Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 24 of 125
"Registration din su da dan wahala Rayyan, da mun tafi tare sai in tayaka, kaga ba sanin kan makarantar kayi ba"
Kallon shi Rayyan din yake yi, gabaki daya surutun ya ishe shi, tsayuwar da yayi ma ya gaji da ita
"Zan taho idan na shirya..."
Yanayin yanda yai maganar yasa Haris din jinjina kai kawai
"Allah ya bada iko ya taimaka..."
Ya fadi, ko amin din a zuci Rayyan ya fadeta ya raba Haris din yana wucewa daki. Ya guji jami'ar bayero saboda Abbu da tarin abokan shi da yake da tabbacin ba za'a rasa a duk wani fanni da zai nemi gurbin karatu ba. Duk da Abbu din yana bangaren lissafine. Amman yana da matsayi a makarantar da ko da mu'amala bata hadaka da shi ba, yasan kasan sunan shi, kasan kuma ko waye shi. Baya bukatar wannan attention din na mutane, da ma ace Abbu zai shiru da bakin shi, yanda yake alfahari dasu ba zai barshi yaki nuna cewa shi din ba nashi bane ba.
Kowa zai dauki ido ya saka mishi, wasu da yawa zasu dinga tsammanin gaisuwa daga wajen shi a duk haduwar da zasuyi. Ba zai iya wannan rayuwar ba. Yanzun ya tsallaka Zaria ma, Haris yasa shi harya fara dana sani. Dadin shi daya kawai, Bilal yace shima nan din zai nema
"Na dauka Bayero kake so, saboda ka burge Abbu"
Kai kawai Bilal din ya jinjina yana furta
"Kana da matsala"
Ya fita ya kyale shi. Har ran shi daman yaso ya roki Bilal din daya zo ABU shima, tunda har ya hango yanda zaiyi rayuwa a makarantar shi kadai. Tunda yana da yakinin ba zaiyi aboki ko daya ba, watakila sai dai iya gaisuwar cikin aji idan ta zama dole. Yana lissafin yanda da wahala ya iya hada satika hudu cikakku bai shigo Kano ba, har kasan zuciyar shi yake jin yanda zaiyi kewar Bilal din
"Har da Layla"
Wani bangare na zuciyar shi ya fadi a lokacin, zai kewar ganin ya sakata kuka. Yana da wannan tabbacin, amman bayajin tana cikin dalilin da zai sashi zarya tsakanin Kano da Zaria duk bayan wasu yan kwanaki. Sai bayan da Bilal yace zaije Zaria. Sai yaji son yazo duk bayan wasu kwanaki sunki fita daga kan shi, ya fadama kan shine zai dinga zuwan ne kafin Bilal ya sami gurbin karatu. Idan ya samu kuwa watakila sai hutun karshen zango na watanni shidda.
Yunwa yake ji, ko abincin rana baici ba, yasan da gangan Bilal yaki shigowa dakin. Saboda sunyi fada da rana, shine dalilin da yasa ma Rayyan ko yunwa baiji ba, ran shine ya baci. Bilal yafi kowa sanin yanda yake da saurin hawa haka yake da saurin sauka, amman sai suyi fada wani lokacin shi ya gama fushin Bilal yana mishi fisge-fisge. Daya shigo zai zubo musu abinci su dukan su, da Ayya na aiko musu da shi, Bilal ya koyi kinibibin zuwa ya zubo. Sai Ayya ta daina turowa a fada musu ta ma gama abinci ko da suna jin yunwa in bata bayar an kawo ba.
Tunda idan aikowa tayi zai saka dan aiken ya karbo mishi. Abinda bai sani ba shine Ayya ta daina ne saboda shi, saboda wannan yunwar ce kawai dalilin da yake saka shi shiga bangaren ta wani lokaci harta gan shi, tana iya aikawa a kira shi a dawo ace mata an kwankwasa dakin shiru, idan Bilal yana nan kuma yace a shiga, an shiga an same shi yana bacci. Idan ya tashi kuma ko an fada mishi ba zuwa yake ba wasu lokuttan, sai ta taka har dakin da kanta ta mishi tas, shima sai dai yaita kallon ta ko yace
"Ni na manta ne Ayya"
Shisa take kyale su, wanda duk yunwa ta dama yasan inda zaije ya dibi abinci. Tashi yayi yana saka takalman shi da suke bakin kofa ta cikin dakin yana ficewa. Ya karya kwana kenan da nufin shiga bangaren Ayya ya hango Layla. Sai da zuciyar shi ta doka
"Subhanallah..."
