Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 98 of 125
"Sun sami hatsari ne..."
Cikin wata irin murya da Rayyan baisan daga inda ta fito ba ko yanda akayi ya iya motsa labban shi yace
"Hatsari? A ina? A ina? Suna ina yanzun?"
Wannan karin iskar yake ji tana kadawa a ko ina na jikin shi da yayi wani irin sanyi na ban mamaki, baya tunanin ya fahimci abinda aka fada din, saboda kunnen shi yaji daga wajen
"...Babu wanda ya fita a motar, da tankar mai suka hade..."
Abinda aka fada kafin nan da bayan nan duk bai jisu ba, iya inda yaji din ma bai fahimta ba shisa ya mikawa Abbu wayar
"Ban gane me yake fada ba Abbu, kaji me yace"
Abinda mutumin ya fadama Bilal shi ya sake maimaitawa Abbu da wayar ta subuce daga hannun shi yana furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Yana sake maimaitawa ko ina na jikin shi na bari, duniyar gabaki daya tana hargitse mishi
"Menene? Me ya faru?"
Yaya Ayuba yake tambaya saboda yanayin Abbu din duk ya hargitsa shi, shisa ya sauka daga kan titi yana yin parking din motar, wayar Rayyan da take jikin Abbu ya dauka, kiran ya yanke. Bai bi takan su Abbu ba ya sake duba lambar da yake itace kan kiran karshe da ya shigo, sau hudu yana kira duk ana ce mishi busy alamar ana kira da layin, sai ana biyar tukunna ta shiga
"Ina kira akan Bilal Abdullahi Dikko ne, bamu fahimci me kake cewa ba"
A nutse yayiwa kawu bayanin hatsarin da motar ta samu a hanyar Zaria, hatsarin da aka dade ba'a ga irin shi ba, saboda doguwar motar gabaki daya babu wanda aka fitar a ciki, wasu ma sun zama toka, iya gawarwakin da aka samu fitarwa basu fi goma ba idan aka hada jimillarsu, suma wasu duk sun hade da yan uwan su, yanayin da bai bar ma mutanen da suka kawo musu dauki wani zabi daya wuce hade su gabaki daya aka yayyafa musu ruwa aka sallace su hadi da haqa kabari daya aka hade su ba. Shi kan shi kawu babu inda jikin shi baya kyarma, saboda a tunanin shi ma ya kasa hasaso yanda lamarin ya kasance
"Bilal ya rasu"
Ya furta a hankali yana dorawa da
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Abbu ma abinda yake fadi kenan yana maimaitawa, bayason bama kwakwalwar shi wani space nayin tunanin komai. Sun kai mintina goma a wajen kafin ya iya samun karfin jan motar suna nufar gida. Da suka karasa ma aka bude musu ya shiga yayi parking, duka yan gidan babu wanda bai tashi ba. Sun zo harabar da ake ajiye motocin sunyi tsaitsaye ne kamar suna jiran dawowar su Abbu din. Shi kan shi Yaya Ayuba da ya fito yana ganin su tsaitsaye yaji kamar ya koma cikin motar, amman daga Abbu har Rayyan babu wanda ya iya ko motsawa balle yayi tunanin ko zasu fito.
Ayya ce ta karaso wajen da sauri, kallo daya zakayi mata kaga yanda idanuwanta suka kankance suka sake launi saboda kukan da tayi, kukan da yanzun ne zata soma shi.
"Kun gan shi?"
Ta tambaya, Yaya Ayuba na girgiza mata kai hadi da dauke idanuwan shi daga kanta. Ya daiyi mamakin ganin harsu Khalifa a cikin gidan. Suna hada idanuwa da Khalifa ya tako ya karaso inda Yaya Ayuba da yaji shi gefe yake
"Khalifa ya rasu... Bilal ya rasu"
Yaya Ayuba ya furta girman kalaman na dukan shi, cikin tashin hankali Khalifa yake kallon shi, da hankalin shi, a tsayin rayuwar shi baisan wani abu rashi ba, wani daya taba shakuwa da shi bai taba rasuwa ba, yaune rana ta farko da aka fara sanar da shi labarin mutuwar da ya saka gwiwoyin kafafuwan shi yin sanyi gabaki daya, da Yaya Ayuba bai riko shi ba sai yakai kasa
"Subhanallahi, Khalifa"
Yaya Ayuba ya fadi, a zaton shi tunda Khalifan ne Babba a gidan, zaifi sauki shiya fara sani kafin a san yanda za'a sanar da Ayya da ta karaso wajen tana kallon Yaya Ayuba
"Me ya faru? Me akayi?"
