Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 28 of 125
Ba karya kunnuwanta sukayi mata ba, tabbas taji muryar Rayyan din yana kiran Layla. Shisa ta labe ko zata ga fitowar ta, taga alama idan ba jan ido ta nuna akayi karamin tashin hankalin da aka kwana biyu ba'ayi irin shi a gidan ba, to Layla ba zata kyale mata yaro ba
"Shegiya mayya mai zubin yan ruwa. Yarinya baki tafasa ba kina kauri. Wai yar yarinyar nan harta san ta kashewa maza murya. Kai ni Maimuna naga ikon Allah"
Ta furta ita kadai, dan sambatu shine abokinta tun da Rayyan din ya dawo, kusan kullum zaka ganta manne jikin window, tun yaran na magana har sun kyaleta. Huda takan aika idan bata makaranta tace taje ta dubo mata idan Rayyan yana nan, ko ta saka mata ido idan ta gansu da Layla tazo ta gaya mata, abinka da kuruciya randa ta gansu kuwa tun a gaban shi tace
"Ayya tace dana ganka da Adda Layla inje in fada mata"
Da gudunta kuwa ta karasa har dakin Ayya din, inda ko mintina biyu bata hada da shiga ba Rayyan din ya rufa mata baya, tana cikin rattafowa Ayya zance, sai da ya kamo hannunta ya juyo da ita sannan ya wanketa da maruka har biyu
"Karyaki zanyi idan kika sake dibo gulmata kika kawo, kina jina, karyaki zanyi wallahi"
Yake fadi yana girgiza Huda da take wani irin gigitaccen kuka da ba ita kadai ta rude ba, har Ayya da ta fisgeta, babu wanda Rayyan bai daka ba a gidan, daga Khalifa da sam baya shiga sabgar shi sai kuwa tace Huda, ita kadai ma take ganin yana dan yiwa fara'a wasu lokuttan. Amman ranar saboda ta kawo zancen Layla shisa yake shirin kurmantata
"Ni zaka daka Rayyan, ba ita zaka daka ba. Ka dakeni saika nuna mun ka girma kafi karfina. Tunda ni na sakata..."
Ayya take fadi tanajin zuciyarta na wani irin zafi
"Ayya..."
Rayyan ya kira ranshi a bala'in bace, saboda gani yake shi akayiwa laifi, sam bayason gulma, yaga alama kuma Ayya da kanta take so ta koyawa Huda
"Dan ubanka nace ni zaka daka, akan waccen shegiyar yarinyar ne kake neman nakasa kanwarka, kake kuma tsareni da ido"
Kai yasa yana ficewa daga dakin yabarta. Ranar yanda taga dare haka taga rana, washegari sai da tayi wa Bilal zancen
"Wai meye tsakanin Layla da Rayyan? Yarinyar nan duk sai ta lashe muku kurwa ko?"
Da yake kansu a hade yake, dariyar shi ya dinga mata, cikin salo ya canza maganar. Sai ta hakura ta kyale shi, to yanzun Huda da take sakawa ta gano mata me yake faruwa tsoron Rayyan takeyi, ko ta aiketa idanuwanta zasu tara hawaye
"Hamma zai karyani Ayya... Allah zai dakeni"
Dole ta kyaleta, sauran yaran ma babu wanda zaije tasani, idan ma sunje din dawowa zasuyi suce mata basu ga komai ba. Mami ta jima tana sakata kwanan zaune, yanzun kuma ta kawo mata alaqaqai tana sakata tuna satin amarcin Mami din da kalar bakin cikin data hadiya.
"Wallahi Maryama ke ba alkhairi bace a rayuwata"
Ta fadi rannnan da takaici ya qumeta, harda kwallarta. Yanzun kam lissafinta yazo karshe, tunda dai gobe Rayyan din zai tarkata ya koma makaranta, itama ko na kwana talatin ne kafin fitina ta dawo dashi zata samu ta maida hankalinta kan maganar bikin Zubaida. Idan san samune ma Rayyan din yai zaman shi har sai lokacin bikin tukunna. Addu'ar da takeyi baji bagani shine Bilal ya samu gurbin karatu a jami'ar, idan suna tare da Rayyan din acan zaifi dadewa baizo gida ba.
