Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 90 of 125
A tsorace yake, tsoron da ya saka shi tunanin akwai sauki mai girman gaske a tattare da mutuwa, wani tsoron na daban yana kara bugar shi, saboda hango kwanciyar kabarin shi da yake cike da kokwanto da yayi, a da laifukan shi yana jin tsakanin shi da Allah ne, yanajin suna da sauki mai girma saboda Allah Mai Rahma ne. Amman yanzun laifin shi nacin amana ne, kuma bayason fara tunanin makomar masu cin amana. Bayaso sam, gabaki daya jin shi yakeyi a gigice kamar zai shide
"Matsa mun Bilal..."
Abbu yayi maganar da wani yanayi da Bilal bai taba ganin shi a ciki ba, kai Bilal yake girgizawa
"Abbu ni ne, ni ne Abbu"
Ya furta a razane, saboda ba zai tuna ranar karshe daya ga Abbu ya dagama wani daga cikin su hannu ba, amman a idanuwan shi yake ganin inda abun duka a kusa da shi yau zai saka shi ya jibgi Rayyan din, ba zai kara wani laifi ba, bayan cin amana ba zai shiga tsakanin mahaifi da dan shi ba, ba zai iya kara daukar wani tashin hankalin ba, kamar zai fashe da kuka yake kara fadin
"Ni ne Abbu"
Kai Ayya ya dafe, hawaye masu zafi na zubo mata, Mami ta kalla, duk ita ta shigo rayuwar su, ta shigo musu da Layla har suka zo inda suke din nan yanzun. Bilal take kallo da gabaki daya ya rikice, tun tasowar su, ko Rayyan zata daka haka yake shiga tsakani, ko da zata rufe ido taci gaba da kai duka ba zai matsa ba, zai amfani da jikin shi ya kare na Rayyan din yana kuka yana bata hakuri. Akwai tarin lokutta da tasan Rayyan ne yayi laifi amman Bilal din zai dauka. Shine yake faruwa a gaban idanuwanta yau, amman ba zata bar shi ba, ba zata kyale shi daukar wannan laifin ba
"Karya yake, ya saba Ahmadi, ya saba daukar laifin Rayyan"
Ayya ta karasa da wani yanayi, kanta sarawa yake ta kowanne bangare, tana tunanin rashin amfani na Malaman duk da tayita asarar kudinta a kansu, duban su da bugun kasar su ya tashi a banza da suka kasa hango mata wannan tashin hankalin, da basu fada mata ko da bata iya kauce mishi ba tasan yanda zata karbe shi tunda wuri, hawan jinin da bata da shine yake son kamata lokaci daya
"Bilal ka matsa kafin in wanke ka da mari kaima"
Cewar Abbu, jiri yake gani sosai zuwa yanzun, amman so yake Bilal ya matsa ya kara ganin Rayyan
"Abbu wallahi ni ne"
Wani murmushi mai ciwo Abbu yayi
"Karyar ce kake bi da rantsuwa Bilal? So kake in yarda da kai haka?"
Kan shi Bilal ya sadda kasa yana rasa inda zai saka ran shi yaji sauki-sauki. Komai ya cunkushe mishi, yana ganin Abbu ya juya ya fara takawa, sai dai ko taku biyu baiyi ba ya yanke jiki ya fadi. Kan shi sukayi gabaki dayan su cikin karaji banda Rayyan da Layla, shi yana nan tsaye inda yake, yana rasa kalar tunanin da yakeyi ko ya kamata yayi. Layla kuma tashin hankali ne ya sake dirar mata, shikenan ta kashe mutum daya da ya karbeta a lokacin da kowa yakita, mutumin da bai taba sakawa taji maraicin da take tare da shi ba. Kuskure daya ya canza mata komai.
Bilal da Jabir ne suka kama shi suna yin dadin Ayya da shi, dan tunanin asibiti baizo musu ba. Jabir ne yayi tunanin samo ruwa ya shafama Abbu a fuska kafin ya bude idanuwan shi yana kokarin mikewa
"Abbu faduwa kayi fa, ka kwanta dan Allah"
Jabir yayi maganar kamar zai saka kuka, baisan tashin hankali ba duk tsayin rayuwar shi sai yau. Ko abokai ne in ka nemi daga mishi hankali zaka neme shi ka rasa ne. Sam baya zama, shisa abin yake tabashi sosai da sosai.
