Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 59 of 125

Itama Layla a nata bangaren hakane, in da tasan yanda zata daina tabashi da tayi, ko dan yanda taga hankalin Mami ya tashi, amman bata sani ba, Mami take roko da ta yafe mata, ta fahimci ba laifinta bane, soyayya ce take rinjaye akanta a kowanne lokaci, zuciyarta take riritawa fiye da martabar ta da Mami take yawan kira mata a duk wayar da zasuyi. Ta dai ji tsoro na fitar hankali randa Bilal ya sameta har hostel bayan ya kirata yana fada mata magana yake so suyi, bata kawo komai a ranta ba sai bayan sun sami wajen zama ya fara da cewa

"Ban san ta ina zan fara ba, na dai san tuntuni ya kamata in miki magana, in muku magana, sai na zabi in yiwa Hamma duk da nayi a kurarren lokaci, nayi kokarin gyara kuskuren yaki..."

Sai lokacin zuciyarta ta fara bugawa sosai da sosai, musamman da Bilal yaci gaba da fadin

"Abbu ya bani amanar ki, Abbu yace in kula da ke, na kuma mishi wannan alkawarin. Gashi na kasa cikawa, ranar farko da na ga kin rike Rayyan ya kamata in tsawatar miki, banyi ba. Kin san illar hakan, kin san rashin kyautuwar hakan Layla...ban san ya zan miki fada ba, amman zan rokeki, idan ina da wata daraja a idanuwan ki zaki bari, zaki jini tunda shi yaki jina"

Lokacin idanuwanta sun cika taf da hawaye, sai da ta saka su cikin na Bilal kafin hawayen nata su zubo

"Ina son shi.. Hamma Bilal ina son shi"

Ta fadi da dukkan gaskiyarta, a karo na farko tana furtawa wani soyayyar da takeyiwa Rayyan din. Cikin sonyin amfani da ita dan ta zame mata hujjar da zata isa ta bata damar rike shi, tana kallon yanda Bilal din yake fitar da numfashi a hankali kamar yana cikin tashin hankali, sai dai itama a cikin shi take

"Shi sa zaki daina, saboda kina son shi. Ba zaki so yaci gaba da tarawa kan shi zunubi ba"

Bilal ya fadi cike da son ta fahimce shi, kai t girgiza tana mikewa kawai tabar mishi wajen. Kuka tayi sosai ranar, da wayarta tayi kara ko bata kira ba sai gabanta ya fadi, sai tayi tunanin ko Bilal din ya kai karar su gida ne. Bata san me kuma zata cewa Mami bayan karyar da ta shirga mata na cewa Rayyan din baya kulata ba. Kuma da alama Mami ta yadda, bata dai fasa jaddada mata muhimmanci kare martabar ta ba. Kamar yanda itama bata gaji da amsa ta da

"In shaa Allah"

Ba, bata san ya suke so tayi ba, daga Bilal din har Mami, da alama basu san yanda soyayya take ba, basu san yanda duk lokacin da wanda kake so yake a kusa da kai baka muradin komai banda kaji ka rike shi koyaya ne, ka kara hada kusancin da kake ji. Musamman idan wanda kake so din Rayyan ne, Hammanta da emotions sukewa wahalar nunawa, Hammanta da bata da tabbacin zai furta mata wasu kalamai da suka danganci soyayya. Amman idan yana jinta a jikin shi sai take ganin a hankali zata raunana zuciyar shi, zata saka kalaman da take son ji su kubce mishi.

Balle takan karanta girman tasirin mace a wajen namiji, ko sarki ne akan ce a gaban mace shi din bakomai bane. Zuwa yanzun kuma tasan kalar halittar jiki da Allah yayi mata, maza da yawa a makarantar idanuwan su a kanta suke. Bata da wani makami akan Rayyan banda jikin da shima duk baudadden halin shi taga yana so, ko hannun shi ta rike tana kallon yanda yake sauri ya dumtse shi cikin na shi kamar yana tsoron karta subuce mishi. Bilal da Mami ba zasu gane wannan bace kawai hanya daya da zata iya mallaka mata Rayyan.

