Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 124 of 125
Yau kam tsaye yake kofar gidan su Aisha yana neman kwarin gwiwar shiga cikin gidan. Dakyar ya iya kwankwasa maigadi ya bude mishi, kallon Bilal yakeyi yana mamakin inda ya shiga a duk tsayin shekarun, gaishe da shi Bilal yayi yana wucewa harabar gidan, zufa har cikin tafukan hannayen shi yake jinta. Ba tunaninta bane baiyi, sosai take fado mishi. Ko bayan ya dawo dinma tana ran shi, yana tunanin inda rayuwa ta kaita, kasa hakuri yayi yace ma Rayyan
"Aisha tayi aure na sani... Tayi aure yanzun"
Tafiyar shi ta saka ya rasa abubuwa da dama, bayajin wata zata so shi yanda Aisha taso shi. Ya rasa shekaru uku a tare da su, baiga auren da yawa daga cikin yan uwan shi ba, baya cikin hotunan su da rayuwar da sukayi a shekarun, ya kuma rasa Aisha, kai Rayyan ya girgiza mishi
"Bana so in maka magana baka shirya ba. In ba a watan nan tayi aure ba tana nan, naganta a gidan mai last month"
Dan ba zai manta bayan sun gaisa ba, shi duk daburcewa yayi da yaji ta tace, yana zaune cikin mota, ya juyo ya ganta
"Hamma"
Saukowa yayi, da suka gaisa saiya rasa abinda zaice mata, kamanninta suna nan, amman ba yarinyar da yasani bace, ba budurwar Bilal din shi da take yi musu girki bace a makaranta, wannan ta girma, ta zama cikakkiyar budurwa, idan sa'anni daya suke da Layla ba zata shige shekaru ashirin da biyar zuwa da shida ba yanzun. Ba kamar sanda ya santa tana sha wani abu ba. Haka kawai ya tsinci kan shi da son tambayar ko tayi aure, sai ya kasa, bakin shi yayi mishi nauyi, dan yana jiran Bilal ba shida tabbas din zai dawo, baiga dalilin da zaisa yayi mata tambayar ba, amman ga mamakin shi dariya tayi a nutse
"Banyi aure ba Hamma, ban dade da gama bautar kasa ba..."
Kai ya jinjina mata, labarin yayi mishi dadin ji, sallama sukayi da sakon ta na ya gaishe da Layla
"Ka dauki kafafuwan ka kaje kafin ka rasata gabaki daya"
Shine abinda Rayyan ya fada mishi
"Kana tunanin zata so ni har yanzun? Ni din bani da komai da zan bata, ga Nur kuma..."
Kallon shi Rayyan yayi
"Kana da zuciyar ka, ni bansan me zance maka ba, ban iya kalamai kamar Abbu ba, idan kana tunanin makaranta ne na fada maka ina sake tsayar maka duk shekara, zaka iya cigaba sanda ka shirya. Zaka iya fara zuwa kasuwa kasani in ka fadama Abbu, zaka samu sana'ar da zaka iya rike mata..."
Sauraren Rayyan yakeyi
"Nur ba zata hana komai ba in dai tana son ka har yanzun, zata fahimce ka, kuskuren ka a wajen Allah ma mai yafuwa ne balle kuma mutum, rashin ta ne idan bata fahimta ba, sai ka hakura, sai ku hakura da juna. Amman kaje, ko ba komai ta cancanci kayi mata bayani"
Numfashi ya sauke yana sake kallon Rayyan daya dakuna mishi fuska
"Na gaji da magana Bilal, bansan me zan kara ce maka ba"
Dariya yayi, kamar yanda yayi murmushi yanzun duk kuwa da yanda yake jin zuciyar shi na mishi rawa. Wayar shi ya zaro daga aljihun shi yana kiran lambarta, sai da ta kusa yankewa sannan aka daga
"Aisha"
Ya fadi yana jin yanda take fitar da numfashi daga dayan bangaren
"Nawan?"
Ta kira cike da shakku da tsoron da yake karanta a yanda muryarta take rawa.
"Ni ne Aisha, ina cikin gidan ku..."