"Idan na kwanta ba zai canza komai ba Jabir, kabar ni in tashi in fuskanci matsalar nan"
Mikewa Bilal yayi, ba zai iya dauka ba, zuciyar shi ba zata iya dauka ba sam. Ficewa yayi daga dakin zuwa nasu. Rayyan kuwa yana inda suka bar shi, Layla yake kallo har su Mami suka bi bayan su Bilal suna barin su kadai a wajen
"Hamma"
Layla ta kira tana son ya taimaka mata, ko da zai zama lokaci na karshe a tsakanin su, ya taimaka ya fahimce ta, saboda tasan babu wanda zai taba fahimtarta. Yanzun a kan idonta taga rashin yarda a idanuwan kowa kan cewa cikin na Bilal ne, kowa yaki yarda, tana kuma ganin katanagar da Rayyan yake ginawa a tsakanin su, idan ta bude bakinta, idan ta fada musu cikin na Bilal ne duka zasu yarda, dole zasu yarda. Amman idan suka ce ta auri Bilal fa? Tunanin kawai ya girgiza duka ilahirin zuciyarta balle ya kasance ya tabbata, da gaske mutuwa zatayi idan ta rasa Rayyan.
Watakila tana da sauran rabon zama da Rayyan shisa yaki musa cikin jikinta ba nashi bane ba, so take ya bude bakin shi yayi mata magana
"Hamma"
Ta sake kira, dafe kan fuskar shi Rayyan yayi da hannuwan shi duka biyun, yakai mintina biyu a haka kafin ya bude su akanta, a karo na farko yana tsintar kan shi da kin son ganinta. Har a zuciyar shi bayason ganinta
"Dan Allah Hamma..."
Ta fadi cikin kuka, kai Rayyan yake girgiza mata
"Bana son ji, koma menene, ba zai canza komai ba Layla"
Ya karasa yana juyawa, baisan yana cikin tashin hankali ba saida ya karya kwanar da zata kai shi dakin su yaji kafafuwan shi sun kasa daukar shi, a wajen ya tsugunna ya dafe kirjin shi yana jin kamar zai rabe gida biyu. Bude bakin shi yayi yana fitar da numfashi saboda ta hancin kofofin sun toshe mishi, cikine a jikin Layla. Yaron wani ne yake rayuwa a jikinta, yaron da ba na shi ba. Layla, Laylar shi ake magana a kai ba wata ba. Waye zai musu wannan abin? Waye zai taba mishi ita haka, runtsa idanuwan shi yayi yana kuwa bude su babu shiri saboda kazantar hoton daya hasaso cikin kan shi.
Koma wanene tare da Layla suka ci amanar shi. Abin da yafi tsana a rayuwar shi, ya bude baki ya fada mata yana son ta, Layla da ya dawo da burin fuskantar kowa da sunan soyayyarta ce da dan wani a cikinta. Bangon wajen ya dafa ya samu yana mikewa, so yake ya karasa daki ya kwanta, jiri yake gani a tsugunnen ma. Dakyar ya iya mikewa yana shiga dakin su inda ya samu Bilal a tsaye
"Zuciyata zata fashe Bilal, kirjina ciwo yakeyi"
Rayyan ya fadi, in bai gayawa wani ba da gaske zuciyar shi fashewa takeyi. Bakin shi ba zai iya shiru a gaban Bilal ba, wannan abin ya mishi girma ya dauka shi kadai, so yake a lallashe shi, kamar karamin yaron da yayi mummunar rauni haka yake ji, a hankali Bilal ya juyo yana sauke idanuwan shi akan Rayyan da yake fitar da numfashi kamar mai ciwon asthma. Shima yana gab da fara fitar da numfashi ta wannan sigar idan wani bai yarda dashi ba, idan bai fadama wani laifin shi bane, saboda shi kowa yake cikin rudani, tashin hankalin zai mishi yawa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.