Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 13 of 125

Haka takanji ana fadi, tana kaunar Deeni har ranta, bata son abinda zaizo ya cutar dashi sam.

"Ke dai kiyimun fatan alkhairi kawai"

Deeni ya fadi yana dariya, sai gashi daga baya kowa na yabon kirkinta. Cikin kankanin lokaci ta shiga zukatan jama'a. Maryama da kowa sun alakanta hakan bayan rasuwar Mannira mintina kadan bayan haihuwar 'yarta mace. Mutuwar ta daki Deeni ba kadan ba, har akayi jana'iza baisan inda kan shi yake ba. Kowa ya budi baki ca yakeyi rabone kawai ya hada kaddarar Mannira da Deeni, shisa duk yanda akaso hana shi aurenta yaki ji, ashe ma zaman nasu bamai tsayi bane, tunda duka watannin su sha hudu. To lokacin ne tafiyar da tayi mai tsayi, shekaru kusan biyu kenan da suka wuce.

Lokaci zuwa lokaci takan yi tunanin yarinyar, saboda tun a wajen rasuwa kowa ya kalleta sai yayi magana kan kalar idanuwanta. Tasan ba kasafai ake samun irin idanuwan a cikin mutane ba, musamman anan yankin Najeriya. Amman sai take ganin gara idanuwan yarinyar da taci suna Layla akan na wani bawan Allah data taba gani, har gobe ko ita kadai ta tuna sai tsikar jikinta ta tashi, saboda sak kalar idanuwan miciji, sai da tayi zaton ko tayi gamo ne. Ahmadi yaita mata dariya, yake cewa a wajen aikin su akwai wani bature nashi idanuwan kalar ganye, koraye ne sosai. To ita kam gara mata bature, wannan ba abin mamaki bane, amman a jikin bakar fata, dole abin ya girgizata.

Shisa da taga Layla ta kara jinjina ma Ikon Allah, dan Shi ya banbanta halitta a tsakanin mutane, bata da kalar da zata misalta idanuwan Layla dashi, ko kyanwa kowacce da kalar nata idanuwan. Amman tabbas ta wata kyanwa kawai ta taba gani da kalar idanuwan yarinyar. Kalar surutun da akeyi tun a wajen rasuwar Mannira, sam Maryama ba zaci za'ayi bakwai yarinyar bata bi mahaifiyarta ba. Tun tana tsammanin bayan dawowar su labarin rasuwar Layla zai iso musu harta daina.

Yau dinma har tasha Ahmadi ya rakata, da yake kwana biyu zatayi, daga ita sai Marwan ta taho. Sauran yaran tabar su wajen Maimuna da fuskarta babu yabo babu fallasa tace mata

"Allah ya tsare, ki gaida su"

Da tayi mata sallama, babu wani abu da zatayi da Maimuna zata zauna lafiya da ita. Shisa yanzun inta gaya mata maganar da taji ba zata iya dauka ba, ramawa takeyi. Yaranta ne kawai ta kula Maimuna na budewa hakora, kishinta sai yazowa Maryama da sauki tunda bata saka yaran a cikin rashin jituwar su. Hankalinta kwance tabarsu a gida, suma basu damu ba tunda ko unguwa zata fita a gida takan barsu. Ranta kal tanata kallon gari har suka isa kankia.

Furaira uwargidan Deeni ta karbeta hannu bibbiyu, ta sauketa kamar yanda ta saba taryar su, shisa kowa a danginsu baya gajiya da fadar alkhairinta. Sai dai ta girgiza matuka da ganin dan uwan nata, damuwar da take shimfide akan fuskar shi mai yawa ce, duk da murmushin da yake mata da suke gaisawa, tana ganin yanda bai kai cikin idanuwan shi ba. Tunda ta isa ta jima bata ga giccin Layla ba, kafin daga baya yarinyar da take bacci ta taso ta fito. Farat daya Maryama tajita har cikin ranta, sai bayan Furaira ta basu waje da Deeni ne ta samu damar tambayar shi me yake faruwa, murmushin da yayi mai ciwone matuka.

"Bana jin dadin tsangwamar da Layla take fuskanta daga wajen mutanen kauyen nan. Ko unguwa Furaira ta rage fita sai dole, tana iya kokarinta, amman ko taro ta shiga da Layla sai iyaye su fara janye yaran su, babu wanda ta taba cutarwa, bansan me yasa suke alakantata da maita ba. Dan Allah ya banbanta kalar idanuwanta da nasu sai suke dora alhakin hakan akan Mannira, suna zantukan da bana son maimaitawa...."

