Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 115 of 125
"Ina Bilal? Lambobin shi gabaki daya a rufe, mun kasa samun lambar Rayyan, kaima taka tayi wahala saboda babu yan set dinku da sukayi saura, wallahi tunda aka dawo muke tunanin ko lafiya....sai yanzun muke tunanin kalar zaman da mukeyi da yanda ya kamata ace kowa yana da adireshin gidan kowa ko da halin ziyara bai samu ba"
Wani murmushi mai ciwo Haris yayi, zuciyar shi daya dauka ta dake yaji tana rawa, muryar shi ma a raunane yaji ta lokacin daya kalli Abdul da fadin
"Ya rasu, hatsari yayi. Ya rasu..."
Ya karasa maganar wani abu na tokare mishi makoshi
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Din da Abdul ya furta cike da tashin hankali na saka shi raba Abdul ya wuce cikin gidan. Da yake ya karbi mukulli a wajen Ayya, shiya dauko ya saka yana bude dakin, bai shiga tashin hankali ba sai daya kunna kwan dakin yana ganin yanda yayi wata irin kura kamar mutane basuyi rayuwa a ciki ba. Dakin yake karewa kallo, yana hango wajeje da lokuttan da suke zaune a ciki shi da Bilal, sai yaji har kirjin shi ma zafi yake. Ba zaice ga mintinan daya dauka a cikin dakin ba kafin yaji shigowar yan gidan su Bilal din da babu wanda yace mishi komai, dakin suka fara taya shi sharewa.
Kusan babu wani abu da yayi, su suka dinga hada komai, duk yanda ya so ya kwashe komai saiya kasa, daga takardun da yake tunanin suna da muhimmanci sai suttura ya dauka, sauran hatta da katifa nan yabar ma su Abdul da yake ganin yanda mutuwar Bilal din ta dake su sosai. Lambar shi suka karba da fadin zasu shiga Kano suyi wa Ayya gaisuwa. Kai kawai ya jinjina musu yana ficewa ya shiga motar shi da aka loda kayayyakin a ciki. Sai daya zauna sannan yaji jikin shi na rawa ba kadan ba.
Rayuwa aikin banza, babu wani abu da yake da tabbaci a cikinta, ba mutuwar Bilal kadai yake ji ba, harda tashi mutuwar yake hangowa, duk tarin burukan da suka ci shi da Sa'adatun shi mutuwa zata iya yanke musu shi, ga Bilal nan da Aisha, ya tabbata yarinyar bata taba hango auren wani ba Bilal ba, soyayya tun firamari ake yinta, ta ina zata fara yanzun? Wa zata budewa zuciyar ta, wanne waje ma zai samu bayan ko ina cike yake da kaunar Bilal? Hawayen da yaji ya share a kasan zuciyar shi yana fadin
"Allah ya jikan ka Bilal, kai din mutumin kirki ne. Allah ya sa mutuwa hutun ka ce"
Sai dai daya ajiye kayan Bilal a dakin su akwai wanda ya dauka, duk yanda yaso ya barwa Rayyan komai saiya kasa, ciki harda wannan hular da ya saka a kan shi, tare sukaje suka siya da Bilal ba zai manta ba, shi da kan shi ya dauketa ya dora ma Bilal din a kai
"Hamma ni fa bana son wannan zanen, ina da shigen shi"
Maganar Bilal din ta dawo mishi a lokacin
"Ni ina son shi, tunda ni zan biya"
Dariya Bilal yayi
"Jiba ikon Allah, dan zaka sai mun shine ba zan zabi abinda nake so ba? Yaushe aka taba yin haka?"
Shima dariyar yayi
"Yau za'a fara idan ba'a taba ba"
Sai kuma ya dinga yawan ganin Bilal din da hular, duk kuwa yanda manyan kaya ba damun shi sukayi ba
"Na dauka baka son zanen?"