Jin yanda take fitar da numfashi yasa shi dorawa da
"Ban rasu ba, bana cikin motar da ake tunani, bana ciki Aisha"
Daina jin ko motsinta ta dayan bangaren da yayine ya saka shi sauke wayar daga kunnen shi, mintina ya bata ta tattara nutsuwar kafin ya sake kira har sau biyu, amman ba'a daga ba
"Ki daga dan Allah, Aisha ki daga"
Yake fadi yana sake kiranta, da yake kan shi na duke yana kallon wayar baisan ta karaso ba
"Nawan"
Ta fadi tana saka shi dagowa yana kallon ta, tunda yake da ita yaune karo na biyu da take tsaye a gaban shi babu hijabi, na farkon kuma a asibiti ne. Ko takalma babu a kafafunta, shisa baiji takun tafiyarta ba
"Nawan..."
Ta kira wannan karin muryarta na karyewa, kai yake iya daga mata, kafin yayi wani motsin kirki ta hade space din da yake tsakanin su, a jikin shi ya jita, ba haramcin hakan bane tashin hankalin shi, asalima so yake ya zagaya hannuwan shi ya riketa a karo na farko a jikin shi ko dan kewarta da yake ji a ko ina na jikin shi. Amman a cikin gidan su yake, baida idon da zai kalli wani na gidan su idan ya fito ya gansu a haka. Shisa ya kamata yana dago ta daga jikin shi
"Ki rufamun asiri Aisha, laifina mai yawane har a idanuwan yan gidan ku, kar ki mu kara musu dalilin da zasu hana mun ke"
Hannu tasa tana goge hawayen da ta rasa ta inda zata fara tsayar da su. Duk yanda Bilal yaso ta koma gida ta dauko takalma da hijabi kiya tayi, haka ya hakura ya kyaleta, anan suka tsaya yana rasa ta inda zai fara yi mata bayani. Sai ya zabi yaji yanda take a maimakon bayani
"Ban sani ba Nawan, ban san ya nake ba, amman na san komai zai dai-daita tunda ka dawo kafin a hadani aure da wanda bana jin soyayyar shi ko kadan a cikin zuciyata"
Hira sukayi, hirar duk da tazo musu ita sukeyi, dakyar ya iya barinta da tarin alkawurran da yake fatan cikawa. Bai mata bayanin komai ba sai da yaje gida, har aka kira asuba suna manne da juna a waya. A washegarin ranar ya samu Abbu da maganar aje gidan su Aisha, bai musa mishi ba kuwa, da yake itama Aisha ta samu Baban nata da cewar za'a zo a gan shi. Ana isha'i su Abbu sukaje gidan. Bilal da yake gida ya kasa zaune ya kasa tsaye yana jiran dawowar su, sai kiran Aisha yakeyi sai tace mishi
"Ba su tafi ba har yanzun, ban san me suke cewa ba, bana jiyo su daga inda nake. Nawan ba zan iya sake rasaka ba, bana jin zan dawo dai-dai wannan karin"
Bashi da kalaman bata tabbaci idan ba dawowar su Abbu ya gani ba, shisa yake fada mata na shi tsoron. Saboda da gaske ne, babu macen da zata so shi kamar ita. Su Abbu kam da albishir din an bashi Aisha din suka dawo mishi
"Kaddarar su mai girma ce, ni ba zan hana Bilal ita ba, ba zan hana shi Aisha ba. Allah ya san dalilin da ya sake hada su"
Sune kalaman Baban Aisha, shisa Abbu bai boye mishi komai ba har da kaddarar rabon Nur, da yake mutane ne masu dattako da wadataccen ilimin addini daya fadada fahimtar su, hakan bai zame musu matsala ba. Baban Aisha ya jima yana juyayin kaddara irin ta yaran. Bilal kasa hakuri yayi, motar Ayya ya ara yana zuwa gidan Rayyan dan bayason ya fada mishi a waya, ya fi so ya gan shi ido da ido
"Hamma an bani Aisha, an bani ita"
Shine kalaman shi na farko bayan ya shiga gidan Rayyan din
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.