Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 43 of 125

"Hamma..."

Ta furta da wani yanayi a muryarta, tayi kewar shi, jiya kawai da bata gan shi ba kewar shi take ji har cikin ranta. Rayyan bai tsammaci zata kwanta mishi a kafada ba duk da ta zauna kusa da shi, wani irin tsalle zuciyar shi tayi kamar zata fito waje saboda wani irin yanayi da yaji ya tsirga mishi, tureta yayi tana shirin dawowa ya matsa da sauri

"Azumi nake Layla"

Yai maganar yana mikewa tsaye gabaki daya, turo labbanta tayi. Shi kuwa Rayyan numfashi yake mayarwa, tun rannan yake tsintar kan shi a wannan yanayin duk idan jikin su ya hadu waje daya. Bilal kallon su yakeyi, zuciyar shi kamar zata fado kasa, idan Rayyan baya kallon Layla da wata fuska data wuce yan uwantaka ya tabbatar ba zai tunanin azumin shi ba dan ta kwanta a jikin shi, tunda tanayi lokutta da dama, bai taba damuwa ba, karshen abinda zaiyi shine ya kamata ya bambare yana fadin

"Mayya ce ke? Duk wajen nan sai kin hadu da jikina? Me yake damun ki?"

Ita yake fadawa kalaman, amman Bilal sukeyi wa zafi, musamman idan yaga Laylan ta sake komawa ta mannewa Rayyan din duk da zafin kalaman shi da suke shimfide a idanuwanta. Ya rasa yanda zaiyi da su, ya kuma rasa ta ina zai fara hanasu wannan rike-riken junan da sukeyi. Yana kallo Layla ta mike itama tana shirin tafiya

"Ina zaki je?"

Rayyan ya bukata yana tsareta da idanuwa

"Ina da lecture, kawai zan ganka ne daman"

Kai ya jinjina, farar riga ce kal a jikin shi da wandon jeans, saiya dora jacket a sama, ko maballan bai balle ba, kawai ya dora ne, taku hudu yayi yana karasawa inda Layla take tsaye, mayafin da yake wuyanta yaja yana daga shi, wani dan ziriri ne, kai kawai Rayyan ya girgiza. Shi baiga amfanin mayafin ba tunda babu abinda ya rufe, bayason yanda maza suke kallonta duk idan ta wuce, wancen satin da yake wando ta saka saita dora kimono a kai, duk da haka sai da yace wa wani dan ajin su

"Ko zaka dauke ta hoto ne?"

Ganin irin kallon da yake bin Laylan da shi bayan ta wuce, murmushi kawai gayen yayi yana barin wajen. Kawai bayaso wasu maza na kallon ta, shisa ya bi bayanta, ya taba ganinta da rigar kuma yaga da madauri baisan me yasa bata saka ba. Hannunta ya kama ranar

"Ina madaurin rigar nan?"

Cike da rashin fahimta tace

"Yana cikin jakata"

Jakar ya karba da kanshi ya bude ya dauko, sannan ya mayar mata da jakar cikin hannunta. Da kan shi ya zagaya madaurin yana soka shi a mazaunin shi ya taho da shi ta gaba ya daure mata yanda ya taba ganin ta daure, saida ya rankwashi kanta daya gama yana sakata fadin

"Wayyoo Hamma"

Ta dafe wajen dan taji zafi sosai, kara kai mata rankwashi yayi ta kauce, idanuwanta cike taf da hawaye ta kama hanya. Dan sam Rayyan baya damuwa da mutanen da suke waje, bama ya damuwa da yanda saboda idanuwanta yanzun tana cikin 'yan matan da aka sani a fadin makarantar cikin kankanin lokaci, ga turancinta da yake burge mutane. A ajinsu ma kowa so yakeyi yai kawance da ita, har maza suna mata magana, kawai dai ba kowa take kulawa ba, a matan ma baifi mutum biyu suke yawo tare ba, saboda ta kula duk sunfi kowa wayewa a cikin ajin, kuma daku nan su da juna babu nisa a hostel, floor daya suke, hawa na ukku. Suna ma zuwa wajenta a dakin su.

Jacket din da take jikin shi Rayyan ya cire. Sai da ya rankwasheta

"Me nayi? Me nayi ni?"

