Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 68 of 125

"Layla?"

Tana sauko da kafafuwanta daga kan gadon, tsaye Layla tayi bakin kofar, so take wani abu da zai nuna mata mafarki takeyi ya faru, kamar ace Anisa ta girgizata tana tashinta yanda ta saba da fadin

"Ke banza takwas saura"

A ranakun da suke komawa sallar asuba bayan sun makara. Amman kallon da Anisa takeyi mata ya tabbatar mata da cewa ba mafarki takeyi ba, idonta biyu. Ta dai kasa karasawa cikin dakin ne, kafafuwanta take ji sunyi wani irin sanyi. Ganin haka yasa Anisa ajiye wayar tana saukowa daga kan gadon tazo ta kamata

"Layla? Lafiya?"

Kai ta girgiza ma Anisa da ta kamata tana janta zuwa kan gadon, sai da ta zauna sannan jikinta ya fara bari

"Dan Allah menene? Me ya faru? Ko wani ne ya rasu?"

Anisa ta karasa muryarta na karyewa. Gabaki daya yanayin Layla ya gama daga mata hankali, ta san yanda mutuwa take, Yayanta ya taba rasuwa, ta kuma ga kalar hargitsin da kowa ya shiga, yanayin Layla ya nuna cewa tana cikin matsananci shock da ba labari bane me kyau yake haifarwa. Shisa gabaki daya hankalinta ya tashi

"Ki saka mun ruwa inyi wanka"

Layla ta fadi daga kasan makoshinta, watakila ruwa da sabulu su fitar mata da daudar da takeji, kila kuma idan ta saka ruwa a fuskarta zata farka. Babu musu Anisa ta tashi, sukan ajiye ruwan zafi a flask ko dan shan shayi, shi ta juye mata a bokiti tana sirkawa, da kanta ta kai mata komai bandaki ta dawo tana fadin

"Ki tashi ga ruwan can"

Mayafi kawai Layla ta cire, ko towel bata dauka ba ta fice daga dakin. Da yake sukan dibo ruwa da bokatan wankan nasu, da sun fito bandaki sukan saka omo su wanke shi har bayan. Shisa tasan ruwan ciki mai tsarkine, karkatawa tayi ta fara wanke hannayenta, a karo na farko da takejin sauqi irin na addinin musulunci, niyyarka a zuciya idan ka daurata tayi, ba saika fadeta a fili ba, bata da kwarin gwiwar motsa labbanta da daura niyyar wannan wankan da take tunanin ya zame mata dole. Tashin hankalinta bai fara ba sai da ta wanke fuskarta tana sake bude idanuwanta a cikin bandakin.

A daddafe ta karasa wankan, kayanta ta mayar tana fitowa, can ta baro bokitin, sai Anisa ce ta koma ta dauko, doguwar riga ta dauka ta sake kayan jikinta da take da tabbacin ta gama saka su har abada. Wayarta ta bude jaka tana dauka, tana kallon yanda hannunta yake bari, a kasa ta zauna. Tambayoyin Bilal ne suke dawo mata, amman yanda ta kula ya kasa gane yanda akayi abinda ya faru ya faru, haka itama take cikin wannan rudanin. Ta san sanda ta shiga dakin su, ta tuna sanda ta zauna harta sha ruwa, amman daga nan babu abinda zata iya tunawa banda tashin hankali da wani irin firgici marar misaltuwa.

Dakyar ta iya lalubo lambar Bilal tana kiran shi, bugu biyu ya daga

"Hamma ba mafarki bane ba, ba mafarki bane Hamma..."

Ta furta da wata irin nisantacciyar murya, girman kalaman na zauna mata da wani yanayi daya birkita mata komai, wayar ta sauke daga kunnenta tana ajiyewa a gefe, kafin ta janyo kafafuwanta ta hade su da jikinta. Har lokacin jinta takeyi kamar bata da kaya

"Martabar ki darajar ki Layla, martabar ki sutturar ki..."

