Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 93 of 125
Idan duk tarin kaunar da take mishi bai hanata fadin abinda ta fada ba, bashi da tabbas akan abinda mutanen da suke jiran kuskuren shi zasu fada, cike da matsananci tsoro Abbu yake kallon Yaya Ayuba
"Ya zanyi? Me zanyi?"
Dan jim Yaya Ayuba yayi, a cikin abin duka baiga wani zabi mai sauki ba, in dai cikin yana nan basu da tabbas akan tsayawar maganar a tsakanin su kawai. Amman yanzun bayason fadin wani abu da zai kara firgici da fargabar dan uwan nashi, shisa ya zabi fadin
"Shi Rayyan din ya kamata ya aure ta"
Kai Abbu ya jinjina cikin aminta da maganar da Yaya Ayuba yayi. Wayar shi da take kan kujera ya dauka yana kiran Ayya
"Ki kira Rayyan sai kuzo tare"
Ya fadi tana dagawa, bai jira amsarta ba ya kashe. Mami ma kiranta yayi yace ta taho da Layla
"Gara su san da maganar"
Ya fadi yana kallon Yaya Ayuba da baice komai ba, bayason ya tuna ma Abbu ko da za'ayi auren sai bayan ta haihu dole. Sosai yake kara jinjina lamarin. Ayya ce ta fara shigowa dakin da sallama, duk da gefe ta samu ta zauna. Ta kasan idanuwanta Abbu take kallo, yanda fuskar shi take a kumbure na taba zuciyar ta, zata dauke mishi duka wannan tashin hankalin in zata iya. Saida ta koma daki ta zauna ita kadai sannan tasan babu yanda za'ayi ta taba son Mami da Layla, saboda da bata dauko musu yarinyar ba da yanzun suna zaman su lafiya, da bata shigo musu da ita cikin gida ba, da mijinta bai shiga wannan yanayin ba.
Da ta dauko ta din, data riketa yanda ya kamata, da bata barta tabi mata yaro har Zaria ba duk wannan abin da sun kauce mishi. Sai dai in tayi magana yanzun za'a ce ita din bata san kaddara ba, kuma ba haka bane ba, tasan kaddara, ta dai san akwai wadda take tafiya da son zuciya, akwai kuma wadda take hade da sakaci irin wanda Mami tayi kuma Abbu na kallo ya biye mata. Da sun fada mata ita da tasan yanda zata nisanta yaronta daga Layla, watakila da duk basu zo nan ba. Yanzun da taje ta kirawo Rayyan din, zaune ta same shi ya hada kan shi da gwiwa, Bilal ma yana bakin kofar dakin a zaune ya hade na shi kan da gwiwa. Sai bayan ta fito ne ta dafa shi ya dago mata fuskar shi da take a kumbure kamar wanda yaci kuka
"Ka tashi daga nan Bilal, ko dakina ka koma"
Numfashi ya sauke, da wani yanayi yake kallonta
"Ki barni anan Ayya, dan Allah ki barni"
Bata da zuciyar tursasa shi, shisa ta kyale shi din tana tafiya. Yanzun ne tayi mamakin ganin shi ya biyo bayan Rayyan daya juya yana mishi wani irin kallo, yanda yayi tsaye na sanyaya wani abu a zuciyar Ayya, bata san meye take gani a tsakanin yaran nata ba, amman bata son shi, koma menene yana kara ma wutar tashin hankalinta fetur. Gefe Rayyan ya karasa yana tsayuwa, Bilal ne ma ya zauna a kasa kusa da Abbu. Yaji me Ayya tace, yaji tana fadama Rayyan din Abbu na kiran shi, sai da ya fito sannan shima ya mike da nufin rufa mishi baya
"Ina zaka je?"
Rayyan din ya tambaya, ya gwada shiga dakin bayan ya dawo sallar la'asar, ya sake yin magana da Rayyan, ko baice komai ba ya zauna a tare, amman yana daga labulen ya dago yayi mishi wani kallo da ya saka shi mayarwa ya saki. Bayason ganin shi, kamar yanda kowa na gidan yake gab da fara ji a kan shi ya sani, har karshen rayuwar shi zai kasance mai godiya da karamcin su, yanda suka karbe shi suka darajta shi. Ba kuma zai ga laifin su ba, yaci amanar sune shisa, yayi musu kuskuren da ko bakin da zai basu hakuri baida shi.
