Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 97 of 125

Ba don ya yarda da kalaman Rayyan din ba, ya dai yi tsaye ne har sai da ya daina ganin Rayyan din da ya nufi dakin su. Kayan da Bilal ya baza ya fara harhadawa, watakila yabar wani abu da ko yane zai nuna alamar inda ya nufa, amman harya gama hadasu baiga komai ba. Gefen gadon ya zauna yana rasa kalar tunanin da ya kamata yayi, kafin wani abu cikin kan shi ya fada mishi baiyi sallar asuba ba. Alwala kam dan sabo ne shisa ya cikata dai-dai. Lokacin daya idar da sallah, bai san ta inda zai fara addu'a ba ko abinda zai roka, kawai yana rokon Allah Ya duba halin da yake ciki ya karbi sallar da yasan bashi da wadatacciyar nutsuwa a lokacin daya gabatar da ita.

Baisan iya lokacin daya dauka a zaune ba, rurin da wayar shi takeyi ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da yakeyi. A hargitse ya mike yana rasa inda zai gano wayar, har ta yanke tana sake daukar ruri

"Dan Allah ina dubawa ne Bilal, nasani, ni nasan babu inda zaka tafi ka barni"

Rayyan yake fadi yana cigaba da neman wayar kafin ya juyo ihunta cikin jakar shi da ko budeta baiyi ba. Lalubo wayar yayi, kafin ya daga ta sake yankewa, budewa yayi yana kallon lambar hadi da nazarin inda ya taba ganin ta, ko ma a ina ne yasan lambar, kafin a sake kira, bai tsaya jira ba ya daga wayar yana karawa a kunnen shi

"Hamma..."

Muryar Aisha ta daki kunnen shi tana saka zuciyar shi matsewa a cikin kirjin shi, kafin ya amsa ta dora da fadin

"Hamma ina Nawan? Sakon shi nagani yanzun, bansan ko ya yarda wayar bane, saboda na kasa fahimtar duka zantukan da yakeyi"

Runtsa idanuwan shi Rayyan yayi, akwai wani yanayi tattare da muryar Aisha da yake kara bude bangarori da dama a cikin zuciyar shi

"Dan Allah ka fadamun...kai mun magana"

Sai da ya bude idanuwan shi sannan ya iya cewa

"Ina kike tunanin idan Bilal ya bar gida zai je?"

Ta kusan mintina uku kafin ta amsa shi, muryarta na fitowa a karye

"A watan nan yana yawan maganar kasancewa a wajen da kowa bai san shi ba, yana fadin Lagos ne kawai zakaje ka bace bat... Ban sani ba, ban san me yake faruwa ba, me yake faruwa Hamma? Me yasa zai tafi?"

Ta karasa maganar ne da alamar kukan da ya kwace mata, ba shi da amsar da zai bata, ba kuma shi da wasu kalamai da zai tausheta dasu, shima yana bukatar lallashine

"Ina zai tafi ya barni? Ta ina zan fara?"

Wani irin numfashi take saukewa kamar wadda aka shaqe

"Zan kiraki"

Rayyan ya fadi yana sauke wayar daga kunnen shi, dan yaji alamar zata kara hargitsa mishi lissafi ne. Yana da abubuwa da yawa a gaban shi. Mikewa yayi yana saka wayar a aljihun shi, sai da ya karasa bakin kofa sannan yayi tunanin saka takalma a kafafuwan shi, tashin hankali bai barshi yaji kasar da yake ta takawa ba yau. Yana fitowa daga daki yaci karo da Abbu

"Abbu zan duba a tasha, ina motocin Lagos suke lodi? Aisha tace Bilal yana maganar zuwa can ne"

Kai Abbu yake jinjina ma Rayyan, gabaki daya ya rasa abinda zaiyi tunani. Duniyar ta birkice mishi, yaran da yake tunanin yana duk wani kokari da yake karkashin ikon shi dan kare sune yake kallo yau kaddara na aikinta a kan su babu abinda zai iya. Bilal ne ya dauki kafar shi yabar gida yau, Bilal da gabaki daya rayuwar shi zagaye take da tasu, shine yau ya nufi inda baisan kowa ba, ya ture komai ya tafi saboda yana tunanin yayi musu wani laifi. Wani irin tsoro Abbu yake ji yana shigar shi, Rayyan yake kallo, yana tuna kalaman da yayi mishi jiya na yabar gida

