Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 99 of 125
Baiji wani ya amsa shi ba, ya dai ji lokacin da Haris din ya bude murfin motar a bangaren da yake. Ya kuma ji hannun Haris ya kama na shi yana janyo shi ya fito da shi daga motar
"Rayyan... Rayyan"
Haris yake kira, amman baya ganin komai, ba shi da kalma ta hausa da zai misalta ganin shi da ita, abinda bature ke kira da "Blank" shine abinda yake faruwa da ganin shi. Yasan akwai mutane a zagaye da shi, amman baya ganin su, jin su kawai yakeyi. Da duk dakika kara jinsu yake, kukan su da maganganun su da yake tabbatar mishi da kalaman da yaji dai-dai ne, Bilal ya rasu, Bilal ya bar shi, ya mishi nisan da bashi da tabbas akan ranar da zai kamo shi
"Rayyan..."
Ya sake jin muryar Haris wannan karin yana jijjiga shi, iska yake nema, ko yayane ya samu ta isa cikin kwakwalwar shi, watakila ganin shi ya dawo, watakila ya daina jin duniyar na katantanwa da shi. Idanuwan shi ya lumshe yana jin wani shiru a cikin kunnuwan shi, kafin tunanin shi ya dauke gabaki daya.
BAYAN KWANA UKU
Hannun shi yake ji kamar a daure, yayi kokarin motsa shi amman bayajin karfi ko kadan a jikin shi balle ya iya motsawa, idanuwan shi ma ya dauki wasu dakika yana kokarin motsa su cikin son ya bude su kafin ya samu nasarar yin hakan, wani haske da yaji yayi mishi yawa na saka shi mayar da su ya rufe gam saboda kan shi da ya fara sarawa, sake gwada bude idanuwan na shi yayi, yanayin dakin ya fara karewa kallo, yana kokarin fahimtar inda yake, kafin yabi hannun shi da kallo, karin ruwa ne a jiki
"Rayyan..."
Yaji wata murya da bai taba sanin ta ba ta kira shi, a hankali ya juya kan shi yana kallon mutumin da kayan jikin shi yasa shi gane likita ne, kafin ya tabbatar da a asibiti yake, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su da tunanin me yake yi a asibiti, sake runtsa idanuwan shi yayi, komai na dawo mishi kamar shirin film kafin ya bude su yana wata irin mikewa, likitan ya dafa shi
"Akwai karin ruwa a jikin ka, kabi a hankali"
Hannun likitan da yake kafadarshi ya ture, yana jin makoshin shi kamar sahara ce a ciki saboda bushewa, karin ruwan da yake jikin shi ya fisge yana sauko da kafafuwan shi kasa, maganar da ta daina karasawa kunnuwan shi ita likitan yakeyi, da ya saka kafafuwan na shi a kasa ya taka sai yaji kamar sunyi mishi sanyi, kamar yayi kwanaki bai taka su ba, shigowar Haris da ya fita siyo wata allura ya saka shi daga kai ya kalli Haris din da yaga kamar ya rame
"Hamma mu tafi gida"
Da alamun gajiya a tattare da Haris din yace
"Yanzun ka tashi Rayyyan, dan Allah kayi hakuri ka kara warwarewa tukunna, kaji..."
Kai Rayyan yake girgizawa tunda Haris ya fara magana, ba zai zauna ba shi kam, yana son ya ga Ayya, yana son ganin Abbu, da dukkan zuciyar shi yake jin son ganin iyayen na shi kafin ya bude zuciyar shi da koma menene yake ji
"Dan Allah Hamma, rokon ka nakeyi, ka kaini wajen Ayya"
Kai Haris ya jinjina mishi, bashi da karfin yin gardama da Rayyan. A kwanakin nan ukku shi kadai yasan kalar tashin hankalin da ya gani.