Kan shi Khalifa ya dafe yana saki, numfashi yake fitarwa ta baki ko zai samu saukin abinda yake ji, amman komai kara hade mishi waje daya yake. Gurin motar Ayya ta karasa tana bude bangaren da Abbu yake, kan shi taga ya hade da gaban motar, a tsorace ta dafa shi, ya kasa dagowa
"Ahmadi"
Ta kira, amman bai ko motsa ba, mantawa tayi da yaranta na wajen, mantawa tayi akwai kowa banda ita da shi, ta saka hannuwanta tana dago da shi
"Ahmadi..."
Ta sake kira, idanuwan shi Abbu ya saka cikin nata, kafin ya dago nashi hannuwan ya kama nata da yake jikin shi, kamar yana so ta taimaka mishi ya fito daga motar, hakan kuwa tayi, duk da yana fitowa sai ya kasa yin komai banda jingina bayan shi da motar yana zamewa a hankali ya zauna, har lokacin yana rike da hannuwan Ayya shisa itama ta bishi kasan tana tsugunnawa, da wani yanayin tashin hankali yake kallonta
"Ya rasu Maimuna... Bilal ya rasu"
Ba wannan bace mutuwa ta farko da aka fada mata, ance baka san daci na mutuwa ba sai ranar daka rasa mahaifa, miji ko da. Ta dandani mutuwa kala-kala, bata san ciwon rashin da daban yake ba sai yau, dan wani abune ya tsirga mata daga dan yatsan kafarta zuwa tsakiyar kanta, kafin komai ya tattaro ya dawo yana tokare mata kahon zuciya, kukan kowa da wani yanayi yake isa kunnuwanta, musamman Rukayya da ta karaso inda take tana jijjigata
"Ayya me suke cewa? Ayya kice mun karya ne, ki ce mun Hamma Bilal bai rasu ba"
Bata ko iya juyawa ba, hannuwa Abbu da yake rike da nata ne kawai abinda tasan yana rike da sauran hankalin da take tare da shi, haka Rukayya ta dinga bin duk wanda ta samu tana jijjiga shi, har ta karasa inda Mami take tsaye hawaye na zubar mata, wani nabin wani. Tun jiya Ayya ta fada musu abinda yake faruwa, tun jiyan kuma Rukayya take tunanin rayuwa da yanda komai zai iya canzawa cikin kankanin lokaci. Tun da ta taso Ayya ke fadin laifukan Mami, duk da sanda ta fara hankali ta gane rabin mitar Ayya din na tare da kishin da yake dawainiya da ita.
Mami bata taba ko da mata kallon banza ba, gaisuwar mutunci tana hadasu, wasu lokuttan ma har su danyi hira. Duk yanda Ayya taso ta ga laifin Mami bata taba gani ba, sai yau da ta karasa tana kama hannun Mami
"Kingani ko Mami? Muna zaman mu ki dauko mana Layla, da bata shigo rayuwar mu ba da yanzun bamu san tashin hankalin nan ba, da Hamma bai bar gida ba, da labarin mutuwar shi baizo mana ba... Wallahi ba zan yafe miki ba, Mami ba zan yafe miki ba..."
Rukayya take fadi tana durkushewa wani irin gunjin kuka na kwace mata. Duk abinda akeyi Rayyan na cikin motar, ba jinsu bane bayayi, kan shi yake ji kamar a wata duniya ta daban. Komai ne yake karasawa cikin kunnuwan shi kamar saukar ruwan saman da babu hadari, yana zaune ciki yaji muryar Haris na fadin
"Bilal ya rasu? Yaushe? Garin yaya?"
Kafin ya dora da
"Ina Rayyan?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.