Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 79 of 125
Tun kafin ya fada mata yasan ita din tashi ce, idan bata rike hannun shi yanzun ba, zata rike nan gaba. Abu daya ya sani, hannun shine na farko kuma na karshe da zata taba rikewa a rayuwarta. Yana da wani irin kishi da akanta ne ya fahimci hakan, musamman yanzun, ko ganinta yaje yi duk idan zai tafi sai yace mata
"Bana son kowa a kusa da ke kin sani ko?"
Dariya takan yi ta daga mishi kai, haka kawai saboda ita yakan shiga cikin makaranta, murmushi yakan bata a matsayin tukwici saboda yanayin shigar da takeyi yanzun, abaya take dorawa akan kayanta, wasu ranakun ma hijabi take sakawa, tana mishi kyau naban mamaki, hakan dai bai hana shi jin wani zafi a kirjin shi ba, duk idan yaga tana magana da wani dan ajin su, bayason ganin kowa a kusa da ita. Har ran shi baya so, ya fara kirga kwanakin da suke cikin shekara biyu da kusan rabi daya rage mata a ABU.
Jiyama tun da akayi Magriba yana wajenta sun sami waje sun zauna, ba wani hira suke ba tunda ta bashi labarin jarabawarta, da wani yaro da aka kama yana satar amsa. Da akayi isha'i dai ita ta koma cikin hostel shikuma yaje masallacin yayi sallah. Suka kara dawowa, shine ma yace mata
"Gobe da safe zan tafi In shaa Allah...Bilal zai kaini"
Shiru ta danyi na wasu dakika
"Sai yaushe zan gan ka?"
Numfasawa yayi, goben zai kama lahadi
"Zan shigo nan da sati daya in shaa Allah..."
Kallon shi Layla tayi, ya girgiza mata kai
"Kar kimun kuka Layla, idan zan iya zuwa a wasu ranakun da ba karshen mako ba zan zo"
Muryarta a shagwabe tace
"Ba zan gan ka ba, mun gama jarabawa, na tafi gida sannan"
Ta karasa maganar da wani irin yanayi
"Zan zo gida... Bance nan da satin ba, amman zan zo in gan ki"
Numfashi ta sauke
"Ka siyi waya Hamma"
Zuciyar shi yaji ta doka, kamar ya dora hannun shi a kirji karta fito waje, saboda sai da ta saka idanuwanta cikin na shi tukunna tayi maganar
"Ina da waya"
Ya amsa yana dauke idanuwan shi daga cikin nata
"Wannan ba waya bace ba, calculator ce kake da Hamma"
Ta karasa tana dariya, rankwashinta yaje yi ta kauce tana sakeyin dariya
"Waya nake nufi, waya irin ta kowa da kowa"
Kafadu yadan daga
"Ni ki barni"
Gyara zamanta tayi tana fuskantar shi
"Dan Allah Hamma, zamu dinga chatting, ko bamuyi ba zan kiraka video call in gan ka idan baka zo ba"
Shiru yayi yana jinta
"Kaji... Dan Allah"
Shirun dai ya sakeyi yana kauda kan shi gefe, bata gaji ba ta tashi ta same shi ta dayan gefen tana fadin
"Ka siyi babbar waya Hamma"
Numfashi Rayyan ya sauke
"Ni ki barni, bani da kudi"
Da sauri ta amsa
"Ni ina da kudi sai in baka"
Murmushi yayi yana mikewa saboda dare ya fara yi, kuma yanzun Bilal na ran shi ko da yaushe, basu ci abinci ba ya fito, bayaso ya koma ya samu Bilal yayi bacci, ba zai iya tashin shi ba, ba kuma yaso ya kwanta baici abinci ba.
"Allah ina da kudi, Abbu ya sake turamun, kuma kaga bamuci abinci a waje ba sosai, dafawa mukeyi ni da Anisa. Ka bani account number dinka sai in maka transfer"
Wannan karin ya rankwasheta, ta dafe wajen tana murzawa
"Na fasa baka Hamma"
Tace tana murza wajen sosai, murmushin ya sakeyi
"Dan Allah ka siya"
Numfashi ya sauke yana furta
"Mayya..."
