Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 65 of 125

"Rayyan!"

Yaji muryar Ayya kamar a wata duniya kafin wani haske ya gilma ta cikin idanuwan shi yana saka shi runtsa su ya sake budewa, ji yake kamar an kama kafafuwan shi an sadda kan shi kasa ana jijjiga shi, idan wani abu ya sami Layla, baisan ya zaiyi ba, amman bai kara sanin asalin firgici ba sai da yai tunanin wani abu ya sami Bilal

"Gabana sai faduwa yake tun safe"

Ya tuna maganar Bilal jiya da daddare

"Kayi addu'a"

Ya amsa shi, yana kallon yanda ya danyi jim kamar mai nazarin wani abu sai kuma yaci gaba da danna wayar da yakeyi, sai yau din yaga kamar akwai rama a cikin idanuwan Bilal din da baigani ba sai yanzun yake tunawa

"Ka kwantar da hankalin ka, watakila ko ya ajiye wayar wani waje bai ganta ba, ka san Bilal"

Wani irin numfashi Rayyan ya sauke

"Ni da ke mun san Bilal baya ajiye abu ya rasa in da ya ajiye Ayya"

Cewar Rayyan yana sauke wayar daga kunnen shi ya kashe kiran, a gefe ya ajiyeta yana dafe kan shi da hannuwa biyu, tabbas da ace zai sami motar da zata juya Zaria ba zai kwana a garin nan ba yau, bashi da wata natsuwa idan bai sami Bilal ba. Bappa ne ya shigo da leda a hannun shi yanayin sallamar da Rayyan ya amsa ya dora da

"Zan iya samun motar da zata koma Zaria yau?"

Da mamaki Bappa ya kalle shi

"Da daren nan? Amman ka san hanyar ba aminci gareta ba ko? Kuma me yasa kake tambayar motar Zaria"

Cike da damuwa Rayyan yace

"Zan koma ne"

Sai da Bappa ya karasa ya ajiye ledar hannun shi ya zauna sannan ya fuskanci Rayyan sosai

"Lafiya dai ko?"

Bai san me yasa yaji kamar zai iya yadda da Bappa ba, bayan shi din baya yarda da mutane.  Amman yana cikin damuwa kalar da bai taba sani ba, taimako yake bukata ko daga wajen waye

"Ina ta kiran kanina baya dagawa"

Kai Bappa ya jinjina

"Watakila baya kusa da wayar, ko kuma ya yarda ba'a kai da tsinta an kashe ba. Ko wani ya dauke, akwai dalilai irin haka"

Kai Rayyan ya girgiza mishi, yau kalamai yake nema da zai misalta abinda yakeji Bappa ya fahimta

"Banda kanina, Bilal ba haka yake ba. Zai kirani ko da wayar wani ne ya fadamun. Yaune na farko da muka yini bamuyi magana da juna ba"

Numfashi Bappa ya sauke

"In shaa Allah komai lafiya. Ka kwantar da hankalin ka, ba kada lambar ko abokin shi haka? Sai ka kira a duba shi?"

Kai Rayyan ya girgiza, a karo na farko yana dana sanin halayen shi, da ace ko lambar mutum daya a cikin gidan nasu yana da ita yau zatayi mishi rana

"Mutum yana da ranar shi Hamma, duk yanda kake tunanin baka bukatar wani bayan ni da Layla ba fata nai maka ba, Allah kar ya nuna maka ranar da zata karyata tunanin ka..."

Ga ranar ta zo yau, ranar da Bilal yayi mishi addu'a karya gani

"Allah bai amshi addu'ar ka ba Bilal"

Rayyan ya fadi a zuciyar shi

"In shaa Allah komai lafiya. Na san zai kira"

Numfashi kawai Rayyan yaja yana mikewa dakyar, kamar abinda ake kira "anxiety attack" ne yake shirin kamashi saboda tashin hankalin da yake ciki. Inda jakar shi take ya karasa ya dauka yana budewa, jikin shi babu inda baya bari sanda ya dauko kwalin sigarin shi, ya dauki kara daya ya saka a baki ya lalubo lighter din saiya tsinci kan shi da juyawa, yau abubuwan da suke baqi a wajen shi yake tayi

