Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 125

Bata bar gidan Gwaggo ba saida kwarin gwiwar Malamin Gwaggon zai mata maganin matsalar auren nan da Ahmadi yake so ya jajibo musu. Dan ko da ya dawo gidan ya rufeta da fadan da tunda suke duk tarin laifukan da takeyi bai taba mata irin shi ba akan zuwan da tayi gidan su Maryama hakuri ta bashi. A ranar kuwa ta kwana tayi juyi tana zubar da hawaye, tana kara tabbatar da asiri akayiwa Ahmadi, inda babu asiri shidin bazai taba daga mata murya akan wata mace ba.

Ba'a cika sati biyu ba Gwaggo tazo gidan ta kawo mata magunguna da rubutun da zata sha ta shafe jikinta, sai maganin kuma a barbada a abincin da Ahmadi zaici.

"Kinji asiri ne ko? Turaren ne ta goga tazo nan gidan dashi, har a kofar gida tayi miki barbade ya tsallaka"

Kada kai kawai Maimuna tayi, mutum ba abin yarda bane, shisa kawarta daya Khadi tun tasowar ta, saboda rashin yardar da take da ita. A shekarar da ta wuce Maimuna ba zata manta ba, wajen sau hudu Maryama na zuwa gidan da sunan zumunci, ashe duk karyace, mijinta take kokarin aurewa. Wasu cikin kudaden da Ahmadi kan bata da ba wani abu take siye ba dan shidin mai kyautatawa iyalin shine ta diba tabawa Gwaggo dan ance gaba harda na tsari za'a karo mata da wanda za'a turo aljanin da zai katange gidan ko da su Maryama zasu gwada wani asirin.

Ranar jikinta har bari yake da Ahmadi yakai lomar abinci, sai tashi tayi tabar mishi dakin tana wucewa bayi ta kulle, inda tai zaune tana garzar kuka, sai takejin kamar taci amanar zaman su, kamar bata kyautawa kaunar da Ahmadi yake nuna mata ba da ta barshi yake aikawa cikin shi abincin da yasha garin magunguna har kala biyu, ga lamurje da ta hada mishi da ruwan rubutu.

"Kaga abinda hange-gangen ka ya janyo mana ko Ahmadi?"

Ta furta tana wani irin kuka mai taba zuciya, sai takejin kamar ta tsallaka wani waje yau mai wahalar komawa baya. Sai dai me babu abinda ya canza, da duk rana da yanda maganar auren Ahmadi take kara kusantowa. Maganar tashin hankalin da Maimuna take ciki ba'a fadi. Ga laulayin ciki daya sakata a gaba lokacin, kalar kulawar da Ahmadi yake mata na kara hura wutar kishin shi, ko rufe ido tayi ta kwatanta raba kaunar shi da wata Maryama sai zuciyarta tayi kamar zata tarwatse. Sai yanzun take ganin gaskiyar Khadi, take ganin wautar da tayi wajen kokarin hanata shiga Malamai saboda rashin kyawun hakan a addinance.

Khadi itace ta ukku a wajen mijinta, shigarta sai da tayi nasarar fitar da ta biyun daga gidan. Bayan fitarta ne yai dai-dai da rabon cikin da Khadi din ta samu, dan ta fadawa Maimuna cewa Malamanta sunce mata kishiyarce ta qulle mata mahaifa. Da tana ganin kamar haihuwa nufin Allah ne, sai yanzun ta gasgata zancen Khadi, kishiya ba abinso bace ko da ta batumbatumi ce. Ranar da kanta ta sami dan aike har gidan Khadi tace inta sami dama ta leqota. Kwanaki biyu tsakani kuwa Khadi tazo gidan.

Kuka sosai Maimuna ta tusa mata

"Khadi ki taimakeni, Malaminkin nan da yayi miki aiki kije mun wajen shi ko zai taimaka mun akan Ahmadi, dan Allah Khadi, wallahi ya kara auren nan zuciyata bugawa zatayi"

Dariya Khadi tayi har tana saka Maimuna jin haushi

"Ai gara da kika farka, idanuwan ki suka bude... In anyi duniya da Manzo kin kawo kukan ki inda za'a share miki"

Wannan maganganun sun kara karfin amintakar da take tsakanin su. Kudade Maimuna ta baiwa Khadi masu yawan gaske, dan idanuwan ta sun rufe da zafin kishin da bata tunanin addu'ar neman sauki akan shi, ta saki Allah ta komawa yan tsubbun da ta aminta sune kadai maganin matsalar da take fama da ita yanzun. Sai dai wani sabon tashin hankalin ta shiga dan Malamin Khadi ya hango dole sai Maryama ta shigo gidan sannan zata iya nasara a kanta

"Da ayaba akayi mishi wannan mallakar, da ace baki ma farga da wuri ba da yanzun sun shiga tsakanin ki da Ahmadi, dole sai ta shigo gidan za'a san yanda za'a karya sihirin..."