Layla take tambayar shi kamar zata fashe da kuka, rigar ya zagaya yana kafa mata idanuwa,  hannunta ta zira a ciki, tana saka dayan ma, ya gyara mata zaman rigar data sauka tana rufe bayanta sosai, maballi daya ya kama yana ballewa, bude baki tayi zatayi magana ya katseta da fadin

"Bakin ki zan fasa in kikayi mun surutu...wuce ki bani waje ni"

Wucewar tayi kuwa, kafin ta juyo tana kallon Bilal da yake zaune yana kallon ikon Allah

"Hamma sai anjima"

Kai ya iya daga mata, yana kishin ganinta a haka, bai taba magana a kai ba, bai taba kokarin hanata shigar da takeyi ba, a zuciyar shine bayason abin, amman Rayyan yayi wani abu a kai, a gaban idanuwan shi ya nuna mishi dalilin da yasa idan yana waje Layla bata ganin kowa sai shi. Baisan me yake ji a ran shi ba, ranar kuma da suka koma gida ya manta yake mishi tayin abinci kai ya girgiza yana amsawa da

"Zanci anjima"

Sai lokacin Bilal din ya tuna

"Kana azumi fa ko?"

Kallon shi Rayyan din yayi

"Ni na fada maka?"

Kai kawai ya girgiza mishi, tun ranar kuma yana kula da shi a ranakun litinin da alhamis, azumi baya wuce shi. Ba dai yason kowa yasani ne tunda badan wani yakeyi ba. Har mamakin mutanen da kamar jira suke ayi musu tayin abinci su sanar cewa suna azumi ne, kamar dan wani suke ibadar. Abinda kakeyi dan Allah, a haka sai ladan yayi tafiya batare da sanin ka ba, idan har ka tsarkake niyyarka, ya kamata ibadunka da ba farilla ba su zamana tsakanin ka da wanda kakeyi domin shi. Abincin Bilal ya karasa cinyewa yana mikewa ya dauko ruwa ya sha hadi dayin hamdala.

*

Hanjin shi har daurewa yakeyi sanda suka dawo daga sallar Magriba. Gashi baisan abinda zaici ba. Ruwan zafi kawai ya dora a tukunya da nufin ya sha shayi, baiga Bilal ya dauki kulolin Aysha ba sanda zai fita, balle yace watakila in zai dawo zai taho musu da abinci. Baiso a dame shi shisa yana shiga yaja labule ta ciki ya tura kofar dakin, ko babu wuta gara yayi fifita da wani ya dago labule neman Bilal ya saka shi yin maganar da bai shirya ba, balle kuma yau yan nepa suna jin mutunci, tunda suka dawo akwai.

Ya juye ruwan zafi a kofi kenan ya saka Lipton yaji ana Kwankwasawa, karamin tsaki yaja yana yin shiru, idan aka gaji za'a tafi, yasan idan Bilal ne zai tura dakin tunda yasan yana ciki. Sake Kwankwasawa akayi, ya kara jan wani tsakin. A fusace ya mike tsaye yana bude kofar dakin, ga mamakin shi Layla ya gani tsaye sai maida numfashi takeyi, ta rungumo wani kwando da kuloli a ciki, kamar zatayi kuka tace

"Hamma ka amsa, hannuna zai karye"

Tsautsayine ya sa ta saka riga da siket, da zata hau mashin har kofar gidan su Rayyan. Keken da ta samu kuma yaki shiga da ita lungun. Har ca tayi ta kara mishi kudi saboda kwandon data dauko amman yakiya. Haka ta tako tana tafiya tana kwashe mishi albarka saboda nishin da take dirkawa, ga kwandon hannu daya sai cirewa yakeyi idan ta rike, sai rungume shi tayi. A jigace ta isa gidan su Rayyan din, hannuwanta duk sunyi sanyi.

"Idan ba zaka amsa ba ka matsa daga kofar"

Tayi maganar cikin tsiwa ganin Rayyan din yana tsaye yana kallonta. Hannun shi daya daga yasata tunanin kwandon zai karba, tallafe mata kai yayi

"Rashin kunya"

Ya furta yana matsawa, ba zai karba ba tunda tayi mishi surutu, karasawa tayi cikin dakin tana ajiyewa a kasa, inda ya tashi ta zauna tana mayar da numfashi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.