Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 125
Sai da akayi wajen kwanaki takwas tsakani sannan ta sami dalilin da tayi amfani dashi wajen fitar. Mamaki ta dingayi tana karawa, saboda karyayyun tsinkayen da Malam Mainasara ya batane ya juye cikin wani farin kyalle ya nannade, ya jujjuya a gaban idanuwansu ita da Khadi, ana bude kyallen saiga tsinke mike kyam kamar ba'a karya shi ba
"Ma shaa Allah, aiki yayi yanda ake so. An samu damar karya sihirin"
Farin ciki fal ranta, farin cikin da batayi wasu dakika tanayi ba, tsoro ya maye gurbin shi, jin Khadi tace
"Saura raba soyayyar Haris da Ahmadi Malam, ya za'ayi da yaron?"
Zungurinta Maimuna tayi cikin tashin hankali, Khadin na zabga mata harara, taga alamar ko kadan Maimuna ba zatayi hankali ba har yanzun. Har wani abin tausayine a batun daya shafi kishiya
"Ni dai kar ayi mishi wani abu, idan sihirine a warware abin ya kaunace shi dai-dai da sauran yaran"
Maimuna ta fadi cikin rawar murya, ba jan yaran take a jikinta ba sam, bata dai tsangwamar su, idan sun zo bangarenta su zauna, idan abincine suka samu su Khalifa naci sukan ci dasu, suyi wasan su. Amman Haris har rawar jiki yaron yakeyi idan ta saka shi ya miko mata abu, ko kuma Ahmadi ya aiko shi bangarenta, da gudun shi yakan shigo. Harda murmushin nan da duk idan yayi sai taga kamar Ahmadi. Batasan kome takeji akan su Haris kauna bace, tafi alakanta shi da shakuwa da kuma shiga rai irin wanda yara suke dashi, wani garin magani ya dauka ya bata
"A ruwa zaki dan barbada yasha, shikenan"
Karba dai tayi kawai badan zuciyarta ta aminta ba, haka ta dawo gida tana jinta kamar marar lafiya. Duk shigowar dasu Haris din sukayi ranar ta kasa ko da mikewa balle ta barbada maganin ta san yanda zatayi ta bashi. A haka Ahmadi ya shigo ya sameta, yaran suka tarye shi da gudun su suna fadin
"Abbu sannu da dawowa"
Kamar yanda suke kiran Ahmadi da shi, Maryama kuma Mami. Amman duk a cikin yaran Haris ya zabi ya dauka, sai ta bishi da kallo, bataso yanda ya tabbatar mata da zancen Malam Mainasara ba, sam bata zaci Maryama na da zuciyar wannan muguntar ba. Ita kam ba zata saka ido Ahmadi ya dinga nuna bambanci a tsakanin yaran ba.
"Duk yaran baka ga kowa ba sai Haris kenan?"
Ta bukata, tsareta Ahmadi yai da idanuwa, duk rashin kunyarta tana bala'in shakkar shi, yanzun ma tsintar kanta tayi da sauke nata idanuwan. Saida ya sallami yaran ya basu alawa da biskit din daya siyo musu tsaraba, suka fice daga dakin, sannan ya kara kallon ta
"Me yake shiga kanki ne wani lokaci?"
Kallon shi tayi itama
"Ni babu abinda ya shiga kaina, amman kana nuna bambanci tsakanin yaran. Inma Haris kafi so bai kamata kana nunawa karara ba, ko ni zuciyata bata sosu ba, yara ai suna gani, kuma yaro baya mantuwa"
Numfashi Ahmadi ya sauke, Allah ne shaida yana kaunar yaran shi, idan ma akwai wanda yakeji daban a cikin su Zubaida ce. Kaunar da yake ma yarinyar daban take, sai yake jin kamar tafi kowa bukatar kaunar shi, dan kasancewarta mace, ko kallon su yake yana hasaso yanda rayuwa zata kasance musu, sai ya dinga ganin su Khalifa sunyi aure da iyalinsu suna zuwa duba shi badan suna bukatar shi ba, dan kyautatawa kawai, amman yakan hango Zubaida har karshen rayuwar su tana bukatar kulawar shi, kuma ba zataji kamar ta girmi taimako daga wajen shi ba.
