Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 66 of 125

"Ungo"

Bude idanuwa yayi, yaga robar ruwa sai irin maganin shi guda biyu a dayan hannun Bappa, jikin shi na kara sabon bari ya mike yana karbar maganin ya watsa a cikin bakin shi hadi da lumshe idanuwan shi, kafin ya sake bude su yana karbar robar ruwan ya kora

"Ka kara mun guda biyu"

Kai Bappa ya girgiza mishi

"Zai rikeka zuwa safe"

Ya fadi yana wucewa ya koma inda ya tashi, abincin shi yaci gaba daci, Rayyan kuwa ya kai mintina talatin kafin maganin ya fara nutsar da shi, rawar jikin da yake ya bari, ya sake gwada kiran su Bilal amman shiru. Wannan karin Bappa da yake kwance akan kujerar cikin dakin yana danna waya ya kalla, a saman damuwar shi tunanin waye Bappa ya darsar mishi, haka kawai ya tsinci kan shi da son sanin waye Bappa?

*

Sama-sama yake jin shi, iskar da yake shaka da fitarwa ma kamar an daureta da zaruruwa haka take shiga kofofin hancin shi. Jin shi yake kamar a cikin wani mugun mafarki da zai farka daga shi ko yaushe. Sai dai kamar ya farka kusan awa daya da ta wuce ko fiye da haka, babu agogo a hannun shi balle ya duba lokaci, ba shi da natsuwar kiyastawa kuma. Amman tabbas ya farka daga abinda ya tabbata ba mafarki bane ba, dumin jikinta ya fara tabbatar mishi da ba mafarki yake ba, kafin ya kara ware idanuwan shi akan fuskarta, wani irin mikewa yayi yana hankadeta gefe tare da fadin

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

A matuqar razane, kan shi ya kalla da yanayinta itama kafin komai ya dawo mishi, ba Aisha bace ba, Layla ce, Layla ce. Wata murya a cikin kan shi take fadi tana maimaitawa. A matuqar gigice ya suturta kan shi, baisan abinda ya kamata yayi ba banda kokarin ganin ta tashi, dabarar ya shafa mata ruwa bata zo mishi ba, haka yaci gaba da jijjigata a gigice har Allah ya dawo mata da hankalinta ta bude idanuwanta akan shi

"Layla ki tashi, dan Allah ki tashi ki karyata mun abin nan, ki ce mun karya ne, ki ce mun ko a mummunan mafarki ba zai faru ba..."

Bilal din yake fadi a gigice, yana girgiza ta, sai da ta kama hannun shi ta ture, jinta take kamar tana yawo a saman gajimare, dakyar taja jikinta tana mikewa, numfashi dakyar take fitarwa lokacin da ta kama skirt dinta tana saukewa, idan tace ga abinda take ji karyane, a fadin duniya babu wasu kalamai a cikin kowanne yare da zasu taba yiwa halin da take cikin adalci wajen fassara shi. Kafafuwanta ta sauko daga kan gadon, tana mikewa taji wani irin abu ya tsirga mata, amman bata da lokacin ririta kowanne ciwone yake taso mata, dakin kawai take son bari

"Layla..."

Bilal ya kira, amman bata kula shi ba, dankwalinta ta dauka tana daurawa. Ta dauki jakarta da mayafi

"Layla..."

Ya sake kira ganin tana shirin nufar kofa a halin da take ciki. Shirun tashin hankalinta yake karanta da yake kara bugun zuciyar shi. Bashi da karfin motsawa balle ya hanata ficewa daga dakin. Tun fitarta bai motsa daga inda yake ba, sai yanzun daya samu yaja jikin shi yana dora kan shi a jikin katifar, idanuwan shi ya lumshe kamar hakan komai daya faru yake jira ya dawo mishi

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Ya furta daga wani lungu na zuciyar shi jikin shi na wani irin bari

"Me zan cewa Abbu? Me zan cewa Abbu..."