Ya tambaya yana saka Bilal din yin dariya
"Dana dan shiga haske da ita rannan sai naga ya danyi kyau"
Hannu Haris ya kai da nufin cire hular daga kan Bilal daya kauce yana dariya
"Ba'a kyauta a kwace Hamma"
Shi din da Bilal zai iya cewa kamar abokai ne ba Yaya da Kani ba, ba zaiyi son kai ba, tunda ya kula kusan kowa zaice da kadan shakuwar da take tsakanin Rayyan da Bilal tafi wadda take tsakanin su. Amman yau Rayyan ya saka shi jin wani iri, yanda ya tambayi hular Bilal ce a kan shi kamar babu wanda yake da damar saka wani abu na Bilal banda shi, kuma har ga Allah bai san ya akayi ya sakata ba, har sababbin huluna yana da su daya keta siya na tanadin bikin shi da aka hada lokacin shi dana Rukayya. Kawai ya dauki wadda hannun shi ya fara kaiwa ne, sai kuma akayi dai-daito ya dauki wannan din.
Shisa ya daga mishi kai kawai yana ficewa, ba zasu fara gwada waya fi kusanci da Bilal ba. Musamman yau din, wani irin numfashi Rayyan yaja yana fitarwa cikin yanayin da ya saka Bappa kallon shi
"Idan ya mutun kuma fa? Bappa idan ya mutun da gaske ya zanyi?"
Rayyan ya karasa muryar shi a tsorace, saboda da gaske baisan yanda zaiyi din ba idan ya rasa Bilal na har abada
"Hakuri... Shi zakayi Bilal, hakurin da kowa yakeyi a yayin rashin, hakurin da su Ayya sukayi..."
Kai Rayyan yake girgizawa Bappa, saboda yanajin kamar bai shirya ba, kamar ba zai iya ba. Ba duka labarin Bappa ya sani ba, kadan daga ciki da Rayyan ya fada mishi sai kuma sauran guntayen da yake tattarawa a kullum, sai ka dauka labarin ka cike yake da hargitsi, sai kaji na wani saiya saka ka gode Allah da kalar taka kaddarar
"Hakuri zakayi Rayyan, ayyukan ka zaka cigaba da gyarawa idan kana son sake rayuwa da shi"
Cike da rashin fahimta Rayyan ya kalli Bappa, kalaman Baba ne shima zai ara yau, duk da sun jima basuyi mishi aiki ba, amman sun gyara abubuwa da yawa a tare da shi, sun samar mishi natsuwar da yake fatan su samarwa Rayyan a yanzun
"Rayuwa ba ita bace karshen mu, duk da itace farkon mu, amman karshenta mu musulmai shine farkon wata rayuwar, kasan Bilal da ya tafi ba sauri yayi ba, mu da muke nan lokaci muke jira. Ka gyara ayyukan ka, duk da basu bane zasu tsirar damu, amman ka gyara a duk rana dan ka samu damar tambayar Bilal idan ka natsu waje daya a aljanna, idan ya rigaka wuce karya jira na tsayin lokaci. Ba nan bane karshen zaman da zakuyi Rayyan, ka sani, ina tuna maka ne kawai"
Numfashi Bappa ya sauke
"Soyayyar da zaka yiwa Bilal a yanzun tana cikin yawan addu'ar ka ba kuncin ka ba... Ka karasa ka fito mu tafi"
Cewar Bappa yana ficewa daga dakin, numfashi Rayyan yake ja yana fitarwa. Wani irin ciwo zuciyar shi takeyi da yanda yake son tursasa mata amincewa da sun rasa Bilal amman wani bangare nata yana mishi taurin kai. Ruwa ya karasa ya dauka ya sha, abinda yakeji yana nan tokare da kirjin shi, hular shi ya dora saman kan shi yana zira takalma a kafar shi ya fita shima. A bakin kofa ya tsaya yaja numfashi yana danne abinda yake ji kafin ya samu ya dora murmushi saman fuskar shi.
*
Zaune take a gefen Rayyan a cikin dakin Abbu, ta hade yatsunta da take wasa dasu waje daya. Gani takeyi komai da yake faruwa kamar mafarki tun da safe da ta tashi, da taimakon su Rukayya ta shirya, da yake Sa'adatu yar gidan Yaya Ayuba tana kunshi ita tazo har gida tayi wa Layla din. Kafin wani lokaci ta fito tsaf a amaryarta, tayi wani irin kyau cikin leshin da ta saka kafin a dawo daurin aure. Akwai banbanci kadan a yanda ta hango aurenta da kuma yanda ya kasance a yau din, ba mutanen bane sukayi kadan, wasu a cikin sune babu, musamman Bilal da kewar shi take tabata a cikin kwanakin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.