"Ko da zan taba ce maka kabar mun gidana, karka tafi ko ina, kalaman ba zasu taba fitowa daga zuciyata ba"

Abbu ya fadi yana dorawa da

"Bari in dauko mukullin mota sai mu tafi"

Anan inda yabar Rayyan ya dawo ya same shi, sun karasa wajen motar ne Yaya Ayuba ya shigo, ko gaisawa ba suyi ba ya fara da tambayar

"Lafiya? Ina zaku je da sanyin safiyar nan?"

Abbu na bude murfin mota ya amsa shi

"Bilal ne ya bar gida, Rayyan yace kamar Lagos ya nufa. Shine zamu duba a tasha mugani"

Karasawa Yaya Ayuba yayi yana karbar mukullan motar daga hannun Abbu batare da yace komai ba. Shiga sukayi, Rayyan na bude gidan baya ya shiga. Da yake Yaya Ayuba yasan duk tashoshin da motocin Lagos suke lodi. Tunda kafin ya samu budin hawa jirgi idan tafiya kudu ta kama shi motar hayar yake bi. Rayyan ba tuqi ya iya ba, amman gani yake kamar Yaya Ayuba baya taka motar da sauri, saboda so yake kawai su karasa yaga Bilal din yaji dalilin da zai sa ya fara tunanin barin su.

Kudi Kawu Ayuba ya bama cikin yan kamasho na tashar, kafin kace wani abu an dauko musu wani babban littafi da jerin sunayen mutanen da suka hau motocin Lagos daga daren jiya zuwa wayewar gari, motocin safe. Amman ko daya babu sunan Bilal a ciki, duk da Rayyan yaki aminta, wanda ba shi ya duba ba da kan shi sai da ya karba ya sake dubawa, tashoshi suka dinga bi har wajen karfe tara na safe, saboda duk inda sukaje sai sun tsaya an duba list sannan suke barin wajen. Suna hanyar nufar wata tashar da akayi musu kwatance, wayar Rayyan ta fara ihu, bai bi ta kanta ba harta yanke, saboda wani abu na fada mishi ba Bilal bane ba.

Sake kira akayi, ko waye ma bai hakura ba a karo na biyu, ya sake kiran a karo na uku

"Rayyan ba wayar ka bace take kara?"

Yaya Ayuba da yake tuqi ya tambaya, Rayyan din bai amsa shi ba, dan daga jikin shi yayi yana zaro wayar daga aljihun shi, dubawa yayi yaga ko Aisha ce, dan bashi da wata magana da zai fada mata, da akwai daya kirata kamar yanda yai mata alkawari. Wata lamba ce yagani daban, karamin tsaki yayi yana shirin saka wayar a silent kar a dame shi aka sake kira, dagawa yayi ya kara a kunnen shi yana fadin

"Waye?"

A hasale, ta dayan bangaren aka furta

"Daga tashar Mass ne, mun dauki lambar cikin lambobin da daya daga cikin fasinjan da motar su ta tashi karfe hudu na safiyar yau daga nan Kano zuwa Lagos ne mai suna Bilal Abdullahi Dikko..."

Zaman shi Rayyan ya kara gyarawa yana kai hannu yana wuyan rigar shi da haka kawai yaji kamar ya shaqe shi

"Ni ne, ina Bilal din?"

Ya furta a kagauce, dan jim yaji anyi cikin yanayin da ya saka shi fadin

"Hello, ina Bilal din? Wacce unguwa tashar taku take?"

Yana kallon Abbu ya juyo da jikin shi gabaki daya daga gaban motar yana fuskantar shi

"Bilal ne ya bada lambata a tashar shine suka kira ni"

Ya tsinci kan shi da fadama Abbu daya sauke wani numfashi da baisan yana rike da shi ba, Rayyan kuwa hankalin shi ya mayar kan wayar jin har lokacin ba'a kara cewa komai ba, ya bude baki zai magana yaji muryar mutumin ta daki kunnen shi da wata iska mai karfin gaske

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.