"Ba zaka dauki laifin da bakayi ba, ba zan bari ba Hamma"
Sai da Rayyan din ya dan dafe kan shi sannan ya saki yana kallon Bilal din
"Karka biyoni Bilal, karka fara biyoni..."
Kamar baiji kashedin Rayyan din ba, yana juyawa, inda ya saka kafar shi nan Bilal ya mayar da tashi, yana tsayawa shima ya tsaya, batare da ya juyo ba wannan karin yace
"Nace karka biyoni bakaji ko?"
Sun kusan minti daya a tsaye kafin Rayyan din ya sake cigaba da tafiya, wannan karin sai da ya sha kwana sannan Bilal yabi bayan shi. Ba zai zauna ya sake hada Rayyan din da su Abbu ba, bayan abinda yayi, ba zai bari ya kara wani ba. Ko yanzun da Rayyan din ya bishi da wani irin kallo, kan shi kawai ya sadda kasa, ya zauna kusa da Abbu ne saboda ya san damar yin hakan na gab da kwace mishi, zuciyar shi yake ji zaune cikin kirjin shi tana dokawa a hankali a hankali, kamar wadataccen jini baya zagaya mata, suna zaune Mami ta shigo, Layla na bin bayanta, har yanzun tun kayan dazun ne na jikinta, ko hijabin ma bata cire ba.
Inda suka barta bata tashi ba, anan rana ta sameta, anan kuma tabarta, ko sallah batayi ba sai da Magriba da Jabir yazo ya sameta tana zaune anan, shima har zai wuce saiya kasa, ya dawo baya
"Ki tashi daga nan"
Taji shi, ko karfin kirki bata da shi balle tayi motsi, hannunta ya kama yana dagata, batayi musu ba ta mike. Janta ya farayi, suka wuce Mami da take zaune a kasa kan kafet, sai da ya kaita dakinta sannan yace
"Kinyi sallah?"
Kai ta girgiza mishi batare da ta kalle shi ba
"Tun dazun kina waje Layla? Baki tashi ba? Anan kika zauna rana ta kare akan ki? Baki da hankali ko?"
Idanuwanta taji sun kara cika da hawayen da ta dauka sun kare mata da fadan Jabir din
"Ki wuce kiyi sallah"
Batayi mishi musu ba ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito, tana cikin sallah taji shigowar Jabir din kafin ya ajiye kofi yana sake ficewa. Sai da ta gama gabatar da sallolinta duka, zuwa lokacin an kira isha'i shisa tayi, bakinta yayi nauyi, bata san kalar addu'ar da zatayi ba. Dan sallar ma sai take ganin kamar ta makale ne a wani waje, kamar ba zata isa inda za'a karba ba, saboda cikin da yake jikinta, saboda daudar da take ji a tattare da komai nata. Kofin da Jabir ya ajiye ta dauka, shayine mai kauri ya hada mata, sai taji cikinta yayi wani qugi da yunwar da take tattare da ita, ga zazzabi ya sake saukar mata.
Tana kurbar shayin hawaye na zubar mata, batama gama sha ba taji muryar Mami a saman kanta
"Abbun ku yana kira"
Mami ta furta tana juyawa, dan shayin da ta samu ya shiga cikinta taji yana barazanar dawowa saboda tashin hankali. Shisa ta dade a zaune kafin ta iya mikewa. Kara hautsinawa cikinta yayi da taga Rayyan din, gefen Mami ta zauna, tana kokarin ganin idanuwan Rayyan ko yayane, amman a tsaye yake ya jingina bayan shi da bango, kan shi a kasa. Wani irin shiru ne a cikin daki da kowa yake ji a jikin shi kamar bargo, ganin Yaya Ayuba bashi da niyyar cewa komai yasa Abbu yanke hukuncin yin magana, ya dauka zai saukaka mishi komai ta hanyar yi ma su Mami bayanin shawarar da suka yanke.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.