Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 31 of 125
Numfashi ya sauke, gabaki daya ba yajin yana da natsuwar wata tafiya yau
"Ni kam sai gobe"
Baki Bilal ya bude yana kallon shi, so yake yaga ko dan murmushine a fuskar Rayyan din da zai nuna cewa wasa yake maganar da yayi, amman babu, da dukkan gaskiyar shi ya fadi
"Sai gobe? Kasan Hamma Haris na da abu mai muhimmanci da zaiyi goben ko?"
Cikin idanuwa Rayyan ya kalle shi
"Nace kar ya tafi ne? Ban tuna lokacin da nace wani a cikin ku ya jirani ba, kun tambaya na fada muku yau zan tafi. Yanzun kuma nace sai gobe, me yasa kake da matsala da hakan?"
Ba maganganun bane suka batawa Bilal rai, yanayin da Rayyan din yayi maganar, babu alamun bacin rai ko jin haushi, kamar yana ma karamin yaro bayani, saboda bai dauki abinda yayi a matsayin wani abu ba
"Hakane..."
Bilal ya furta yana juyawa, dan dakuna fuska Rayyan yayi dan yaga kamar ran Bilal din ya baci, bayan a duka maganganun da yayi bai ga abin bacin rai ba. Kiran sallar la'asar da yaji anyi yasa shi ficewa daga bangaren Mami, sai da yaje dakin shi ya daura alwala sannan ya fita masallaci. Yana dawowa kuma kan shi tsaye bangaren Mamin ya kara wucewa, sanda yaje a bandaki ya samu Layla ta tsugunna saboda aman da taji yana taso mata, kuma batama wani ci abinci ba balle tace
"Layla... Amai zakiyi? Amai kikayi?"
Rayyan ya fadi yana jin ruwan da yake takawa a bandakin saboda babu takalma a kafafuwan shi har cikin ran shi, amman wahalar da Layla take ciki tasa ko amsa ta kasa bashi, da kan shi ya tari ruwa a famfo yana janyo bokitin kusa da ita, kofin da yake ciki yai amfani da shi wajen zuba mata ruwa a hannuwanta da ta miko mishi ta wanke fuskarta, shi ya kama hannunta tana mikewa ta ficewa daga bandakin ta koma ta kwanta. A ran shi tunanin inda Mami taje tabarta ita kadai a halin da take ciki yakeyi, ran shi na kara baci.
"Ba dole kiyi rashin lafiya ba, ki kalli bandakin da kike shigowa dan Allah..."
Ya furta, duk da wani zai shiga yagan shi tsaf-tsaf, amman a idanuwan Rayyan yayi mishi datti. Omo daya gani ya dauka ya zuba a bokitin yana wanke bandakin, har karamin tawul din daya gani da baisan kona menene ba ya dauka ya goge bangon bandakin. Ko kadan bayason ganin datti, dan jirwayen ruwan da zaka gani na ruwan wanka a bandaki, na dakin su sam ba zaka gani ba, ya goge ko ina qal-qal. Sai da ya wanke kafafuwan shi sannan ya fito daga bandakin.
*
"Muje kawai Hamma... Barin wa Ayya sallama, idan mukai la'asar sai mu tafi"
Bilal ya fadi muryar shi a sanyaye, cike da rashin fahimta Haris yace
"Rayyan din fa"
Kallon shi Bilal yayi
"Yace sai gobe zai tafi, janyo shi zanyi?"
Murmushi Haris yayi, kafin Bilal din ya dan dafe kai yana fadin
"Kayi hakuri...Allah ya batamun rai ne"
Murmushin dai Haris ya sake fadadawa
"Rayyan manya... Allah ya shirya"
Bandakin su da yake cikin dakin Bilal ya shiga ya daura alwala ya fito
"Kaga ni ina da abinda zanyi a makaranta gobe da safe in shaa Allah. Amman ka jira Rayyan din sai ku taho tare"
Tun da ya fara magana Bilal yake girgiza mishi kai, ya taho shi kadai kamar yanda yake so. Da tun farko bai wahalar dasu ba yace shi kadai yake son tafiya.
"Ka bar shi Hamma... Da mun dawo sallah tafiya zamuyi..."