Tana kara gayawa kanta harda rashin Bilal a kusa dashi yasa ya kasa zama waje daya. To Bilal din ya fada mata cewa sunayen farko ya fito babu nashi a ciki, idan Allah ya taimaka sai jeri na biyu da suke tsammani a cikin satin tukunna. Da yake sunyi hutun islamiyya duk suna gida ranar, yaran nata ne suka rage mata tunani, dan suna zaune sunata hira harda Bilal, sai dariya suke. Daga bakin kofa ma zaka iya jiyo rakadin su, Rayyan ya shiga da sallama, yana saka wani irin shiru biyo bayan amsa sallamar tashi da sukayi, kamar basu bane suke ta hira yan dakika da suka wuce.
Kamar yanda baisan taya zai fara hira dasu ba, haka suma basu san abinda ya kamata suyi a gaban shi ba. Duk kuwa tarin kaunar da suke mishi, kowa gudun yin kwakkwaran motsi yakeyi kar su bashi dalilin da zaisa ya juya, dan yana tsaye yaki karasawa
"Ka shigo mana to, kayi tsaye kamar dan sanda"
Cewar Bilal, yana saka har Zubaida bin shi da kallo, dan Bilal ne kadai yake da kwarin gwiwar yi ma Rayyan din magana haka, ita ma sai tayi sa'a yake gaishe da ita. Yana iya wucewa ta wuce, zata kuma yi karya idan tace hakan baya bakanta mata rai sosai. Tana shekararta ta karshe a jami'ar Bayero inda take karantar Mass Communication. Mijin da zata aura a makarantar suka hadu lokacin tana shekararta ta biyu, yanzun kuma yana aiki da gidan jaridar Rana. Dan kusan duk bangaren karatun su daya da ita, kawai shi din journalist ne. Wani lokacin har mamaki Zubaida takeyi na yanda ko kadan Rayyan bai damu da su ba.
Tasan kowa abin nacin ran shi, ba dai sa tattaunawa ne, aikam karasawa Rayyan din yayi ya zauna kan hannun kujerar da Bilal yake, a hankali Bilal din yaci gaba da jansu da hira har kowa ya saki jiki, amman da ido Rayyan yake binsu, yau dai yayi kokari tunda har saida aka kira sallar Magriba tukunna duk suka tashi. Ayya taji dadin shigar tashi, ta manta ranar karshe daya zauna ya hada mintina sha biyar cikakku a cikin dakin nata. Duka abinda basu sani ba shine maganar da Bilal yayi mishi
"Kai kasan ko na zauna ni bansan me zance ba, ku bakwa gajiya da surutu"
Rayyan ya fada a takura
"Ko bakace komai ba idan ka zauna Ayya zataji dadi, saboda Allah ko tausayinta bakaji? Uwa uwa ce (Batul Mamman) Rayyan. Ace sai dai Ayya tazo inda kake, kai ba zakaje ka gaisheta ba idan ba yunwa ce ta koraka ba... Babu wanda zai fada maka baka kyautawa, nima dana fada maka ba lallai ka saurara ba, tunda kai babu wanda ya isa ya saka a hanya"
Bai amsa Bilal din ba harya fice daga dakin. Da rana ya aiki Layla ta siyo mishi batirin tocila din shi da yake amfani da ita a makaranta, yasan zai iya siya idan yaje, kawai yana son dalilin da zai ganta ne, tunda yasan washegari zai koma makaranta, duk ranar aiken rashin dalili yake kirkira yana mata, sanyinta ne yake mishi wani iri, kamar ba Layla ba yau, harar da takan watsa mishi duk idan tagaji ba taso ta fada mishi tana kuma tunanin baya ganinta yau babu.
Sosai ya dinga sakata kananun abubuwa amman sai yaganta da sanyi-sanyi, shisa da ta kawo mishi battery din yace
"Menene? Me yake damun ki?"
Kallon shi tayi da idanuwanta, itama ba zatace ga asalin abinda yake damunta ba, kamar zatayi zazzabi take ji, ga wani irin ciwo da takeji kasan cikinta nayi, inya tsira mata har cikin bayanta da cinyoyinta da suka rike takeji
"Kawai bana jin dadine"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.