Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 122 of 125
"Ayya..."
Huda ta kira cikin sabon tashin hankali tana juyawa, yanayin da yasa Ayya kallon inda ta kalla, tana ganin Bilal, runtsa idanuwan tayi tana sake bude su hadi da jin kamar wani ya watsa mata ruwan kankara saboda tsikar jikinta da ta mike gabaki daya, wani irin yanayi ne da babu kalaman da zasu misalta shi, dole Huda zata firgice, ta sha hasaso ganin Bilal, ba'a mafarki ba a ido biyu, amman da gaske ne, girman kusanci ba zai taba hanaka tsorata ba idan har zakaci karo da mutumin da kasan mutuwa ta rabaku, saboda wani irin tsoro ne kamar bargo ya nannade daga kafafuwanta har zuwa kanta kafin ya sami wajen zama a cikin zuciyar ta.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Jan 30, 2021.
34
"Ayya..."
Bilal ya kira yana sa ta raba idanuwanta da inda yake tsaye tana kallon Rayyan daya daga mata kai yana tabbatar mata da yaji kiran, ba kunnuwanta bane kawai suka ji cewa Bilal ba tsaye kawai yake a cikin dakin ba, har magana yakeyi. Hankalinta ta sake mayarwa kan shi tana ganin yanda yake takawa yana karasawa inda take kamar wanda yake koyon tafiya, da duk takun da zaiyi da yanda zuciyarta take kara dokawa a cikin kirjinta da wani irin tsoro, sai dai kamar jira kawai yake ya karasa inda take kafafuwan shi su kasa daukar shi dan anan gabanta ya durkushe. Yayi kuka mai yawa bayan da ya tafi, amman baiji kalar kukan da yake tattarowa daga duk wani lungu na zuciyar shi daya taba yin ciwo ba irin yanzun.
Dan wani irin gunji ya saki mai tsuma zuciya yana rike kafafuwan Ayya da itama taji sunyi mata wani sanyi, Huda ta ture gefe, ba tsugunna tayi ba, zama tayi akan kafafuwan ta kamar mai zaman sallah tana kallon Bilal, ya sha bamban da fatalwin da take gani a fina-finai, jikin su baiyi kalar na shi ba, batajin kuma ana iya jiyo hucin numfashin su, a hankali ta daga hannunta da kafin ta kai shi fuskar Bilal ya kama shi da duka nashi biyun. Ko da fatalwa ne shi na danta ne, Bilal ne. Hannun shi na shine, hannu ne daya saba kama nata tun kafin yakai girman haka.
Duk da yanzun girman bai canza yanayin shi ba, zata gane hannun Bilal a cikin dubban hannaye, saboda zai rike nata hannun kamar yanda ya rike shi yanzun, cike da yarda da kaunar shi da batajin wani da bai san zafin da ba zai iya fahimta.
"Bilal"
Ayya ta kira yana daga mata kai kawai saboda kukan da yake yi, abu na farko da duk wata mahaifiya takeyi a lokacin da take ganin hawayen da na ita bace sanadin zubar su shi Ayya tayi, zame hannun daga cikin na Bilal ta kama shi zuwa jikinta duk kuwa da girman shi, kan shi ya dora a jikinta yana sake sakin wani sabon kukan, kukane na kewar ta, na kewar su gabaki daya, kukane na ban hakuri, kukane na abubuwa da yawa. Ba zaice ga lokacin daya dauka a haka ba, amman bai dago ba sai da yaji zuciyar shi ta daina nauyin da take mishi tukunna ya dago yana kallonta, ita yau ta nemi inda hawaye suke ta rasa, da kansu sun san cewa yanayin da take ciki sun girme su.
"Bana cikin motar Ayya, ban shiga ba, bana ciki"
Sune kalaman da suka zo ma Bilal, kallon shi Ayya takeyi, kallon shi take saboda bata taba saka ran sake ganin shi ba, kallon shi takeyi kaunar shi da babu inda taje mata tana tasowa tana kuma shafe duk wani bangarori na zuciyar ta daya hakura da shi, bangarorin da sukayi jinyar rashin shi, hannuwan shi ta kama tana saka fuskarta a ciki hadi da sauke wata irin ajiyar zuciya da ta budewa hawayenta waje, wannan karin ita ta kwantar da kanta a jikin Bilal, kukan ta yana sake fito mishi da sababbin hawaye
"Kaga me kayi ko Bilal? Kaga me tafiyar ka tayi mana?"
