Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 71 of 125

"Kuma yanzun Maryama tabar nan, tace bata samu Layla a waya ba"

Wannan karin da kallon da yake mata hade yake da mamaki, duk da batun yanzun yasan akan yaran su Ayya zata iya ajiye duk wani tashin hankali a gefe ba, yaji dadi, sosai yaji dadi har cikin ran shi

"Ki kwantar da hankali, in shaa Allah nasan lafiya. Yanzun haka wayoyin suka kai wani waje... Idan har zuwa anjima ba'a samu ba, gobe da safe sai in kira aje a duba su, kinga yanzun ba zaka kure mutane cikin daren nan ba dan suna jin kunyar ka"

Kai Ayya ta jinjina mishi, duk da haka sai da ya kara zama a wajen nata ya tabbata ya ga murmushi a fuskarta sannan. Yana fita daga dakin nata wayar shi ya zaro yana kiran abokin shi da yake Zaria, amman bai daga ba, bayason ya karasa rikita Ayya, amman akan yaran shi ya fisu rauni, sosai zuciyar shi take bugawa, yunwar da ya yini da ita ta dauke daf, dakin shi ya nufa inda ya sami Mami ta shirya mishi abinci, shigowar da tayi yasa shi daukar plate, da kanta ta karasa ta zuba mishi abincin, yasan bataci ba shisa ya saka cokulla biyu, batayi mishi gardama ba, haka suka dinga tura abincin ba dan yana musu dadi ba.

"In shaa Allah babu wani abu, da yardar Allah lafiyar su kalau"

Kai kawai Mami ta iya daga mishi, amman yanayin jikinta yana kara tabbatar mata da babu lafiya, kawai addu'a takeyi a zuciyarta. Abbu ma haka, daren duka ukkun cikin wani irin yanayi sukayi shi, kowa da abinda yake tunani.

*

Tabbas yara raunin iyaye
Yara karfin gwiwar iyaye
Yara kwanciyar hankali da natsuwar iyaye
Yara tashin hankali da firgicin iyaye.

Allah ya bawa dukkan iyaye karfin zuciyar kaddarar da zata gifta ta kan yaran su.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: 13 Dec, 2020

(An kirkiri Airport a Zaria domin tafiyar labari badan akwai ba)

20

Lokaci zuwa lokaci wanda yake kujerar kusa da shi a cikin jirgin yakan ja karamin tsaki saboda yanda Rayyan din yake bubbuga kafar shi a kasa cikin kosawa. Gani yake kamar jirgin baya sauri, baisan menene a nannade tare da harshen Bappa da kalaman shi ba, amman sunyi tasirin da suka saka shi daukar shawarar shi na tsayawa yayi abinda ya kaishi Bauchi ya wuce wajen, sai su duba idan akwai jirgin da zai tashi daga Bauchi zuwa Zaria, da yake a yar jakar shi duka katikan shaidar shi suna ciki, na makaranta, katin zabe da kuma katin shaidar dan kasa. Bappa na dubawa kuwa yayi nasarar ganin akwai jirgin da zai tashi karfe biyar da rabi na ranar.

Har suka gama abinda sukeyi a camp wajen azahar suka dawo hotel room din Rayyan bai daina mamakin yanda akayi Bappa ya saka shi zama a Bauchi har wannan lokacin ba, saboda gabaki daya hankalin shi yayi Zaria. Bai sake gwada kiran lambobin su Bilal ba duk ranar, wayar shi dai tana hannun shi, yana gudun kar ya sakata ko da a aljihune wani a cikin su ya kira ya zamana bai samu ba. Har airport din ma Bappa ne ya raka shi, a hanya ya tsaya ya sai mishi strawberry yoghurt, da yake yana da sauran biskit a jaka saiya hada ya dan sakama cikin shi, jiri har dibar shi yake idan ya mike, kuma yasan yunwa ce.

