Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 44 of 125
"Banfa samu mashin har gidan nan ba, akan hanya napep ta ajiyeni, da kafata na shigo wajen nan..."
Dakin Rayyan ya bude saboda yanda zuciyar shi take dokawa ba zai rufe daki daga ita sai shi a ciki ba. Ya rasa lokacin da ganinta ya fara hargitsa tunanin shi har haka, kuma bai saka idanuwan shi cikin nata ba, ya koyi kallon har fuskarta batare da idanuwan shi sun shiga cikin nata ba
"In da na tashi nan zaki zauna?"
Ya bukata yana karasawa wajen ya rankwafa, hannunta ya kama ya fisga yana dagata
"Hamma dan Allah, wallahi nagaji, nagaji ni"
Hannun ya sake rikewa sosai
"Da daddare kika biyo hanya?"
Duk da ko fita kayi yanzun din za kaita cin karo da mutane, unguwar tasu dalibai sunfi yawa, dare sai kaga kamar rana ne, amman wani abu a zuciyar shi baison yanda ta fito da magriba haka
"Abinci zan kawo maka, ba kana azumi ba? Dan Allah ka sakeni"
Ta karasa muryarta na rawa, tun azahar yau ta gama darasinta, tana komawa hostel ta fara aikin yi mishi girkin nan saboda ta siyo kifine sai tayi mishi sauce ta dafa wake da shinkafa. Anisa da suke daki daya taso tayata, tunda wani lokaci har girki sukan hada, tace karta damu zatayi in yaso sai Anisa din tayi wanke-wanke. Ba tsafta bace bata da ita, kawai halin jujun Rayyan ta sani, zai iya tambaya idan ita kadai tayi girkin, kuma ba zata iya kallon shi tayi karya ba, yana ganeta, ta sha gwadawa bakinta yanayin jini
"Karya ne"
Yake fadi a duk lokuttan yana kara kai mata wani dukan, sakar mata hannu yayi yana komawa wajen shi ya zauna. Tsaye tayi a wajen tana murza hannunta, shikuma ita yake jira ta zuba mishi, hakan ta kula da shi, bata dauko faranti ba, a dakin ta samu da cokali, sai da ta dauki ruwan leda tana fita wajen dakin ta daurayo su sannan ta dawo
"Kazama, a bakin kofa kika zubar mun da ruwa ko?"
Bata kula shi ba, turo labbanta tayi kawai, sai lokacin ta cire hijabin da yake jikinta tana ajiyewa kan teburin da yake cikin dakin. Bai taba mata maganar kayan da take sakawa ba, amman tasan bayaso, har wata zuciyar na fada mata kishi yake shisa, ba karamin dadi take ji ba kuma. Jacket din shi guda hudune a wajenta yanzun, kuma duk idan ta saka kayan da baisone yake bata. Kamar yana yawo da jacket dinne yanzun ko zai ganta da kayan da bayaso, dan kwanaki a jakar shi ya fito da jacket din. Kuma Rayyan sam bai damu da yawan mutanen da suke waje ba idan ya tashi yi mata abu, kamar ma baya ganin su haka yakeyi.
Abincin ta zuba mishi tana neman waje ta zauna, ya fara ci yaga yanda take bin duk cokalin da zai kai a bakin shi da kallo, kai ya girgiza yana ajiye farantin da ya daga, ya gyara zaman shi sosai
"Me yasa zakiyi girki ba zakici ba?"
Tasan baya tambayeta dan ta bashi amsa bane, shisa tayi shiru, ita batama san tanajin yunwa haka ba sai yanzun da taga yana cin abincin. Cokali ya dauka yana mika mata, zata saka cikin abincin ya dakatar da ita da fadin
"An taba marin ki cikin ido? Ba zaki tashi ki wanko shi ba, kazama kawai"
Mikewa tayi tana daukar sauran ruwan da ta ajiye a gefe ta daurayo cokalin ta dawo. Tare suka cinye abincin tana kara zuba musu wani. Abin bai mata wani iri ba, zuwanta makarantar wannan ne karo na wajen biyar da suke cin abinci tare, na farkon ta kusan raba dare data juya yanayin su tare take hangowa sai wani murmushi ya kwace mata da ba zata ce ga dalilin shi ba. Da yake yana cin abinci da sauri, kafin taci guda daya yaci uku, baisan dalilin da zaisa ka tsaya yanga in zakaci abinci ba. Da kanshi ya dauki kular yana kara mata ya zuba mata miya a kai, abincin da yawa tayi.