Haris na da kwalafaci, a iya zaman da yake da yaran shi yana kula da dabi'un su, Haris na cikin yaran da suke yunwar kulawa, ko yanayin shi ka gani yanda yake so yayi komai dan ya faranta maka ko zaka kula shi ya isa ka fahimta, ba bambanci yake nunawa ba, kaunar su yake nuna musu dai-dai bukatar su, amman idan yai kokarin fahimtar da Maimuna zata sauya zancen shi zuwa wani abin. Shisa ya sake zancen gabaki daya
"Yaya Ayuba kemun maganar kara bude wani shago, ina jin zan mishi zancen zaki kawo wani abu ko yaduka ne a siyo a juya miki...."
Kai kawai ta iya jinjinawa, ta kula da maganar Haris ne bayaso ayi. Shisa ta kyale shi, washegari kuwa da safe saiga yaran sun shigo dakinta, tana hada shayi. Zuciyarta na rawa ta sami kofi ta shiga kitchen, anan ta kwanto maganin da yake nade cikin karbun zaninta, sai take ganin kamar Ahmadi zai fito ya ganta, barbadawa tayi a kofi tana saurin zuba ruwan shayi a ciki, dan shekawa tayi, ko bai shanye ba inta samu ya kurba hakan ma ya isa. Tana shiga daki ta ajiye kofin a kasa ta nufi inda Bilal yake rike da cokali mai yatsu da batasan inda ya dauko shi ba karya cake ido ko wani waje. Kama shi tayi ta karbe cokalin, kallonta yakeyi da ido kawai tunda da wahalar gaske kaji kukan shi.
Tana juyowa taga kofin shayin da ta ajiye a hannun Rayyan, ya kuma daga ya kafa bakin shi
"Rayyan...."
Ta kira cikin tashin hankali, kafin ta karasa ta karbe kofin harya shanye. Dago shi tayi gabaki daya ta rikice
"Na shiga uku ni Maimuna.... Na shiga uku, Rayyan...."
Take furtawa tana tale bakin shi kamar hakan zai dawo da abinda yasha, kafin ta saka hannu tana taba fuskar shi, goshin shi da wuyan shi, har hannu tasa cikin rigar shi taji ko ya fara alamun zazzabi, bata taba tsorata irin haka ba, sauke shi tayi kasa dan sai buntsurewa yake yi tana tsugunnawa itama
"Dan ubanka ka tsaya kafin in kwada maka mari"
Ta fadi jikinta ko ina na bari da tashin hankali, dai-dai shigowar Ahmadi
"Lafiya? Me ya faru? Me ya same shi?"
Ya jero mata tambayoyin ganin yanda take a rikice
"Kamar wani abu naga yakai bakin shi, kafin inzo harya hadiye"
Ta furta muryarta na rawa, dana sani ne yai mata rumfa, saboda tashin hankalin da take ciki na rashin sanin mai maganin zaiyi tunda a kan idanuwanta taga karfin aiki irin na Malami Mainasara.
"Bakwajin magana wallahi, na rasa me yasa kuke ajiye kananun abubuwa da yaran nan zasu iya dauka su hadiye...."
Ahmadi ya karasa maganar yana daukar Rayyan da a lokacin duka shekarun shi basu karasa hudu ba
"Me ka ci Rayyan? Fadamun kaji?"
Kai Rayyan din ya girgiza mishi alamar shi baici komai ba. Babu dabar da Ahmadi bai mishi ba, amman yace shi shayi kawai yasha. Barin shi yayi tunda zai fita aiki, yace ma Maimuna din da taga ko zazzabi ya fara ta dauke shi ta kai shi asibiti, kudi ya dauka ya bata, duk da yakan ba kowaccen su kudi su ajiye tsaron laluri koda wani abu na gaggawa zai taso shi yana wajen aiki. Yinin ranar Rayyan wasan shi yake kamar komai bai faru ba, itace ta wuni ta kuma kwana da zazzabi.
Har alkawari tayi na cewa in dai komai bai sami Rayyan ba, har abada ta daina bin Malamai zata cigaba da addu'a tana shan karya tambaya dai da kaikayi koma kan mashekiya, babu kalar addu'a da alkawurran da bata dingayi ba. Daga wannan zazzabin da takeyine ya juye mata laulayi mai zafin gaske. Ta sha wahala matuka, cikin da ta samu kuma na kara daga kimar aikin Malam Mainasara a idanuwanta. Bata yaye Rukayya ba kuma ta sami cikin Shamsu, kamar yanda tayi a haihuwar Khalifa da Zubaida, harma da Rayyan. Duk yanda Khadi taso su koma wajen Malam Mainasara kiyawa tayi, dan ta tsorata da lamarin shi akan Haris, batasan meye ya bata ba har Rayyan yasha, tsoro kuma ya hana ta furtawa kowa zancen, har aminiyar tata Khadi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.