Bappa ya zauna da shi har sai da lokacin tantancewa yayi sannan suka mike a tare

"Nagode... Nagode sosai"

Rayyan ya tsinci kan shi da furtawa, saboda shine kalaman da zai iya fitowa da su da kalar karamcin da Bappa yayi mishi. Kai kawai ya jinjina ya furta

"Sai munyi waya"

Shima na shi kan ya jinjinawa Bappa, bai tabayin aboki ba balle ya san yanda yake. Amman yanajin da rayuwa ta hada shi da Bappa da wuri, watakila da sun zama abokai. Bayason mutane, amman Bappa yana mishi daban, ba shi da lokacin tunani akan abin saboda su Bilal da suka kara taso mishi suna danne duk wani kwanciyar hankali da yake tare da ita. Da su a manne cikin kan shi suka sauka garin Zaria. Kafafuwan shi kamar basa mishi saurin da ya kamata yau haka yake ji lokacin daya karasa bakin titi da yake da yar tafiya daga cikin airport din. Mashin ya samu zuwa gida

"Dari biyar"

Mai mashin din ya fadi, kai kawai ya daga mishi yana hawa

"Kayi sauri dan Allah"

Rayyan yayi maganar da wani irin yanayi a muryar shi, har sai da mai mashin din ya dan duba ta mudubi ko zai ga Rayyan din da kyau, ko a cikin abokai lokacin daya fara koyon tuqin mashin din "Dan asabe ganganci" ne lakabin shi, yanzun ma sunan Dan Asabe ya bace sai ganganci din, yanda yake jan mashin idan yana tuqi kowa mamakin samun kwastomas din shi yakeyi. Musamman idan ya busa hayaqin wiwi din shi, bakin shi babu hakora wajen biyar saboda hatsarin da yakan yawaita samu. Tabbas yau ko labari yaje ya bayar na cewa wani ya nemi ya kara gudu da shi a mashin babu wanda zai yarda.

Daman ance in da ranka zaka sha kallo, yau ya dauko mahaukaci. Sai yake jin shi a tsorace da Rayyan din, wani mahaukacin tas zaka gan shi, saika saki jiki kaji saukar duka. Haka suka lallaba harya sauke shi. Kafafuwan Rayyan din yaji suna mishi rawa, kamar suna son ce mishi ba zasu iya karasawa da shi cikin gidan ba. Zuciyar shi bata kara gudu ba sai da ya karasa tsakar gidan, har wani numfashin tashin hankali yake fitarwa, dakyar ya karasa dakin su yana ganin kofar a ture, daga hannu yayi cikin tunanin ya kwankwasa ko ya tura, ko kuma ya gwada saka mukulli. Karshe ya tsaya kan shawarar turawa, yaga dakin ya bude, duk da gidan akwai hasken wutar lantarki, dan ga mutanen cikin gidan nan sunata shige da fice, dan ko sun mishi magana ma bai kula da su ba.

Yana tura dakin ya ga duhu, makoshin shi ya bushe kamar an zuba ya shi, switch ya laluba ya kunna, duk yanda ya sha cin karo da tsayuwar bugun zuciya a karance da kuma a videos bai taba tunanin haka abin yake ba sai yanzun da ganin Bilal a kwance a kasa kamar gawa ya saka tashi zuciyar tsaya na dakika kafin ta soma aiki tana wata irin bugawa, wannan karin kafafuwan shi duka sunyi sanyi, gwiwoyin shi kamar an buge su da guduma haka yake ji, kasa yayi gabaki dayan shi. Da rarrafe ya karasa inda Bilal din yake yana dora hannun shi a jikin Bilal din

"Bi.. Bilal..."

Rayyan ya kira cikin rawar murya, tashin hankalin shi na karuwa, dan gani yayi kamar Bilal din ya rabe mishi gida biyu, idan zuciyar shi bata daina gudu ba yana gab da sumewa, dakyar ya iya birkito Bilal yana dora hannun shi kan kirjin Bilal din inda yaji zuciyar shi na dokawa a hankali a hankali cikin yanayin daya fara nutsar da na shi bugun zuciyar.

"Bilal..."

Ya sake kira can kasan makoshi, Bilal din da yake jin shi a wata duniya yana bude idanuwan shi dakyar kafin ya sake mayar da su ya rufe. Tun jiya yake nan kwance, dakyar yaja jikin shi da safiyar yau din ya shiga bandaki, daya fito ma jiri ya dinga dibar shi har ya karasa daki, towel din shi na wanka ya ajiye a kasa ya dauki ruwa yai alwalar asuba a kai, dakyar yayi sallah sabo da ciwon kan da yake fama da shi ko numfashi dakyar yake fitarwa, sanyi yakeji, amman ya mika hannu ya janyo bargo ya kasa, anan yake kwance tun safiyar yana jiran ikon Allah ya cika a kan shi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.