Kai Haris ya jinjina yana mikewa. Alwalar yayo shima suna fita masallaci tare, suna dawowa shi ya shiga dan ya fito da jakunkunan su da na Bilal ne guda biyu. Shi kayan shi basu da yawa, Rayyan kuwa jakar shi karama ce, babu abinda yake tafiya da shi. Daga gefen jakar takardun zanen shi ne daya nannade su ya soka. Shi kuma Bilal ya wuce bangaren Ayya inda ya tsaya daga bakin kofa yana fadin
"Ayya zamu wuce..."
A kasan murmushin alfaharin da tayi akwai damuwa shimfide, gidan har yayi mata wani irin shiru. Da Rayyan ya tafi daman ta saba, dan ko yana cikin gidan sai tayi kwana biyu bata saka shi a idanuwanta ba, amman Bilal, a duk cikin yaranta babu wanda ta shaku da shi kamar Bilal, banda Ahmadi shine namiji na biyu a rayuwarta da yake gane akwai damuwa a fuskarta tun kafin ta furta, yake zama har sai yaga tayi fara'a sannan. Bilal ne kuma ka dai yake dora bukatunta akan nashi. Ko bangaren ya zaba na karatun shi tasan saboda ita ne
"Wai duk cikin ku babu wanda naji yana sha'awar lissafi....ko yar kara ba zakuyi wa Abbun ku ba"
Ta fadi wani lokaci can baya, sosai Bilal yayi dariya, musamman da Zubaida tace
"Wallahi Ayya idan zaki tsareni bansan ya akayi na wuce lissafi a shekarar farko fa, kowa na kallona a matsayin yar Abbu a ajin, suna tunanin zan baro A, dakyar D ta fito..."
Nan aka bude caftar tattauna lissafi, shi bai taba bashi matsala ba, kuma Rayyan yana ganewa matuka, idan waje ya shige mishi duhu daya nunawa Rayyan din yake warware mishi
"Kina son wani ya karanci lissafi ne Ayya?"
Kai ta dan rausayar
"Naga wahala yake baku ai"
Murmushi kawai yayi, sai ranar daya amso takardar samun karbuwa a ABU ne ya nuna mata lissafine gurbin daya samu
"Bilal..."
Ta fadi tana jin kaunar shi har kasan zuciyar ta
"Ki mun addu'a kawai Ayya"
Shine abinda ya fadi, addu'a kam bata gajiyawa da yi musu ita. Tun da satin tafiyar tashi ya kama take jin yanda zatayi kewar shi. Ko na rana daya Bilal din bai taba zuwa wani waje ya kwana ba, yaran nata girma sukeyi a gaban idanuwanta, amman zuciyarta na kallon su yan kanana. A wajenta har karshen lokacin da Allah ya ara mata tare dasu ba zata daina ganin yarintar su ba.
"Allah ya tsare mun ku, Allah ya baku sa'a a karatun ku. Ka kula da Rayyan kamar yanda ka saba"
Ta karashe maganar da yanayi mai nauyi a muryarta
"Sai gobe shi, ya fasa tafiya yau"
Da mamaki Ayya take kallon Bilal
"Saboda me? Bashi ya zabi yau din ba"
Kallon 'Rayyan ne Ayya' Bilal din yayi mata
"Kawai ya fasa tafiya yau din ne"
Ita fa sam zaman shi a Zaria yanzun ya fiye mata zaman shi a garin Kano. Saboda zai nisanta shi da Mami da kuma Layla. Ko kadan bata kaunar ganin yana wata mu'amala da su
"Yana ina?"
Dan jim Bilal yayi, saboda bayason bata mata rai, yana da tabbacin idan ya fada mata Rayyan na dakin Mami ranta zai baci sosai. Amman a lokaci daya ba zai iya mata karya ba
"Yana wajen Layla ko?"
Ta tambaya zuciyarta na wani irin zogi, ta rasa ta inda zata fara bullowa al'amarin Rayyan. Shekaranjiya suna tare da Khadi da zuwanta aikin hajji shekaru bakwai da suka wuce yasa duk yan unguwa suna kiranta da Hajiya Dije. Taso tayi mata zancen Rayyan din dan tana da yakinin ba zata rasa shawarar da zata bata ba. Amman sai ta tsinci kanta dayin nauyin baki
"Bilal tambayar ka nakeyi"
Ayya ta fadi rai a bace, kai ya dan daga mata
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.