"In ba zaka damu ba"

Ya cewa Bappa da yayi dan murmushi yana girgiza mishi kai. Kunna sigarin yayi yana shanyeta cikin yan dakika ya sake kunna wata, sai da ya sha kara biyar, amman jikin shi bai daina kyarmar da yake yi ba. Karshen daya rage ya karasa bakin kofa inda ya hango kwandon shara ya zuba, harda kwalin daya tara toka a ciki. Dawowa yayi yana kara saka hannun shi cikin jakar shi ya laluba, kafin zuciyar shi tayi wata irin dokawa da bata da alaka da su Bilal, ya manta magungunan shi, jiya bai saka a jakar shi ba

"No.. No... Please no"

Yake fadi cikin tashin hankali yana kara dubawa ko watakila bai manta din ba, amman babu su, har kayan ya fito da su yana duddubawa, kafin ya sake mayarwa yana runtsa idanuwan shi, ji yake kamar wani abune a cikin kan shi yau da yake jiran cikar lokaci kafin ya tarwatse. Juyawa yayi ya nufi kan gadon, bai karasa ba yaji muryar Bappa da shaf ya manta yana dakin ta daki kunnuwan shi

"Ka ci abinci sai ka kwanta"

Kai Rayyan yake girgiza mishi yana zama a gefen gadon saboda yanda jikin shi yake bari, sosai yanzun yake bukatar magungunan shi, badan bacci ba, sai dan mugun sabon da jikin shi yayi, jiya bai sha ba in zai tuna, yini biyu kenan bai sha ba, shisa jikin shi yake sanar da shi babu lafiya.

"Kana bukatar ka sa wani abu a cikin ka"

Cewar Bappa da ya bude ledar take away din da yayo musu a cikin hotel din, shinkafa ce dafaduka ta sha nama da kayan hadi, harda hadin salad a gefe. Yana kallon Rayyan din ya sake girgiza mishi kai

"Yunwa da withdrawal effect ba hadi bane me kyau"

Bappa ya karasa maganar yana saukowa kasa kan kafet din dakin ya ja abincin shi daya saka cokali a ciki ya fara ci. Shi din ya karanci Psychology ne a kasar amurka, zai koma yaci gaba, saboda yana son zama abinda ake kira Profiler, akwai graduate degree da zaiyi akan forensic psychology kafin ya fara aiki da hukumar tsaro ta yan sanda da yake a can kasar, yana da kokarin da yasan da wahala idan bai samu ba.

Shi din dan gidan Sheikh Abdullah Bappa ne, sunan kakan shi yaci wato Muhammad sai suke kiran shi da Bappa kamar yanda ake kiran kakan na shi, baban shi sanannen Malami ne, duk kuwa da tarin arziqin da suke da shi. Suna da dattako, ana kuma ganin girman su a garin Kano, da wahala ka kira sunan Baban shi ace an samu mutane biyar a waje babu wanda ya san shi ko yaji labarin shi. Tun da ya dauko Rayyan yaga alamun damuwa a tare da shi, karantar shi yake tayi har zuwa yanzun.

Yanayin dabi'un shi, yanda jikin shi yake kyarma da idanuwan shi da sukayi wani irin haske duk kuwa da doguwar hanyar daya sha yasa Bappa gane cewa yana ta'ammali da miyagun kwayoyi. Watakila shima Rayyan kamar sauran mutane ne masu fama da depression, daga shan magungunan da zasu taimaka sai su dinga kara daya akan ka'idar da likita ya rubuta, a hankali a haka sai abin ya zame maka shaye-shaye batare da ka kula ba. Ka kara wa kanka matsala da kanka. Rayyan kuwa shiru yayi yana tauna maganganun da Bappa yayi kafin ya kwanta yana juyawa, Bappa bai san shi ba, dan ya gane daya daga cikin matsalar shi baya nufin ya gane gabaki daya.

Amman jikin shi kyarma yake, makoshin shi yakeji kamar an zuba yashi saboda bushewar da yayi, harshen shi babu miyau ko daya a ciki. Numfashi Bappa ya sauke yana mikewa, Rayyan baiga me yakeyi ba saboda ya rufe idanuwan shi har sai da ya karaso in da yake kwance yana fadin

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.