Yasan Bilal in dai ba wani abu yaci a wajen Aysha ba, zaici, in baici ba da safe sai su dumama suci abinsu. Layla na karasawa, ruwa kawai ta sha, batama gama ba Rayyan ya mike
"Tashi muje"
Kallon shi tayi da tashin hankali a fuskata
"Ina zamu je? Hamma kabari abinci ya tsarga mun, yanzun fa nagama ci"
Kallon da yayi matane yasata mikewa ta dauki hijabinta tana buga kafarta, duka Rayyan ya kaimata tana kaucewa dan ta gan shi
"Zaki wuce ko saina kwada miki mari?"
Ya bukata, fita tayi daga dakin, shima takalmi ya zira a kafafuwan shi yana fita, baisan ko Bilal ya dauki mukulli ba, shisa ya janyo kofar kawai, gidan su ba'a taba yin sata ba. Kusan ko yaushe Bilal kan yabi halayyar yan gidan. Ko baka rufe daki ba, wani zai janyo maka. Haka sukeyi, in shanya kayi hadari ya hado ma za'a kwashe maka, inka dawo a kawo maka. Suna da kirki matuqa. Shisa bayajin dadin yanda Rayyan yake hade musu girar sama da ta kasa. Shiya fara yin gaba Layla na biye da shi, cikinta take ji har wuya, inda tasan ba zai bari abinci ya natsa mata ba, da bata cika cikinta haka ba.
Ganin har sun kai titi suna tsallakawa yasa ta fadin
"In mukai nisa fa ba zamu sama abin hawa ba"
Dan juyawa Rayyan yayi ya kalleta, hannunta yake shirin kamawa ta kauce
"A kafa? Hamma a kafa? Tafdin... In dai rakani zakayi nagode...amman ni wal..."
Da sauri yace
"Karma ki rantse, zakiyi azumi yarinya... Ki zo mu tafi"
A kafa yake jin tafiya, saboda yana son dan takawa tunda ya cika cikin shi, kuma ko ba haka ba, a ranshi yana jin yin tafiyar tare da ita, ko tana so ko bata so ba matsalar shi bane ba, duk yau ganinta ne yadan nutsar da shi, amman da wani kunci ya wuni, wasu ranakun idan yana azumin yakan ji shi wasai, har Qur'ani yakan dauka ya karanta. Amman wasu ranakun bawai bayaso ya dauka bane, kawai wata irin kasala kan rufe shi duk idan ya yunkura sai ya kasa, haka zai hakura yaita juyi, inya gaji ya kunna sigari ya bukama cikin shi.
"Ni dan Allah kabarni, wallahi nagaji, kuma na saka dogon takalmi"
Layla ta furta tana shirin yin kuka, tun kafin ta fito take murnar zuwa ta gan shi, amman yanzun harya isheta, ta ina zata fara shafawa a kafa ana zaune lafiya. Zagaye suka fara
"Layla..."
Ya furta cike da kashedin da yasata tsayawa waje daya, yasan ko bata zagin shi a ranta, tana tunanin hanyoyin da zata jibge shi idan ta samu dama ne saboda kallon da takeyi mishi, hasken wutar lantarki ya sake ma idanuwanta launi, sai da gabanshi ya fadi daya kalle su, musamman da irin kallon da take watsa mishi, hannunta ya damqa yana janta tana tirjewa kamar karamar yarinya. Bai damu ba, cigaba yayi da janta har suka karasa wani shago, yana rike da hannunta har lokacin ya siya silipas, babu karamar lamba, dan koshi sun mishi yawa, sakinta yayi ya fito dasu daga leda yana ajiye mata
"Ni ce zan saka wannan?"
Ta bukata tana ware mishi ido, kamar duk ranar bataga wani abu daya daga mata hankali irin shi ba, takalman kafafuwan shi dana fata ne yan zire ya cire yana saka silipas din
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.