Rayyan yake fadi yana kifta idanuwa saboda baya son ya fara kuka, yanajin su duka ba kuka sukeyi ba, idan ya fara ba zaiji lallashi ba
"Daada"
Nur da ta fito ta kira Rayyan din, da gudu take tahowa tana saka zuciyar shi mantawa da komai da yake faruwa saboda yanda take dokawa da tsoron karta fadi, bai sami natsuwa ba sai da yaga ta zagayo ta kama kafafuwan shi kamar ta dade bata gan shi ba, ko daki ya shiga tana wani dakin, idan ya fito haka take barin duk abinda takeyi ta tashi ta rugo ta rike shi kamar yayi wata tafiya mai nisa, sai yaji ta nutsar da shi, ta saka zuciyar shi wani irin sanyi. Ganin ta dago daga jikin shi tana kallon Bilal yasa shi kallon Bilal din shima. Sosai Nur take kallon Bilal kamar ta san shi. Abinda kafin psychology yayi mishi bayanin shi yake ganin tsakanin Ayya da Bilal, tsakaninta da sauran yan gidan shi yake gani tsakanin Nur da Bilal da har lokacin baima kula da ita ba.
Hankalin shi gabaki daya yana kan Ayya da ta dago tana saka hannunta ta goge fuskarta da shi. Shima Bilal tashi fuskar yake gogewa, hakuri yake so ya bata, amman kalaman sunki fitowa. Ko da Nur bata kai haka ba, sam yarinyar batayi qwiya ba, kowa ya dauketa zuwa takeyi, gashi bata tsoron mutane, kawai magana ce batayi sosai
"Yarinyar nan ko dai kurma ce Hamma?"
Layla ta tambaye shi, yayi dariya sosai ranar, har yanzun ko shi kadai ya tuna sai yayi dariya
"Allah da gaske nakeyi fa, ko irin wakar nan ta yara Nur batayi sam, in ba kuka take ba bakajin sautin komai"
Kai kawai ya girgiza saboda dariya da ta hana shi magana, shi yanajin wakar da take magana, ba ko yaushe ba, haka ta dade bata fara magana ba, da ta fara din ma ba sosai ba, duk rashin surutun shi yana iya ba Nur labari har ya gama yanayin fuskarta ne kawai zai nuna tana jin shi, ko in abin amsawa ne ta daga mishi kai. Ko kayan wasa tafi son wanda suke kamar bulalluka tayi ta hadawa, sai kuma puzzle da zata zazzage ta yini tana shiryawa, shisa yanzun ma baya tarkato mata komai sai kalaluwan su. Yar tsana da teddy duk inda ka ajiye nan zaka dawo ka dauka, bata so, in ya tare mata hanya zata dauka tayi cilli da shi gefe.
Yanzun ma Rayyan ta kalla, kamar tana son ya bata izini ne bai fahimta ba, ya dai daga mata kai, sannan ta juya, hannunta daya rike da rigar Rayyan, dayan kuma mika shi tayi tana bubbuga bayan Bilal da yana juyowa ta kara matsawa tana shigewa jikin Rayyan, kallonta Bilal yakeyi, itama kallon shi takeyi. Zuciyar shi ta gama shan duk wani mamaki na duniya, watakila shisa yaji ta natsu waje daya yanzun. Rayyan ya kalla yana neman tabbaci,kai Rayyan ya daga mishi
"Maimunatu... Nur"
Rayyan ya furta a hankali, yaso ya dora da
"Bamu ka dai ka bari ba har da ita, ka rasa abubuwa da yawa Bilal"
Amman sai ya kasa, yanayin da yake fuskar Bilal din ya saka shi ya kasa cewa komai. Nur ya rankwafa ya dauka yana sabata a kafadar shi ya raba su ya wuce, cikin dakin ya shiga sosai ya samu kujera ya zauna tare da Nur a jikin shi. Banda Huda data bar falon, daga Ayya har Bilal nan inda suke suka zauna, da alama babu wanda ya iya motsa. Rayyan bai musu magana ba, asalima Nur ya tashi yabi da taja hannun shi, mangwaronta ta dauko ya kamata zuwa kitchen ya wanke ya dauki wuka da filet, yayyanka mata yayi ya bata ta fita falo taje ta zauna.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.