Ya furta kasan makoshin shi, tana karasowa ta zabi ta sauke idanuwanta cikin nashi. Duk fadin wajen sai a cikin nashi idanuwan ne zata nemawa nata masauki
"Mayya..."
Ya fadi yana kallon yanda ta kara ware mishi idanuwan
"Me yasa ba zanzo waje ba sai kinsan yanda kikayi kika biyoni?"
Kallon shi takeyi, duk ranar bata saka shi a idanuwanta ba, asalima tun jiya da rana rabonta da shi. Har rigar shi daya bata guga ta shiga taje ta kai mishi baya nan. Islamiyya da zata fitane da kuma kashedin da yayi mata na da yamma zai saka rigar yasa ta bude dakin ta ajiye mishi rigar. Da ta bari ya dawo ta gan shi tukunna. Tana da mukullin dakin su, da hannun shi wata rana ya kama hannunta ya saka a ciki
"Idan ya bace saina karya ki Layla"
To wani lokacin yakan sa ta share musu dakin, ko idan ya aiketa yace ta kai mishi daki. Duk da idan tayi shara sai ya maimaita, wata rana ma bayan ta gama zai kai mata duka ya karbi tsintsiyar
"Kina mace baki iya share waje da kyau ba, fita kafin in kwada miki mari..."
Dalilin ya daketa kawai yakan nema tasani, shisa yake sakata shara, ko son ya wahalar da ita, tunda sai ya maimaita, da wanki ma idan ya bata tana kawowa ya jujjuya zai nade rigar ko wandon ya lafta mata
"Haka ake wanke kaya? Banda maita zuwa duk inda nake me kika iya a rayuwar ki?"
Yakan sata ta dibo ruwa a bokiti ya kara tsoma kayan ya wanke, ya bata ta shanya, wata rana ma tana tsaye tana kukan dukan da yai mata. Yanzun ne ma zata wanke mishi kaya wata ran baya ko duba hannuwan, wuyan rigar da wajen aljihun. Yake karba ya ajiye. Ta dai rasa dalilin da duk wahalar da take sha a hannun Rayyan haka kawai wani lokacin idan ta dauki wasu awanni bata ganshi ba sai taji tana son ganin shi. Da ta ganshin kuma zai fita daga ranta, saboda sai ya fada mata maganar da zataji tayi dana sanin son ganin nashi.
Har lekowa tayi dazun, bata gan shi ba ta koma, sau biyun da aka leko akayi mata magana a daki sai da taji gabanta ya fadi, tana mikewa da sauri zaton ta shine ya aiko a kirata, sai taji wani abu kamar dissapointment a lokutta biyun da kiran ya kasance ba daga shi bane ba. Yanzun ma shanya uniform dinta da ta wanke ta fito yi a igiyar dake bayan bangaren nasu, tana sane ta zagayo ta nan, da fatan ko zata ganshi a ranta, saboda tun dazun take tunanin ko bashi da lafiya, ko wani ya bata mishi rai shisa yayi shiru da yawa haka.
Tana hango shi wani murmushi ya kwace mata, murmushin da tayi kokarin boyewa daga kan fuskarta, murmushin daya dishe gabaki daya bayan kalmar shi ta
"Mayya..."
Da ya jefeta da ita. Badan bai saba fada ba, itace ta kasa sabawa har yanzun, sosai kalmar take mata zafi, musamman idan daga bakin shi ta fito, tana jin maganar da take son mayar mishi na mata kaikayi akan harshe. Amman sai ta zabi yau da taqi biye mishi. Ta juya kenan yace
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.