Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 25 of 125
"Layla..."
Kowa idan zai kira sunanta sai taji kamar Laila yake fadi da harafin "i" maimakon harafin "y" da take amfani da shi. Rayyan ne kawai yake kiran sunan ta yanda take jin tana furta shi a bakinta. Hatta Mami bata kiran sunanta yanda take so, yana ba harafin "y" din da yake ciki hakkinsa, tun tana mita tana gyarama sauran yan gida da mutane yanda take so a fadi sunanta harta gaji ta kyale su.
"Sam idan kana tare da yan gargajiya ba zasu barka yin gayu yanda ya kamata ba"
Shine abinda take fadama kanta a ko da yaushe. Ko maganar kananun kaya Mami tayi mata sai wannan tunanin yazo ranta. Ita Mami yar gargajiya ce, tunaninta yaki tafiya da zamani, taki gane cewa yanda sukayi tasu rayuwar daban da yanda ta yanzun take. Zabinta ne taci gaba da gudanar da rayuwa kamar zamanin da, amman ita kam tana jin ya kamata a kyaleta ta tafi a zamanance. Ko kallone ba zaka rabata da fina-finan amurka ba. Saboda yanayin 'yan cinsu yayi mata. Yanda suke gudanar da rayuwar su tayi mata.
Shisa take da wani irin buri nayin zurfi a karatu, zatayi wayewar da babu wanda zai kuskura ya alakantata da maita, zata zama tana zagaye da wayayyun mutane da idanuwanta ba zasu saka su fadin komai ba sai yanda suke jin daman ace suma sun sami idanuwa irin nata suma. Wayayyu da zasu fuskanci cewa maita bata da wani yare, asalima a musulunci bata da tushe. Ta tambayi duk wani Malami da yake a islamiyyar su ana tabbatar mata da maita bata da tushe a addini, kambun bakane kawai musulunci yai magana a kai.
Ta rasa dalilin da yasa ake hada yaren nufawa na mahaifiyarta ana fadin duk yawancin su mayu ne. Mami kan jaddada mata da cewa mahaifiyar ta ba mayya bace duk idan ta shiga da kuka wani lokacin kan Rayyan ya kirata da mayya. Yanzun kam yanda ya kira sunanta yasa taji zuciyarta ta wani kumbura ta cika kirjinta taf, har murmushi tayi, gabaki daya ya wanke bacin ran da ya sakata yan dakika da suka wuce. Bata juyo bane sai ma tafiya da ta fara yi, hannun taji ya riko yana juyo da ita da karfin da yasa ta fadin
"Hamma hannu na"
Gyara rikon da yayi ma hannun nata yayi yana murdawa sai da taji idanuwanta sun tara hawaye
"Dan Allah kayi hakuri"
Ta furta cikin rawar murya, idanuwanta kan rage bashi tsoro idan suka cika da ruwan hawaye haka, sai yaga sun kara sake mishi launi, sakin hannunta yayi, yana kallon yanda ta yarfe shi tana murzawa. Bude baki yayi zai magana, Maimuna da ta leqo ta gansu a tsaye tana saka shi mayar da bakin shi ya rufe
"Ina wuni..."
Layla ta furta tana kokarin mayar da hawayen da suke cike da idanuwanta bayan ta, wata irin harara Maimuna ta zabga mata, kamar surutai taji, kuma sai muryar tayi mata kamar ta Rayyan, shisa ta leqo, sanin in dai surutun shi ya yawaita to da Bilal ne. Zaka iya kirga maganar shi, itama a fuska da yanayi zakaji yanda yake yinta kan dole. Yana iya bata maka rai kayi shiru ka kyale shi, sai da gabanta ya fadi da ta gan shi tsaye da Layla, sai taga kamar data fito yana rike da hannun Layla din, daga ranar farko da ta dora idanuwanta kan Layla bata kaunarta ko kadan, kuma ta tabbatar da Layla ta san haka.
Ko tare suka shigo da su Haris sai ta koreta, itama Layla din a nata bangaren hakane, Ayya na daga cikin jerin mutanen da bata kaunar gani, da hankalinta ita ce ta farko da ta kirata da mayya. Gashi ko a hanya suka hadu cikin gidan sai ta bita da harara, tana gaishe da itane saboda Abbu, dan a yanda taki jinin Ayya ko Mami bata isa tasa ta gaisheta ba, darajar Abbu take ci, dan tana jin shi har ranta, batayi wayan sanin iyayenta ba, gara mahaifinta zata iya tuna fuskar shi, sai kuma tsillin hotunan da Mami ta samo mata nashi bayan ya rasu sanadin gajeruwar rashin lafiya.