Kalaman Mami suka dawo mata. Kalaman na tuna mata da Mami

"Mami... Mami"

Ta ke kira cikin wani irin tashin hankali, duk wata nasiha da ta tabayi mata tana dawo mata. Da gaske martabarta suttura ce a wajenta, sutturar da bata gane muhimmanci ta ba sai yanzun da take jin bata tare da ita. Kuka take nema amman sam yaki zuwa, banda wani irin numfashi da take ja tana fitarwa kamar mai ciwon asma babu abinda take iyayi, batsan shigowar Anisa dakin ba sai da taji ta kamota

"Dan Allah kiyi mun magana Layla"

Cewar Anisa da hawaye cike taf a idanuwanta, dan ita bata son tashin hankali sam, sai lokacin wani irin kuka ya fito tun daga kasan zuciyarta tana sakin shi cikin shesheka, ko ina na jikinta bari yakeyi

"Kiyi hakuri, banma san me ya sameki ba, ko me ya faru, dan Allah kiyi hakuri..."

Anisa tace tana kara rike Layla a jikinta, yanayin yanda take kuka ne yake ba Anisa tsoro, saboda bata taba ganinta cikin yanayi irin wannan ba, wayarta da ta fara ringing Anisa ta dauka tana dubawa, an rubuta

"Mami ❤"

A jiki, gyarama Layla kwanciya tayi a jikinta

"Dan Allah kiyi shiru, kinga ga Mami tana kiran ki"

Wata irin mikewa Layla tayi tana jin kamar an watsa mata ruwan zafi, fisge wayar tayi daga hannun Anisa, tana kifeta akan cinyarta, kamar hakan zai hanata rurin da takeyi, jikinta kara bari yakeyi cike da sabon tashin hankali, ji takeyi kamar Mami ta gane, kamar tasan me ya faru shisa take kiranta, tana yankewa wani kiran na sake shigowa, amman ta kasa dubawa, sau biyar ana kira tana yankewa, kukanta ke kara tsananta saboda tashin hankalin da take ciki, saboda tasan duniyarta ce gabaki daya tazo karshe shisa Mami ta gane, shisa take kiranta. Bata da abinda zata fada mata

"Fyade"

Shine kalmar farko da ta dace a yanayi irin wannan, ita kuma ce kalma guda daya da zata iya labewa bayanta dan samun sauki. Amman zuwan kalmar tunanin ta, alakanta Bilal da wannan kalmar kawai barazana take karawa shige da ficen iskarta. Ko kwaya Bilal yasha ba zai taba mata fyade ba ita tasani, ita zata bada shaidar waye Bilal. Shisa bata da kalmar da zata fassara abinda ya faru din, bata da shi, da duk dakika da yanda rudani da tashin hankalinta suke karuwa. Wanne irin mugun abune wannan yake faruwa dasu? Kamar wanda akayiwa asiri, asiri ne kawai abu daya da take da shi da zai fassara mata abin nan ta yarda, sai kuma iskokai, amman a iya saninta bata da iska, haka ma Bilal.

Sai dai akwai iskar da bata bayyana sai daga baya, watakila abinda ya faru da su kenan. Amman wa zatayiwa wannan bayanin ya gane?

"Ke yanzun kina tunanin shi Rayyan din da kike biyewa idan tsautsayi ya gifta a tsakanin ku zai aure ki?"

Kalaman Mami suka dawo mata, suna kuma tuna mata da Rayyan daya fice daga kanta na wucin gadi

"Na shiga uku, Anisa na shiga uku na"

Ta ce cikin firgici

"Ki daina Layla, babu kyau fadar haka, ki daina dan Allah. Kiyi addu'a koma menene zai zo da sauki"

Kai Layla take girgiza mata wasu irin hawaye masu dumi na zubo mata, jiya ta ga yanayin da bata taba gani ba a cikin idanuwan Rayyan, a karo na farko jiya yayi mata kalar murmushin da bata taba gani ba, zata rantse daga zuciyar shi yayi mata murmushin bayan ta fada mishi tana son shi, kamar yana son gaya mata ita da shi din zasu iya faru, a cikin murmushin shi ta ga possibility din zaman su a karkashin inuwa daya a matsayin masoya da zai iya kaisu da aure wata rana, ta hangi cikar burinta a kwayar idanuwan shi. Da yace ta tafi sai taga kamar akwai rokon da yake mata, kamar yana bata amanar kanta ne kafin ya dawo.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.