Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 15 of 125

"Ahmadi da gaske nakeyi ba zan zauna da ita ba. Dan Allah to ka raba mana gida"

Ta karasa hawaye na zubo mata

"Ke kinsan ko ina da hali ba zan raba muku gida ba saboda banason zumuncin yarana ya samu tangarda, balle kuma bani da wannan halin..."

Mikewa Maimuna tayi, hawaye takeyi sosai, ta kowacce fuska Maryama ta zame mata bala'i.

"Ni kam zan bar muku gidan, sai ku zauna. A banza ba za'a zo a lashe mun kurwa ba wallahi"

Gyara zaman shi Ahmadi yayi baice mata komai ba, rigima take nema sosai. Ya rigada ya gama magana, ba zai biye mata ba. Kamar yanda yace Layla kama zama daram a cikin gidan. In tayi rikicin ta gama taga da gaske yakeyi zata hakura. Yana nan zaune yaga ta fito da jaka ta saka mayafi

"Ina zakije?"

Sai da ta share kwallar da ta zubo mata sannan tace mishi

"Gidan mu"

Yasan ba lokacin da ya kamata yayi dariya bane, amman dariyar ce ta kubce mishi, da kuruciyar su ma, duk fadan da takeyi dashi batace zatayi yaji ba sai yanzun da girma yazo musu, dariya yakeyi sosai da ta kara sosa ranta, wato bai damu ba, bai kuma dauki abinda takeyi din da wani girma ba

"Tunda kaga mahaukaciya dole kayi dariya Ahmadi..."

Ta karasa maganar cikin kuka tana daukar yar jakar da ita kanta batasan me da me ta zuba a ciki ba. Tasan idan akace ta bar gidan Ahmadi da sunan yaji ba zata iya ba, tunda ta aure shi, rasuwar Audu ne tayi kwanaki har bakwai batare da shi ba, kuma ko a cikin jimami na rashi, kewar shi na nukurkusarta. Yanzun ma tayi ne kawai dan ta razana shi, ganin kukan da takeyi yasa Ahmadi tashi, amman har lokacin murmushine a fuskar shi, jakar yake kokarin kwacewa ta janye, ya kama hannunta duk kokarin kwacewa da takeyi ya karbi jakar, da kanshi ya kama mayafinta yana cirewa

"Ke yanzun da girman ki sai kiyi yaji? Kuma ina zakije ki barni? Ko bakisan Maimuna ce jigon rayuwar Ahmadi bane?"

Wasu hawayen ne suka kara zubo mata, tana tsinewa ranar da Maryama ta dora idanuwanta akan Ahmadi har taji ya kwanta mata, tasata raba wannan soyayyar tashi da ita, shisa bata ga ranar da zata wayi gari da son matar nan ko kankani a zuciyarta ba.

"Ni ba zan zauna da yarinyar nan a gida daya ba, ba zan zauna ba. Kabarni in tafi tunda su ka zaba a kaina. Ka nuna mun yanda banda wani muhimmanci a wajen ka"

Kamata yayi suka zauna, kalaman da yasan da wahala taki yin laushi yake amfani dasu wajen tausarta, tasan yasan cewa shi dinne rauninta, soyayyar shi ita ce rauninta

"Idan ta lashe mun yara fa?"

Tayi maganar da wani irin sanyi murya dan gabaki daya ya gama kashe mata jiki

"Ba zatayi ba, ki yarda dani mana...alfarma nake roko a wajenki Maimuna, ko saina tsugunna..."

Ahmadi ya karasa maganar yana kokarin sauka daga kujerar, da sauri ta riko hannun shi tana girgiza mishi kai, murmushi yayi mata

"Nagode... Dan Allah karki takali Maryama da maganar nan, alfarma dana roka ta hada da wannan, wallahi badan Bilal ta kawo Layla ba, itama da nata dalilin kamar yanda kike da shi"

Taji shi, amman ita tasan gasa Maeyama takeyi da ita, tunda ta kawo Bilal gidan take bakin ciki, shine sai da itama ta nemo wannan mayyar ta kawo, kowa na da yara da kuma dan riko kenan a cikin gidan.

"Kinga daman bata da mace ko..."