Tana ganin yanda Bilal ya kalleta bayan kwana biyu da rokon shi, yanda ta hada ido da shi cikin ban hakuri kafin ta rike Rayyan din. Sai mikewa yayi yana bar musu wajen

"Hamma Bilal zai fadinma Abbu bamu daina ba"

Layla ta furta muryarta na rawa tana dorawa da

"Ya mun magana, yace in daina rike ka, Hamma ban san ya zan fada mishi ya gane ba. Dan Allah kayi mishi magana karya fada a gida. Saboda Mami"

Sake riketa Rayyan yayi a jikin shi, shima din baisan ya zai fadawa Bilal ya fahimta ba, shisa bai taba amsa shi ba. In da zai iya daina rike Layla din daya bari ko dan yanda Bilal yake mishi tashin hankali a kai. Amman bai sani ba, sam baisan yanda zai fara bari ba. Hakan zaiyi dai-dai da nisa da yar natsuwar da ya samu. Yana bukatar wannan natsuwar, tana daya daga cikin katangar da take tsakanin shi da tabin hankalin da yakan ji a kurkusa wasu lokuttan. Haka suka rarrafa sukayi watanni shiddan daya kawo su inda suke tsaye yanzun.

Dan Layla tafi awa biyu a tsaye gaban ajin su tana jiran Rayyan din ya rubuta jarabawar shi ta karshe a ranar ya fito. Kuma da alama bai tsammace ta ba, tana rike da shi din tace

"Congratulations..."

Dan murmushi yaji yana shirin kwace mishi, lokacin daya kama hannunta yana zagayo da ita, kewar shi take ji tana tunanin yanda makarantar zatayi mata fadi idan baya ciki, amman zata danne komai yau ta taya shi murnar kammala makarantar shi lafiya. Wani dan ajin su ta gani yazo wucewa da rigar da daliban da suka kammala karatun su kan saka dan a dauke su hoto, kuma ya kalleta har da dan murmushin shi

"Ko zan iya aron rigar hannun ka na yan mintina dan Allah?"

Murmushin shi ya fadada, yana mikawa Layla da take mishi kallo cike da godiya, tana saka Rayyan kama dayan hannunta ya rike yana ma saurayin wani irin kallo

"Na san yarinyar ka ce"

Saurayin ya fadi yana wuce su. Duk wanda yake a ajin su Rayyan din, koma department din yasan shi da Layla, wanda suke burgewa da yawa, wanda kuma suke zagin su ma haka. Wasu na musu kallon masu dace a soyayya, wasu na musu kallon tantiran marassa kunya. Duk da haka rayuwa take tafiya, mutane basa taba rasa abinda zasu fada a kanka. Balle kuma Rayyan da Layla da suka basu abin magana a kai, a gaban kowa suke rike juna kamar su ka daine a filin wajen, kamar ba yaran hausawa tarbiyyar musulunci ba.

"Ni fa ba zan saka ba"

Rayyan ya fadi yana kallon rigar hannun Layla din

"Dan Allah Hamma... Dan Allah"

Take furtawa tana jan hannun shi da nata yake ciki, bai musa ba yake binta, basu kai da barin wajen ba Bilal ya karaso, hannun Layla da yake cikin na Rayyan din yabi da kallo, shima a watanni shiddan nan duk yayi zuru-zuru. Abinda wasu zasu alakanta da karatu, kusan harda karatu, amman baifi kaso ashirin ba, tamanin da doriya Layla da Rayyan ne. In da zai iya bude bakin shi ya fadawa Abbu a tsawatar musu zaiyi, amman wata murya na fada mishi kishine yake saka shi wannan tunanin ba girman amanar da Abbu ya bashi ba.

Sanda duk zai ga Rayyan da Layla a tare, tana mishi murmushin nan kamar zata iya tsayar da duniyar kacokan domin Rayyan idan tana da damar haka sai wani abu ya bude a kirjin shi. Amman ranar da yaji kamar kirjin nashi ya rabe gida biyu shine ranar fa ta saka idanuwan ta cikin nashi tana fada mishi yanda take son Rayyan, tana maganar kamar shine dalilinta na rike shi, dalilinta na komai. Har jiri yakeji sanda ya karasa gida, daren ranar salloli ya kusan kwana yanayi, bai san da gaske soyayyar Layla a zuciyar shi mai girma bace sai da yaga digar hawaye a cikin sujjadar shi yana neman sauki a wajen wanda ya halitta mishi zuciyar har ya darsa bugunta da soyayyar Layla.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.