Dariya kawai tayi, harya rakata tana mishi magiyar ya siyi waya. Kuma da tunanin ya tashi yau da safe, har yana gama shirin shi. Baima san wacce zai siya ba idan ya tashi, ko kuma nawa kudaden su suke, da gaske bashi da kudi, Abbu yana tura mishi duk wata, ko da ya gama makaranta, Abbu kuma ya sani bai daina tura mishi kudin ba, ya dai rage yawan su, rabin abinda yake bashi ne da yana makaranta. Yana so ma yace daga watan nan kar Abbun ya sake turawa saboda shima zai fara samun kudi, ga na bautar kasa da za'a fara bashi, ga kuma Bappa da yayi mishi text ya fada mishi in da zaiyi bautar kasar suna biyan kudi suma.
Bai dai san yanda zai fadama Abbu haka ba, ko yayi mishi text yake tunani, abinda zai fada din ma yana mishi wahala gabaki daya
"Na wa waya?"
Ya tambaya, yana saka Bilal da yake shiryawa kallon shi
"Waya irin taka, ko ta Layla haka, waya dai da akeyin chatting, nawa?"
Murmushi Bilal yayi, saboda yanayin yanda Rayyan din yayi tambayar, ya kwana biyu baiyi murmushin daya fito tun daga zuciyar shi ba haka
"Wacce iri?"
Kai Rayyan ya rausayar
"Shisa nake tambayar ka, ban sani ba"
Maballin rigar shi Bilal ya karasa ballewa
"Akwai har ta dubu tamanin"
Wani irin kallo Rayyan yayi mishi da ya sa shi kwashewa da dariya, sai yake jin kamar wani abu da yayi duhu a cikin kirjin shi ya dan washe da dariyar da yayi
"Baka da hankali ashe Bilal? Dubu tamanin ka sa ka siyi waya? Ai kam saina fadama Ayyar ka"
Sosai Bilal yake dariya, a tsayin zaman su da Rayyan, yaune karo na farko da yayi barazanar kai karar shi. Yanda yayi maganar kuma kamar har ran shi zai fadama Ayya cewa ya saka dubu tamanin ya siyi waya
"Ina ma ka sami kudi?"
Rayyan ya sake tambaya, dariyar da Bilal yake na son saka murmushi kwace mishi, yayi kewar ganin yanayin a tare da Bilal, yayi kewar ganin shi cikin raha, cikin farin ciki, da dariyar nan tashi da take hayaqa shi a lokutta da dama, saboda Bilal baisan sanda ya kamata ya daina dariya ba idan ya fara, amman yau idan zai wuni yana dariyar nan hakan zai so. Haka yake fata ya kasance, addu'ar shi kenan, yana kuma sake dora wata cikin rokon Allah ya sa damuwar Bilal din ta yaye kenan. Bai san me zai cigaba da fada ba, amman bayason wannan yanayin ya wuce
"Da gaske Ayya zan fadama tunda kai baka da hankali"
Jakar shi Bilal ya dauka yana saka cajar waya a ciki da dan abinda zai bukata, saboda yace zai kwana sai washegari ya dawo tunda har Monday din bashi da jarabawa. Watakila idan ya dan dagama Zaria yayi numfashi batare da nauyin da yake danne da kirjin shi ba
"Waye yace maka wayata dubu tamanin take? Tecno ce fa, waccen na bayar saina cika dubu sha biyu na dauki wannan"
Kai Rayyan ya jinjina
"Kamar irinta nawa?"
Dan jin Bilal yayi yana hada kudin da wayar ta tasar mishi a cikin kan shi, ko watanni biyu batayi ba
"Dubu talatin ko da biyar haka, ba zata wuce da takwas ba dai"
Hannu biyu Rayyan ya saka ya dafe duka kuncin shi, ba dariya yake so ya saka Bilal ba, har ran shi ya girgiza, mamaki yake yana kuma hasaso abinda zaiyi da dubu talatin da yafi siyan wata waya muhimmanci, ta hannun shi dubu biyar da dari ko biyune ya siyeta sabuwa fil a kwali. Kuma yana ganin abinda wayar su Bilal takeyi shima tashi zatayi
"La hawla wala quwwata ila billah..."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.