bai ko girgizata ba
"Maimuna yaushe ne zakiyi sanyi akan maganar Maryama? Da kika taso gidanku abinci kikaga an raba? Me yasa nine zan fara wannan al'adar dan kawai kin dauki zafin kishi kin saka a ranki"
Batasan ko yanda ya nuna dan Yayya tayi hakurin zama da kishiya itama ya zame mata dole tayi wannan bane a fakaice ya taba zuciyarta, ko kuma maganganun da yake mata a fadace saboda Maryama sune suka tunzurata ba, amman bataso hawayen da suka zubo mata ba
"Ni dai na fada maka, kai za'ayiwa asarar abinci saboda wallahi ni ba zanci ba..."
Runtsa idanuwan shi Ahmadi yayi yana bude su a kanta
"Idan akayi hakan shikenan? Idan kowa ya dafa abincin shi yayi miki?"
Kai ta daga mishi, bai sake furta wani abu ba yasa kai ya fice daga dakin. Idan fushi yayi ma shiya jiyo. Ita kama tasan ba zataci duk wani abu da zai fito daga bangaren Maryama ba, su Khalifa ma daki ta sakasu taja kunnen su akan Maryaman ganin yanda take wani jansu a jiki. Dan Zubaida ma ca tayi mata Dodo Maryama take zama da dare, idan ta karbi abin hannunta zata zo ta cinyeta tana bacci. Yaran kuwa har ransu suka dauki hudubar mahaifiyar tasu
"Bana so, karki sake shigomun daki, idan siqewa kikaji yanayi bance ki taimaka mishi ba....idan burgeni kike sonyi Maryama dan girman Allah ko numfashi karkiyi kusa dani..."
Murmushi mai ciwo Maryama tayi, wani bangare na zuciyarta takeji a gajiye da halayyar Maimunar
"Duk yanda bakyason ganina Ahmadi ya hadamu..."
Ido a bude Maimuna take kallonta
"Magana zaki fadamun? Dakina zaki shigo ki fadamun magana?"
Wani murmushin Maryama ta sakeyi da yasa Maimuna takeji kamar ta dauketa da mari, kafin ta kai hannu a cikin ta tana shafawa, haka kawai yau sai takejin tana son bakantawa Maimuna rai ko yayane
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.