Ahmadi ya fara, wani irin kallo da Maimuna ta watsa mishi yana saka shi yin dariya yana daga hannuwan shi ya hadesu waje daya cikin sigar ban hakuri

"Ka tashi ka tafi wajenta idan kewarta ce tasa kake son yimun hirarta a daki..."

Maimuna ta fadi wani irin kishi na taso mata, tashin yayi niyya tunda daman ya jimane haka saboda yana so ya fada mata zancen Layla. Amman maganar da tayi tasa shi yanke hukunci kara zama, yasan ana gab da kiran isha'i, sai yayi amfani da wannan damar ya fice gabaki daya. Maimunar tashi ta zama a lallaba, rikicinta sai shi.

*

Ba ko yaushe yake zama gidan Yaya Ayuba ba, ko da kuwa duka yaran gidan suna can. Lokutta da dama dawowa yake yai kwanciyar shi a daki, yasan ko Ayya tana tunanin yana can wani lokacin. Haka yakan haramtawa Bilal zaman ko da yana so, shi dai da bakin shi baya ce mishi ya taso su taho tare, idan ya taso din kuma baya hana shi biyo shi. Yau baima kula da ya dawo gida ba, zane yake sonyi, haka kawai tunda ya fara rike fensiri, tun ma kafin Abbu ya saka su makaranta zaiyi zane akan duk wani abu da zai samu. Ganin ko gawayi ya tsinto yana musu zane a jikin bango yasa Abbu din kwaso mishi litattafan da zai dingayi a kai.

Yanzun ma gara yayi zanen shi, ko fada sukeyi idan aka rabasu akan takardun zanen shi yake huce haushin shi har sai yaji zuciyar shi tayi sanyi. Ba kasafai yake ganin kyawun abinda yake zanawa din da baya wuce mutane, dabbobi, kwari, ko duk wani abu da yake so ya zana din, amman sai ayita cewa yayi kyau

"Allah yayi riko da hannayenka Rayyan, watakila kai kuma abincin ka a zane yake"

Abbu ya fadi kwanakin baya, baigane asalin ma'anar kalaman ba, ya dai amsa da Amin ne kawai. Ya fara zanen yaji yunwa na naniqar shi, sai ya tuna fada yayi a makaranta bayan sun tashi, daya dawo baibi takan abinci ba. Tashi yayi ya fita daga dakin yana nufar kitchen, yasan inda Ayya take ajiye musu abincin su shida Bilal, nashi ya dauko da cokali, yana dawowa dakin ya samu Layla a ciki, hannunta rike da fensirin zanen shi, dayan rike da takardar da yai kwana biyu yana aiki a kanta, a karo na farko da yaso gwada zana wani a cikin gidan, ya kuma zabi daya fara da Bilal, ta dakuna takardar, tana kuma kokarin kara bi da fensirin a kai.

Kwata-kwata tun ranar daya sauke idanuwan shi kan yarinyar batayi mishi ba, bayason mage, basu da ita a gidan su, akwai a gidan Yaya Ayuba, kuma in dai zai shiga gidan zasu dauke dan ansan tsoron ta yake, a cewar Hajja Mama, matar Baffa kamar yanda suke kiran Yaya Ayuba din, tun yana yaro bayason mage, da ya gani kamar zai shide, shisa bayason Layla, idanuwanta na mishi kama dana jaririn magen gidan Baffa daya gani. Gashi duk inda yayi cikin gidan sai yaga kamar tana bin shine, lokutta da dama Haris ke zuwa yayi sauri yaja hannunta dan kamar shi kadai ya kula da bayason yarinyar na zuwa kusa da shi.

Kuma akan kunnen shi rannan yaji Ayya tace mayya ce, baiyi mamaki ba. Tunda itace mutum ta farko daya taba gani da kalar wannan idanuwan, da gaske mayyar ce, shisa duk inda yabi cikin gidan sai ya ganta. Yar kular abincin ya ajiye a gefe yana karasawa cikin dakin, fensirin ya fara fisgewa daga hannun ta, kafin ya fara kokarin karbar takardar da take rike da ita, bayason yasa karfi ya karba, kamar yanda da dukkan zuciyar shi bayason ko yaya ne jikin shi ya hadu da nata, dan a tsorace yake, kokari yakeyi na ganin bai kalli fuskarta ba

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.