Na rana daya Abbu da Mami basu taba bari taji maraici ba, komai da take so Abbu yana mata, a fuskar shi ma bai taba nuna cewa ita din ba daga jikin shi ta fito ba. Haka dakin Maimuna banda ita da Rayyan duka suna zaune lafiya da sauran yaran, babu mai nuna mata tsana ko wariya. Gara ma Intisar wasu lokuttan takan mata magana taqi amsata. Shisa bata damu dan bata amsa gaisuwar ba yanzun, juyawa tayi zata tafi abinta, muryar Rayyan ta katse ta da fadin
"Na ce na gama magana da ke?"
Tsaye tayi cak, Ayya da take kallon su da mamaki bayyane a fuskarta ce tayi magana
"Rayyan..."
Ta kira cike da mamaki, idanuwan shi ya dauke daga kan Layla yana mayarwa kan Ayya, jin tayi shiru yasa shi cewa
"Ayya"
Cike da mamaki har lokacin tace
"Me zatayi maka?"
Dan ita batasan lokacin daya fara magana da Layla haka ba, zata tuna lokacin kuruciya da, har saida ta fara jin wani iri kan yanda Rayyan din ya addabi yar mutane, haduwa goma zasuyi sai ya kwada mata mari, akwai tabon da har yanzun yana gefen goshinta inda Rayyan din ya hankadeta ta fadi, ranar ita kanta Ayya hankalinta ya tashi, dan bayan Maryama ta dauke Layla sai da ta daki Rayyan din. Hakan ba yana nufin taji kaunar Layla ko kadan a ranta bane, yanzun da suka fara tasawa, inba Abbu ya aiko Layla ba, yarinyar bata fara shigo mata daki.
Ta san dai Bilal ne da babu yanda zatayi da shi akan nacin Maryama da yakeyi, bata da matsala da yaran Maryama din, Haris ne daman, kuma shekarun nan sun sa yaran ya shiga ranta, da wahalar gaske ma kayi zaman awa daya da Haris bai shiga ranka ba. Wani lokaci anan falon ta yake cin abinci. Sauran yaran ne in dai tasan abu daga bangaren Maryama ya fito bata bari suci, Bilal ne kawai yake shigo mata da shi har daki kuma ya zauna yaci. Tama gaji da magana tunda dariya yakan yi yace
"Ayya..."
Da yanayin nan nashi da yakan yi duk idan tayi mishi maganar za'a barbada mishi wani abu a abincin. Kamar bai yarda yana iya faruwa ba. To tasan yana magana da Layla, ko tace Laylar ta nace mishi, kwanakin baya har zancen tayi mishi
"Bilal kaima ka fara koyon taurin kai, idan nayi magana ma ba jina zakayi ba. Banason yarinyar can tana naniqe maka, kafin ta lashe maka kurwa... Ko dan Maryama ta fara lashewa, ragowa ce Layla zata samu, kaga saika hada kayan ka gabaki daya ka koma can, in rasaka hankalin su ya kwanta ita da uwar rikon ta"
Dariya Bilal din yayi kamar a duk ranar babu wanda ya fadi wani abu da ya saka shi nishadi irin maganganunta
"Dan ubanka sai kaje kayi ai, tunda kaga ka fini tsayi, ka rainani ai"
Yana dariyar yace
"Yi hakuri, haba Ayyata, ni na isa"
Harar shi tayi tana wucewa abinta, haka ya bita yana mata hirar shi har saida ta huce. To batajin tana da matsala da Bilal, kowa ma kulawa yakeyi shi, kusan halin shi na mata shige da Haris, bambanci shine zakagani a fuskar Haris idan ka mishi abinda baiso ba, Bilal kam ko kayi tunanin ka bata mishi rai sai dai yayi dariya kawai. Amman Rayyan, zuciyarta rawa takeyi mata, saboda Rayyan daban ne, su Rukayya ma baya magana dasu mai nisan da taji yanayi da Layla din. Yanda ya tsare yarinyar da idanuwa yake yanzun yasa ba zuciyarta ba har kafafuwanta ma rawa taji sunayi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.