Yake fadi kamar wanda ya sami tabin hankali, har lokacin so yake ya tuna lokacin da Layla ta shigo dakin, so yake ya tuna yanda akayi ta hau kan gadon shi, yanda akayi wannan kaddarar ta same su, ko tabin hankali ya fara bai sani ba, tunda ance in kana hauka baka sanin abinda yake faruwa. Saboda in ba hauka yake ba babu yanda za ayi ace wani abu ya faru a tsakanin shi da wata mace daban da igiyar aure bata kulla su ba, balle kuma Layla. Yana da yakinin ko mazinaci ne shi ba zai bi Layla ba, yana mata son da ba zai yarda su kasance a irin wannan yanayin ba.

Hannun shi daya dora kan katifa yaji kamar ya taba wata lema-lema, ba shiri ya dago kan shi yana kallon wajen da hannun shi, abinda yagani na kara gudun zuciyar shi, baisan yanda ciwon bugun zuciya yake ba, amman tabbas yana gab da kama shi, saboda abinda yake gani na kara tabbatar da ko ciwon hauka yake, to tabbas a cikin wannan ciwon ya kasance tare da Layla. Wannan gaskiya ne ko da hankalin shi yabar jikin shi. Wata irin mikewa yayi yana kama zanin gadon ya yaye shi daga kai, fita yayi daga dakin kamar sabon mahaukaci.

Bokitin daya fara cin karo da shi ya saka zanin fadon a ciki ya koma daki ya dauko omo, ya nufi bokitin da sukan tara ruwa ya bude ya diba, kallo daya zakayi mishi da yanda yake wanke zanin gadon kasan ba a cikin hayyacin shi yake ba, yayi mishi wanki yafi biyar kafin ya shanya. Ruwan ya kara diba ya shiga wanka, sai dai ya kai awa daya tsaye a cikin bandakin ko kayan shi bai cire ba, kalar wankan da zaiyi yake tunani, idan ya saka sabulu ya fito tabbas zai fito da daudar da yake ji har cikin ruhin shi.

Idan kuma yayi wankan da zai tsarkake daudar wajen shi baisan yanda zaiyi da ta ciki ba, kuma wankan zai tabbatar mishi da abinda yake so ko yayane tunanin shi ya karyata mishi. Bashi da wani zabi daya wuce yin wankan tsarki ya daura alwala ya fito zuwa daki, kaya ya sake yana fita da wanda ya cire kamar suna tare da wata dauda da ta girmi idanuwa ya saka su a bokiti, dakin dai ya sake komawa ya dauki darduma ya shimfida, har ya kabbara sallar azahar da yake tunanin ta wuce shi, saboda sanda ya fita yaga kamar yamma tayi sosai, komai bai kwance mishi ba sai da yayi sujjada, sai da ya dora goshin shi a kasa ya kara jin yanda bashida wata hijabi tsakanin shi da Ubangiji sannan sauran nutsuwar da yake tare da ita ta kwance.

Maimakon karatun sujjada sai

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Da yake fadi muryar shi can kasan makoshi yana maimaitawa ko Allah zai tausaya mishi ya sake mishi wata kaddara da zai iya dauka ba wannan da ta faru ba, tun yana yi muryar shi na fitowa harta daina ya koma yi a zuciya, tun kafafuwan shi na da sauran karfin durkuson sujjadar harya kife gabaki dayan shi, Ayya kance

"Ko rigimar yarinya bakayi ba Bilal, zan iya kirga lokuttan da naga hawaye a fuskar ka"

Amman yanzun kukane mai gunji ya kwace mishi, kuka yake daga zuciyar shi, rurin shi na fitowa da sauti kafin wasu irin hawaye masu zafi su zubo mishi, hade jikin shi yayi yana wani irin kuka yau da yake neman mai lallashin shi, saboda a labarai ma bai taba cin karo da kalar kaddarar su ba, bai taba jin labarin tashin hankali makamancin wannan da yake ciki ba, bayani yake nema yayiwa kan shi ya kasa, idan ya kasa gane abinda ya faru ko ya akayi ya faru taya zai ma wani bayani ya gane, wanne irin uzuri zai bayar

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.