Deeni ya karasa maganar yana sauke ajiyar zuciya

"Wallahi a kwanakin nan ina tunanin mayar da ita hannun Inna...."

Kai Maryama ta jinjina mishi, zancen na taba zuciyarta fiye da tunani

"Allah ya kyauta ya rufa asiri, rashin ilimi cuta ce babba a tsakanin al'umma. Zan tafi da ita idan zan wuce, nasan Ahmadi ba zaiki ta zauna a hannuna ba, amman kaga ba zai yiwu inje mishi da zancen kai tsaye ba"

Kai Deeni yake girgiza mata tunda ta fara magana

"Karki dora mishi dawainiya, ga nashi yaran"

Murmushi Maryama tayi

"Babu wata dawainiya, indai zai amince in riketa, ina da sana'ata ko ka manta? Ba wani abu nakeyi da kudadena ba. In shaa Allah rike Layla ba zaimun wahala ba. Amincewar ka itace komai na"

Numfashi Deeni ya fitar mai nauyi

"Ni dai ina so ta tashi inda babu tsangwama, inda wani ba zai lakaba mata maitar da batada ita ba..."

Kusan har karfe dayan dare suna shan hirar yaushe rabo da Deeni. Taji dadin damuwar da taga ta ragu a idanuwan shi kafin ta baro garin Kankia tare da Layla, wannan karin da tunani fal a zuciyarta, har ranta take jin kaunar yarinyar, ko dan Allah bai bata 'ya mace ba har yanzun, kuma tana so, inda wani zaman kirki suke da Maimuna ba zataki ko Rukayya ko Zubaida wata ta dawo dakinta gabaki daya ba, musamman tunda yanzun Maimuna goyon mace takeyi, yarinyar da aka mayarwa sunan mahaifiyar Maimuna suke kuma kira da Intisar.

Amman abune da tabar shi a zuciyarta, tunda tasan furta shi matsala kawai zai janyo mata. Addu'a takeyi Ahmadi yabarta ta rike Layla. Harta isa gida, inda bata sami kowa ba cikin yaran gidan, tasan babu Islamiyya tunda ranar Alhamis ce, suna gidan Yaya Ayuba, tunda basu da wajen shiga daya wuce nan din. Daki ta wuce kanta tsaye tunda dai tasan Maimuna ba fitowa zatayi dan ta taryeta ba, ga jigatar hanya, saboda daga Marwan har Layla bacci suketa shirga, shi ta goyashi, Layla kuma tana sabe da ita, ga kayan su ga tsarabar da aka hadota da ita.

Banda nishi babu abinda take dirkawa, fitowa tayi tsakar gidan da nufin yin alwala, in tayi sallar la'asar ko da taliya ce sai ta dora musu, tana da dakakken yaji, yunwar da take ji ba zata jira wata miya ba ko da tana da cefane. Ta idar da alwalar kenan ta shiga daki taji sallamar Zubaida

"Mami sannu da zuwa"

Zubaida ta fadi tana ajiye mata kular abincin da take rike da ita hadi da dorawa da

"Gashi inji Ayya..."

Kallon Zubaida tayi da wani yanayi daya girmi godiya shimfide a fuskarta. Ko a mafarki bata tsammaci wannan kirkin ba. Batama sakawa ranta ba

"Kice nagode sosai Zubaida"

Dan murmushi Zubaida tayi tana ficewa daga dakin. Saida ta fara yin sallah tukunna ta gyara zama ta janyo kular gabanta, dambun shinkafa ne sai kamshi yakeyi. Wani numfashi ta sauke tana daukar kular ta mike tsaye. Kitchen ta nufa ta sami filet ta zuba, ta saka mai da yaji ta dawo dakinta. Tas ta cinye ta mayar da ruwa tanayin hamdala, batasan ta gaji ba saida ta kwanta, kuma lokacin Marwan ya zabi ya tashi ya fara damunta da rikicin shi, dole ta kara mikewa tana zuwa ta zuba mishi dambun shima. Kewar su Haris na damunta, amman da yake ba hankali gare su ba ko suzo su duba suga ko ta dawo.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.