"Ka zauna in zo to"
Wannan karin Rayyan baiyi musu ba ya koma ya zauna kan gadon. Da ido Haris yayi wa likitan nuni da su dan fita. Dakyar ya samu ya yarda su tafi da Rayyan din, dan likitan na tsoron yanda jinin Rayyan din ya hau, idan ya sake faduwa zai samu babbar matsala. Sai da Haris yayi ma likitan alkawarin zasu dawo sannan. Duk yanda Rayyan yaso yin musu da Haris ya kama hannun shi yana dorawa a kafadar shi saiya kasa, bashi da karfi ko kadan. Suna fita daga dakin Haris ya cire takalman kafar shi yana sa kafar shi daya ya tura su saitin Rayyan din da yaji wani abu ya tsaya mishi a wuya.
Saka takalman yayi, shi Haris din na takawa a haka har suka fita daga asibitin zuwa inda motar shi take, sai da ya taimakawa Rayyan ya shiga sannan ya zagaya ya shiga shima. Gida suka nufa, wannan karin ma sai da Haris ya taimaka mishi suka fita daga motar. Sai Rayyan din yake ganin kamar gidan ya canza, saboda akwai mutane a harabar gidan, an kafa rumfuna, ganin su na kara gudun bugun zuciyar shi. Yana jin Haris yayi musu sallama wasu na furta
"Ya karin hakuri?"
Yana amsa su da
"Mungode Allah"
Ya ja Rayyan din suka wuce, har dakin Ayya, nan ma akwai mutane, bai damu da su ba, idanuwan shi Ayya suke nema, harya hangota a zaune da hijabi a jikinta, zame jikin shi yayi daga na Haris da yake rike da shi
"Rayyan..."
Batare da ya kalli Haris ba yace
"Zan iya"
Tsaye Haris din yayi yana kallon Rayyan ya taka ya karasa inda Ayya take zaune yana tsugunnawa a gabanta
"Ayya"
Ya kira, sai lokacin ta kalle shi, idanuwanta duk sun kankance
"Rayyan..."
Ta furta, yanda muryarta ta karye na tabbatar mishi da abinda yake son ji, dakyar ya dafa kasa yana mikewa, batayi kokarin hana shi ba harya bar dakin. Wuce Haris daya bi bayan shi yayi, bango yake dafawa yana tafiya saboda rashin karfin da yake ji, dakin su ya nufa yana kama kofar ya bude ya shiga, jin Haris a bayan shi ya saka shi juyawa
"Dan Allah Hamma, ina son zama ni ka dai ne... Dan Allah"
Sai da Haris ya sauke numfashi tukunna ya dan daga kai, su duk sunyi kukan su, ciwon bai fara rage musu ba, amman sun yarda da cewa Allah da ya basu Bilal ya karbi abin shi, Rayyan na bukatar lokaci yaji mutuwar shima, ya yarda da sun rasa Bilal, ya rasa Bilal. Shisa ya juya, anan inda yake tsaye Rayyan ya durkushe yana zama da gwiyoyin shi a kasa, zafin kirjin shi yakeyi, kamar an tura mishi wani abu a ciki haka yake ji, idanuwan shi ya lumshe
"Ya rasu Maimuna... Bilal ya rasu"
Kalaman Abbu suka dawo mishi, wani irin numfashi yake fisga kamar rayuwar duka na barin shi, sunan Allah yake son kira ko zai samu sauki amman ya kasa motsa labban shi, hade kan shi yayi da jikin shi saboda kirjin shi da yake zafi, kafin yaji an dago shi
"Rayyan"
Yaji muryar Abbu da ta saka shi dora kan shi a jikin Abbun
"Kayi hakuri Rayyan, hakuri zamuyi, bamu da wani zabi daya wuce duk muyi hakuri"
Kai Rayyan yake girgizawa Abbu, kalaman Abbu din na saka wasu irin hawaye masu zafin gaske zubo mishi. Da komai na jikin shi yake son yarda da mutuwar Bilal
"Kun ga gawar? Kun binne shi Abbu?"
Ya bukata wasu hawayen na zubo mishi, yana jin hannuwan Abbu a jikin shi kamar wata fanka da take fifita mishi ciwukan da ke mishi azabar ciwo
"Bamu gani ba, baya nufin bai rasu ba, naga motar, munje ni da Yaya Ayuba, babu wanda ya fita a motar Rayyan... Kuma Bilal ita ya shiga... Kayi hakuri dan Allah, kayi hakuri"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.