Ya kuma tabbatar mata dole saita kara jajircewa daga ita har yaranta. Kullum cikin boye-boye magunguna take da take bankadawa ma cikinta da yara a matsayin karya tambaya da kuma kaikayi koma kan masheqiya. Wasu da inta jika Ahmadi yagani sai tace mishi maganin shawarane da Gwaggo ta hado mata, wani lokaci harya karba kanshi tsaye yasha shima, tunda ta gano wannan hanyar cewa bokon shi bata rabashi da magungunan gargajiya ba take bashi wasu kanta tsaye da sunan maganin Basir ko shawara ko sanyi.

Kishin da yake cinta ne yasa ta zabi daga musu hankali daga ita harshi ko zai kara saka tai gabala akan shi ya fasa auren nan, amman kullum nuna mata yakeyi asirin da su Maryama sukayi mishi mai karfine dan bazai taba iya fasa aurenta ba. Yanzun ma kallon shi take yanda yake yabonta kamar ita kadai din ta ishe shi, harya karasa cin abincin yanayin hamdala

"Sannun ki da kokari, Allah yai miki albarka"

Ahmadi ya karasa yana mikewa ya tattara kwanukan ya fita dasu dan ya taimaka mata, duk idan ta wuce da turtsetsen ciki haka, koya dawo yaga gidan qwal saiya kara jinjinawa mata, ko a tunani ya hasaso kanshi da cikin jikinta sai ya hango yanda zai wuni shame-shame a kwance, amman ita harda kokarin girki, ko da tana laulayi sai yayi da gaske take kinyin girki, koyane saita lallaba ta dafa mishi abinda zaici. Shisa darajarta a zuciyar shi mai girma ce. Ganin da yayi magriba ta karato ya saka shi daura alwala kafin ya karasa dakin yana fadin

"Bari in fita masallaci...."

Batace mishi kanzil ba, sosai yake kewar hirarrakin su da yanda halin ko in kula din da take nuna mishi yake ci mai tuwo a kwarya. Haka yasa kai ya fice daga gidan. Ko da sukai sallar Magriba nan suka tsaya da wasu cikin unguwa danjin labarin Makka daga sabon Alhajin daya dawo satin daya fita wato Sambo. Da yake Ahmadi ba ma'abocin zaman majalissa bane ba, tunda Alhaji Sambo ya dawo basu hadu ba sai yau, yakan tsaya a lokutta irin haka a gaggaisa dan karamcin mutanen unguwar ba karami bane ba. Haka Alhaji Sambo ya dinga nishadantar dasu da labarai kayatattu yana kwadaita musu zuwa aikin Hajji duk idan halin hakan ya samu.

Kiran sallar Isha'i ya tarwatsa taron nasu, inda ana idarwa kai tsaye Ahmadi gida ya wuce, yana shiga soron ya mayar da gidan ya rufe sanin ba bako zasu karayi ba, inma sunyin a kwankwasa yaje ya bude. Jin shirun gidan ya tabbatar mishi da yaran sunyi bacci, da ya shiga daki kuwa Maimuna kadai ya samu, yasan harta kaisu dakin da suke kwana ta kwantar, baisan kuka takeyi ba saida ya zauna gefenta

"Subhanallahi.... Maimuna? Lafiya? Me ya faru? Ko jikinne?"

Ahmadi yake tambaya hankali a tashe yana riko hannunta, kai take girgiza ma duk tambayoyin shi alamar a'a kafin tace

"Me yasa ba zaka rayu dani kadai ba? Me kakw tunanin Maryama zata iya baka wanda ni ba zan iya ba? Ka fadamun dan Allah kagani, Wallahi Ahmadi zan maka komai. Karka tonamun asiri ka hadani da wata...."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.